page 38

376 21 2
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Page 38...

By
Jiddah S Mapi

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

~Gudu yake akan titi burinshi kawai yaganshi a airport, Latif ne yashayo kwanan, da gudu shima yana sauri yaje gida Dan sabida an kirashi awaya Abba ba lafiya an kaishi asibiti, ganin motar Bilal yana gudu kamar zai tashi samane yaji hankalinshi yakasa kwanciya, "to ina Bilal zaije haka? Bari dai nabi bayanshi sabida gudunnan bana Lafiya bane" rivers yayi yafara bin bayan Bilal, Bilal bai tsaya da gudu ba saida ya iso babban airport, yana zuwa yaja wani mugun birki, mutane tsayawa sukayi suna kallonshi, yanayin parking Latif ma yayai parking fita yayi yabi bayan Bilal d'in, Bilal wurin wani Wanda yake babba a office d'in yaje, yana zuwa ya mikawa meshi hannu yace.

  "yallabai inason adubamin information akan wasu Wanda suka dawo daga India ranar 17/9/2020 please, mutumin yace "OK" report yafara dubawa ya d'ago wasu manya manyan takaddu yana duba passport, Bilal ne yashiga tayashi nema, suna cikin dubawa Latif yayi sallama, Bilal hankalinshi baya wurinshi shiyasa ma baiji sallaman ba, Latif ne yakaraso yace "lafiya kuwa?" Bilal ne ya juya yakalleshi da sauri yaja hannunshi yace "zo katayamu duba passport na beauty".

"Wace beauty kuma?" "Beauty na mana Minal" Latif ne ya kwashe da dry yace "daga zuwa India sai mata ta b'ace?" Bilal ko kulashi baiyi ba yaci gaba da dubawa, Latif ma irin takaddar ya d'auka yana d'an dubawa yana dry kasa kasa, kamar dawasa yaga hoton wata me kama da Minal, kurawa hoton ido yayi yana duba information akai, ganin An rubuta Abuja yasashi sakin murmushin dashi kad'ai yasan ma'anarshi, har unguwar da su Minal suke a Abuja saida aka rubuta a pejin, Bilal ne ya leko yace "kasamu ne?" Saurin rufewa Latif yayi yace gaskiya babu wani information kawai ka hakura mutafi, Dan gaskiya bazan barka ka tafi kai kad'ai ba yanda naga kana tuki kamar ka siye kwaltar gaba d'aya"

  "Dan Allah malam ka kyaleni, Dama ai ba sona kuke ba, kowa yana guduna ciki harda kai, wallahi Latif kabani mamaki yanda ka gujemin a lokaci d'aya bayan kasan irin damuwar danake ciki, mutum d'ayace nasan tana tausayamin itace Minal, kuma sabida ita nake gudun domin koda na mutu na tabbata watarana zataji labarin sabida ita na mutu"

  "Relax Mr Love, yaushe kafara soyayya haka? Kaida kace soyayya b'ata lokacine kuma ka manta wulakancin da kakeyi mata?"
"Dan Allah kadaina tunamin baya Latif, abinda yafaru yariga ya faru, yanzu taimakonka nake nema ka taimakamin in nemota wallahi ina cikin matsala"
Latif ne yariko hannunshi yace "yanzu dai Abba yana Asibiti ba lafiya, ka kira driver na gidanku yazo ya d'auki motarnan, sai muje a motata ni zan baka shawara Wanda nakeda tabbacin zakaji dad'inshi"

  Bilal ne yaciro waya yakira driver, yayi mishi bayani, hannun Latif yariko yace "muje meya samu Abba?"
"Wallahi diabetes ne yake damunshi"
Bilal yace "Allah ya kawo sauki"
"Ameen".

  ~bayan su Latif sunje asibiti ne aka kira Bilal awaya  yana d'auka yace " hello ka d'auko motar ne?"
'Dayan b'angaren akace, "wannan motar tayi hatsari a kusada babban airport, sanadiyyar birkin da aka kwance Wanda idan an kamashi sau d'auya to kamu na biyu bazaiyi ba" d'itt aka kashe wayar
Da sauri Bilal yafice da makullin motar Latif, yana zuwa wurin airport yaga mutane sun taru makil, ana baiwa driver kalmatushahada Amma Sam yakasa karb'a sai cewa yake Bilal ka yafeni, Bilal yana zuwa driver yariko hannunshi yace "Dan Allah Bilal ka yafemin nayi maka laifuka da dama kuma da had'in bakin Babanka nayi, ka yafemin, domin tin aduniya Allah ya nunamin" Bilal yace.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now