MAKAUNIYA CE

Av Jiddasmapi

17.9K 991 101

Ta mak'ance ta dalilinshi Amma baisan dahakan ba, ya wulak'anta ta, anci mutuncinta a gidansu.. Mer

Page 1
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
Completedβœ”

Page 2

588 29 0
Av Jiddasmapi

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwane ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

   *Page* 2

"Minal tafiya take tana hawaye yanzu idan naje gida mezan faɗawa Umma na?  Gashi yau ko abincin dazamuci babu, wannan mutumin yacuce ni,  dana sani ma dana karɓi kuɗin wannan Latif ɗin,  to Amma idan Ummana tagani mezan ce mata?  Ita kaɗai taketa maganar,  tana cikin tunani taga wani me keke saura kaɗan ya bugeta,  da gudu tamatsa awajen,  me keken ne yace ke wace irin wawiya ce?  Ana tamiki magana kin share mutane kina tafiya yanzu idan nakaɗeki saiki janyo min matsala wawiyar banza,
Minal ganin yanata zaginta acikin mutane yana mata ihu yasa tace mishi  Malam bana matsa maka ba?  Yazaka tsaya kanamin ihu?  Nifa ba 'yarka bace ba tamm,  yace ko zaki dake nine?  Matsiyaciyar banza kazama,   ran Minal ne yaɓaci tace niba matsiyaciya bace,  yace se waye?  Tace sai kai... Ai kuwa kafin takarasa ya sauko akan keken yaɗaga hannu zai sauke mata mari wani mutum daga gefe yarike hanunshi yace haba bawan Allah tunda ta matsa ba shikenan ba? 
Ke kuma kina mace zaki tsaya kina faɗa da namiji a titi?
Minal ce wanda tuni idonta yafara kawo ruwa tace Baba tinani nake shiyasa yayi tamin magana banji shi ba Amma tinda namatsa ai sai yayi min uzuri.
Mutumin ne yace to yanzu dai kowa yayi hakuri,   Minal ce tajuya tayi tafoyarta tana me share hawayenta.
Azuciyarta tace nikam banida farin jini awajen kowa,   haka harta isa gida,
Tana shiga gida Umma tace Meya dawo dake Minal?  Hala kin manta yaji ko nasanki da mantuwa,   Minal ce tafara kuka zuciyarta tana mata raɗaɗi,   Umma tace haba Minal meyasa kike kuka?  Koso kike nima in fara kuka ne?  Minal tace Aa Umma dama Faɗuwa nayi damuke tafiya shine alalan ya zube,
Umma tace to dan Alale yazube shine zakiyi kuka?  Wanima arana ɗaya yake rasa gidanshi da dukiyar shikuma wancan ya zeyi? Indai akan wannan ne kidaina kuka Allah yasan damu kinji ko?  Minal tagiɗa kai"

_Washe gari_

"Minal ce tafita da Alalenta taje gidansu Madina sun fito tare,  ahanya Minal take cewa Madina nifa inajin kamar in canza wajen saida alale Dan Ummana batasan meyake faruwa ba! Datasani bazata barni naci gaba da saidawa anan wajen ba.  Madinace tace Aa Minal karki faɗa mata kici gaba dakai abunki karki kulashi kinji?
Minal tace tom amma bazan iya daure wulaƙancin shi ba,
Madina tace idan bakya kulashi zai daina.

Shikuma Bilal idan yatuna abinda wannan ƙazamar yarinyan tafaɗa mishi sai yaji kamar yakashe kanshi,
Kwance yake akan makeken gadonshi ya lulluɓa jikinshi da bargo me taushi, jiyake yau kamar kada yaje din bayason ganin yarinyan ko kaɗan.

Knocking na kofarshi aka fara,  ahankali yace Who is that?   Ba'a tsaya da buga kofarba yasake cewa i say who is that?
Muryan mace ne tace "Afrah ce"
Yace me kikazo yi?
Tace "Mom ce tace nazo naduba ka sabida yau kofita bakai ba"
Yace shine inyi miki me yanzu?
Tace "kabuɗe inason inga lafiyarka hankalina yakasa kwanciya"
Wani takici ne yakamashi yanzu yaji da abinda yake damunshi ne ko yaji da nacin Afrah?
Shifa gaskiya yarinyan tafara isanshi dolene yaɗau mataki akanta,  can daga bakin kofan naji tasake cewa "wallahi idan baka buɗe naganka ba zan iya mutuwa"
Bilal ne yaji kamar yarufe idonshi yaganshi a lahira tsabar takaici.

