RAYUWAR JIDDAH ✔

By DielaIbrahim

10.3K 856 277

RAYUWAR JIDDAH Labari ne akan rayuwar wata ya' mace mai suna Hauwa'u Jiddah. Let embark on the journey togeth... More

02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
AL'ADARMU
UMMI KWARAS
AL'ADARMU
AL'ADARMU

01

1.6K 51 7
By DielaIbrahim


Assalamualaikum
Dasunan Allah mai rahama mai jin kai

*****************

Assalamualaikum Fans
Na dawo muku da sabon labari to which I hope zai nishadan tar daku, fatana dai kukasance atare  dani in this long long journey, zanso ku biyoni don jin sabon labarin danake tafe dashi,mai suna Rayuwar Jiddah
***********
I DielaIbrahim assure you that,I'll never disappoint you with this story  inshallah but,In need of your support for sure🙏 just to encourage me.(please).

Rayuwar Jiddah
Part 1/01

____________________________________
Gwamna Road,Kaduna State
10 of August,1988

******
Sefa Specialist Hospital
5, College Road,Badiko Kaduna State.

Misalin karfe takwas 8pm wata karamar mota kirar Toyota ta kutso kai cikin harabar asibitin direct wajan parking ta nufa, cikin sauri kuma batareda bata lokaci ba wani kyakkawan mutum ya fito ya bude kofar baya, kafin ya fara kiciniyar fito da matar dake back seat, babu abinda yake fitowa daga bakinshi sai sannu,yayin da yake kara sauri yana fito da ita daga cikin motar, Bayan ya fito da ita ne ya kulle kofar, sannan ya kamata suka nufi hanyar cikin hospital.

Late pregnancy ne ajikin ta tana cikin third trimester kallo daya zakai mata kagane she is in second stage of labor  ita kadai tasan irin wahalan da take sha
Dukdama da alamar shan wahala da matar take ciki bai hana ta daure tana takawa ba har suka isa cikin hospital din.....Wasu Nurses guda biyu da fitowansu kenan zasuje wajan doctor suka hangosu ba shiri suka nufi inda suke sa'annan suka kama matar sukayi cikin labour room da ita
Sai da suka sanar da doctor, sannan suka dubata cikin ikon Allah Kuma suka ga tana mataki na takwas to which da alamar haihuwan akusa kusa take.

Barinta sukayi for an hour, dukdama suna jin ihun datake ta faman yi, hade da Addu'o'i sai dai fa ihun nata yafi yawa, ta Kira nurses da sunan mijin nata zai kai akalla so hamsin da wani abu Amma  Nurses din koh basu je sun dubata ba har saida sukaji shurun matar lokaci guda kuma sukaji kukan jariri sannan sukayi ciki da gudu.

Da mamakin su ko suka ga 'Da ya fado sai faman tsala ihu yakeyi, matar kuma idanun ta arufe kaman mai bacci tayi shuru, ba shiri suka soma aikinsu to which sai da suka dauki tsahon minti ashirin suna gyara matan da Kuma Dan data haifa.
Cike da murna suka mika ma mutumin daya kawo matar, suna mishi congratulations dayar ke cewa hope kaine baban baby?

Murmushi yayi yana gyada masu kai,bakinshi kuwa ya kasa rufuwa tsabar murna da farin ciki
Nurses din sukace it's a boy

Alhamdulillah ya furta baby boy
Allah na gode maka hade da
Kissing forehead din babyn, sannan yai mashi addu'a ya Kuma karagodewa Allah dayai mashi babban kyauta,..... Dago kai yayi dasauri Yana ce musu " can I see my wife please?"

Daya daga cikin nurses din tace
"Yes sure" but Bari muyi transferring dinta zuwa ward tukunna.

Gyada masu kai yayi hade da neman waje yazauna Yana kare wa kyakkawan jaririn kallo, fadi yake MashaAllah, a ranshi kuma Yana ta saka kamannin da sukeyi da jaririn, Dan kuwa kallo daya zakaiwa babyn kasan ya dauko kaman ubansa sak.....Yana nan zaune sai faman wasa yake da jariri yaji nurse na magana

Sir,Munyi transferring dinta, you can now see her"

Okay thank you" ya amsa cike da annuri a fuskanshi burinshi bai wuci yaga matar tashi ba ayanzu.
Da sauri ya nufi ward din wanda yake cen sama, Kai tsaye dakin ya nufa ya tura ahankali, gadaje shidda ne a ward din, ita tana cen kurya don haka Kai tsaye yayi wajanta yana murmushi......itama dai murmushin ta sakar mashi, sai dayayi kissing dinta a forehead kafin ya nuna mata baby, yana cewa

It's a boy, and you see he looks like me, ya kuma kissing forehead din babyn yana cewa my look alike you are highly welcome to the world.

Wani murmushin ta kumayi ta dubi Uban dan nata, wani irin kara sonshi takeyi...... cikin kula da nuna son ganin babyn playfully tace toh ni bazaka bani na dauke shi ba, ko addu'a nai mishi.

Zare idanu yayi hade da yin baya kadan sa'annan ya kuma rungume babyn kaman wani na Shirin kwace mashi babyn.....alokaci daya kuma ya daure fuska in a serious manner yace Noooooooo har yanzu you are in pain,you still need to rest dear.ya karashe maganar yana turo baki.

Tsare shi tayi da idanu tana kallon shi tana murmushi kaman me son gano wani abu afuskar mijin nata,da sauri tace Mommy huh!!!! Ta kulle bakin ta da hannunta, alamar ta mance da wani abu.

Dubanta yai dasauri, kafin yayi wata magana, ta kuma cewa
Basu sani ba fah.

Dafe forehead dinsa yayi, Yana cewa ohhh shit, namanta Kuma tace idan na kaiki na dawo na dauke ta, wai alokacin tasan jikin nata yayi sauki....yakarashe yana kallon matar cike da damuwa sai Kuma ya daura da cewa....Rahma kedin ce kin rudar Dani, saboda kina cikin pain and I can't go back home at that time, I cannot leave you alone....

Shiiiiihh🤫ta katse shi da cewa yanzu kam sai dai idan mun koma, Ina gobe zasuyi discharging dina? Ta tambayeshi.

Gyada mata kai yayi yana ta jijjiga baby wai shi adole yana rainon babyn da haryanzu bacci ma yakeyi abinshi peacefully.

Karfe shidda na asuba akayi discharging dinsu bayan doctor ya gama duba ta, aka sallame su, suka tafi gida.

Wani katafaren gida suka nufa wanda yake cikin Unguwar Gwamna Road, Mai suna Gwamna Awon kan titin Shehu Idris College Road nan suka Shiga basu tsaya ako Ina ba sai a wani katafaren gida na masu rufin asiri, fita yayi ya bude gate da kansa kafin ya koma ya shigar da motar. Bayan ya kashe motar ya fita ya taimaka wa matar ta fito, sannan ya dauko jaririn sukayi cikin gida.

Da shigar su cikin gidan yara mata guda biyu da  suka fara hango su, sune suka fara murna suka ruga wajan yayan nasu  suka amshi jaririn suna murna kai tsaye flat dinshi sukayi  inda yake cen cikin kuryar gidan ya bude kofa suka Shiga da, alokacin yake tambayan yan matan Ina mommy?

"Tana kitchen babbar ta amsa Masa"

Fita yayi Kai tsaye yayi hanyar kitchen rungume mommyn yayi ta baya, yana cewa mommy Alhamdulillah jikan ki ya iso lafiya"

Cike da murna mommyn ta juyo tana cewa MashaAllah hade da ware hannuwa Ina suke?

Yanzu muka dawo, suna daki...jiya ban samu na dawo na dauke ki ba mommy.....Rahma ce wlhy........