Tashi yayi yaje bakin kofar yabuɗe mata,
Wata yarinya ce wanda zatakai shekara 22 naganta sanye da dogon riga roba roba kanta ba ɗankwali tayi kitson attach kamar ba gobe,  farace ita amma ba sosai ba,  idonta tayi fixing na eyelashes dogo dogo,  tanada jiki kaɗan,  rigan jikinta yakamata sosai,  tauna cingum take yana kara kass kass kass,  tsaya Bilal yayi yana kallonta.

Azuciyarshi yace "yanzu wannan Musulma? Meyasa 'ya'yan musulmai suke haka?..
Kafin yakarasa maganar yaji saukan hanunta a shoulder ɗinshi, tana cewa "Honey meya sameka kazama wani iri haka?"
Janye hanunta yayi daga jikinshi kafin yace "ke kinga banason raini, idan kika kara shigo side nawa da ire iren wannan dressing ɗin saina ɓata miki ranka, oya get out".

Afrah ce tace "haba yaya Bilal meyasa zakamin haka?  Kasani fa duk kwalliyan danakeyi sabida kai nake,  amma sam baka gani, ina laifin wanda yace yana sonka?"

Bilal ne wanda ranshi yafara ɓaci sosai yace "Afrah waike wace irin mayya ce?  Nace banason kina cewa kina sona Amma meyasa bakyaji?"

Sabida inasanka!  wallahi yaya inasanka! Kuma Aurena nakeson kayi.

Ɗago kanshi yayi wanda idanunshi sukayi jaa,  yace "ke in zan Aura? Ai ko mata sun kare a duniya bazan Aureki ba! Afrah kicireni aranki niba sa'anki bane"

Afrah ce tace "me bani dashi wanda 'ya mace take takama dashi?  Me narasa arayuwata?  Menene aibuna?  Kuɗi, kyau duk ina dasu kai kanka kasan kuɗin ubana,
Kasan zan iya kashe ko nawane akanka, sannan kasan yanda Babana yake sona,  ko nawa zai iya kashewa dan nasamu farin ciki......  Ya isa cewar Bilal.

Kuɗi, Babana, kyau, kullum shine maganarki, nasan baki rasa waɗan nan ba,  Amma kin rasa abu Ɗaya wanda yafi muhimmanci a rayuwar mace.

Afrah tace "kafaɗamin mena rasa?  Saina nemoshi ayau ko nawa ake saidawa".

Bilal ne yace "kuɗin ubanki be isa yasiyo muki ba sannan kyaunki baze iya nemo miki ba"

Menene wannan Bilal?  Kafaɗamin.

Bilal yace "Kunya"

itace abinda kika rasa,
Sam baki da ita.
Yana faɗin haka yawuce toilet, tara ruwa yayi acikin bathtub,   yazauna aciki shower yakunna tasaman kanshi,  lumshe idanunshi yayi me yana tunani acikin zuciyarshi,  wannan wani irin rayuwace? Ace mace kwata kwata batada kunya?  Nace bana santa amma ta nace,  ko matan duniya sun kare yana ganin bazai iya auren Afrah ba!
Yarinyan da bata tsoron jikin niji kp kaɗan,  kai ina daya Auri Afrah gara yamutu ba Aure.

Sabulu Me sanyin kamshi yaɗauka yana gogawa ajikinshi, idonshi a lumshe,  Yana gama wankan yaɗauko towel babba da karami yaɗaura babban daidai konkosonshi goge kanshi yake da karamin,  ahankali yabuɗe Kofar toilet ɗin.

Yana fita aɗakin yaga Afrah kwance akan gadonshi,  mamaki ne da takaici suka kamashi alokaci ɗaya,  wannan wace irin mayya ce?
Karasawa yayi inda take azuciy,  saidai yana zuwa Jikinshi yayi sanyi,  ganin yanda ta tattara riganshi tarungume tana bacci.