Shiiiiihh 🤫 tai saurin katse shi
Nasan bazaka iya barinta ita kadai ka dawo ba, nima kuma alokacin bana jin dadi kasani sai da safen nan jikin ya warware, ta num fasa kafin tace don't worry son hope suna lafiya dai koh?
Ya gyada mata kai with full of confidence.
Toh Alhamdulillah Allah ya Kara masu lafiya.
"Ameen" ya amsa
Muje naga karamin Mai gidana please ta fada tana karasa wanke hannunta.
Suka tafi a jere suna wasa da dariya,shikuma ya rike hannunta, har suka isa flat din, basuyi mamakin ganin yanda falon ya cika ba da sauran yan uwan ba, don dama  kowa jira yake ace an haihu lafiya.

Mommy ta nemi waje ta zauna tana duban yayan nata yadda kowa keta daukan jaririn suna murna kowa fadi yake
Wannan fuskan Yaya abubakar ne wlhy, yayinda mommy tace zaku mikomin karamin Mai gidan ne ko yaya.

Dariya yaran suka saki, sannan sukace Lahh🤭mommy ko kunyan Aunty Rahma ma bakyaji  cewar Autar ta mai shekaru goma.

Mommy ta wurga mata harara playfully tace ae kunyar ta tafi amma bari na ganshi tukunna kafin kunyar ta dawo.....ta fada tana kallon Rahma dake ta murmushi abinta cikin zuciyarta kuwa itama tana son ta dauki yaron Amma kunya ayanzu bazai barta ba.......ta kai dubanta ga mijin nata wanda tuni ya dawo kusa da mommy ya zauna yana cewa mommy my replica.....

Mommy ta harare shi playfully sannan tace noooo he is my late husband replicate...he resemble his late grand father, ta karashe maganar tana kallon fuskan Dan nata cikin murmushin wasa

Shikam Abubakar bata rai yayi ya dubi matar tashi yace wai kinji mommy ko tana so ta nuna min babanci don tayi sabon miji....ya karashe yana zumbure baki kaman zaiyi kuka.
Babu wanda baiyi dariya ba a falo.....haka sukaita murna nan aka fara aike ana sanar da yan'uwa na kusa, Yan uwan nesa Kuma ta landline Abubakar yake kiran su Yana shaida masu kaaancewar zamanin lokacin waya bata shigo ba, Abubakar shine da namiji babba awajan mommy( Hajiya Hauwa'u). Mommy yaranta biyar,
Maza biyu mata uku
yarta ta farko mace ce (khadija)
Sai (Abubakar) sai (Yusuf) sannan sai (Maryam) sai auta (Fatima)

Mahaifinsu Late.Yusuf Abubakar alokacin shekaranshi biyu da rasuwa inda yayi karamar rashin lafiya kwananshi biyu a hospital Yana jinya Allah Kuma mai kowa mai komai ya amshi abinsa,..ya rasu yana da rufin asirinshi, shi bamai dukiya bane Amma Allah ya rufamasa asiri sosai. Hakan yasa da fari yayan sun sha wahala Amma ayanzu da abubakar ya fara samu shine komai ya fara dawowa normal.

Ranar suna kuwa Da yaci sunan mahaifin Rahmatu wato
Hafiz Abubakar.

Wannan kenan

***************************

Vote
Comment
Share
Please

Continue Reading

You'll Also Like

2.3K 231 15
Saboda yadda mahaifin mu ya din ga saka Mana suna Fatima, har se da nayi tunanin ko Muna da alaka da shi'a ne, saboda Naga yawancin sune mutanen da k...
10.7K 549 20
Labari ne dake dauke da darussa kala kala na rayuwa, Mai dauke da tausayi, Al'ajabi ga kuma kauna agefe d'aya.. shin wacece UMMI_A'ISHA?
Daisy By Sin

Fanfiction

2.8K 128 9
TokyoRevengersXQinShiHaung!Fem!Reader PAUSED
2.9K 241 29
The story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ƙunshe da ma'an...