Tsaki yaɗanja kaɗan,  yajuya yakarasa wajen kayan shafe shafenshi, 
Mayuka masu kamshi yashafa ajikinahi tare da turare me kamshi da sanyaya zuciya,
Cumb yaɗauko yataje gashin kanshi me tsantsi da yalƙi, wajen wardrobe nashi yaje yaciro wani pink nariga da baƙin jins, hanyan toilet yanufa   yaje yasa kayanshi, koda yafito saiya duba kanshi a madubi yaga yayi kyau.
Makullin mota yaɗauka yafice agidan.

Ita kuma Minal yau daɗi Takeji me takurata baya nan zata saida alalenta hankali kwance,
Latif ne yakaraso wajen yace "kanwata yau zanci alalenki,  kisamin na ɗari uku"

Waro manyan Eyes nata tayi cikin mamaki tace "na ɗari uku?  Kaida wa zakuci?"

Latif ne yayi dariya sosai yanda ganin yanda ta waro idonta yace "kanwata ai saikisa na tsorata,  wannan idon naki ay zasu ruɗa mutum,  Nikaɗai zanci.

Dariya tayi wanda yasa gefen kumatunta lotsawa Tace "to ay bazaka iya cinye na ɗari uku ba,  guda sha biyar fa"

Yace eh zanyi sadaka da sauran, tace tom.

Roba taɗauko tasa mishi na ɗari uku hadda kyautan biyu tace gashi,
Karɓa yayi yaciro ɗari biyar yace ga kuɗinki.

To ay ba canji cewar Minal,
Latif ne yace  kiɗauka duka nabar miki,  tace Aa banaso kabari agida za'a min faɗa,  yace to kirabarwa mutane na ɗari biyun,  tace to.

Ɗaukan roban tayi,  takira almajirai tafara raba musu.

Almajurai ne suka taru akanta suna wawa,  garin zata kwace roban wani Almajiri ya tureta,  ai kuwa sai gata akasa dama jikinnata kamar karkashi,  wawa suke suna tattaka ta.

Da sauri Madina takaraso wajen tana turesu.

Daidai lokacin motar Bilal ta danno kai,  ganin yanda almajirai suka taru awajen suna wawa yasashi fita amotar da sauri.

Karatawa yayi wajen yana san jin meyake faruwa?

Ganin Minal kwance tana ihu ne yasashi tsayawa yana kallonta,  yanda taje birgima akasa kamar 'yar shekara biyu.

Takaici ne yakamashi ganin yanda jikinta yayi datti.

Tsaki yaja azuciyarshi yace "Allah yasa karsu barta haka saitaji ciwo,  yajuya yayi tafiyarshi"

Dakyar Minal tasamu takarɓi roban tafalfala da gudu tabar cikin company ɗin.

Shikuma Bilal yana shiga yaga Latif da roban alale yana ci,
kallonshi Latif yayi yace "you are wellcome,  meyasa yau kayi letti"

Amaikon Bilal ya bashi amsa, sai yace "aina kasayi wannan abun?"

Awajen Minal cewar Latif

Wace Minal?

Latif yace "yarinyan dakake wulaƙantawa"

Dagudu Bilal yashige cikin toilet na office ɗin yafara sheƙa Amai,  gashi ba abunda yaci yau da safe.

Mamaki ne yakama Latif,  daga cewa awajen Minal saiya fara Amai?
Kai ina ganin ba lafiya ba!.

_✅ote Comment and share_

✍🏻   *Jiddah S Mapi*

Fortsett Γ₯ les

You'll Also Like

1.6M 97.9K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
3M 193K 89
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
280K 32.1K 50
π’πœπžπ§π­ 𝐎𝐟 π‹π¨π―πžγ€’ππ² π₯𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐑𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐒𝐞𝐬 γ€ˆπ›π¨π¨π€ 1〉 π‘Άπ’‘π’‘π’π’”π’Šπ’•π’†π’” 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 β˜†|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
3.5M 145K 61
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...