page 22

377 25 9
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 22...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Ameen" Bilal yace.

Doctor yace "to malama Minal a kula sosai, anji?"

"Minal dataki sakin Bilal kin amsawa tayi, Bilal sai dariya yake"

Saida suka fita a office d'in Bilal yace "to sakeni yanzu ai mun fito, karki jawo mutane suyita kallona"

Minal saurin sakeshi tayi, ta turo baki tace "ai kai kace ayimin Allura"

Kura mata ido yayi, yanajin wani irin Abu yana yawo a jikinshi, a 'yan kwanakinnan idan tana magana sai yaji kamar karta daina. Yace "to ai Alluran ne zai sama miki lafiya ko bakyason lafiyar?"

Cikin shagwab'a tace "inaso mana yaya Bilal"

Riko hannunta yayi yace "kin San me?"

Minal girgiza kai tayi alamar Aa.

Yace "bakinki yana min kyau"

Wafce hannunta tayi tafara tafiya cikin jin kunyar maganar tashi.

Riko hannunta yayi da sauri yace "kiyi hakuri"

Batace komai itadai tafiya kawai take, Ummace ta hangosu daga nesa, ta karaso inda suke, tana hararan Bilal, wafce hannun Minal tayi daga nashi kafin taja ta suka tafi.

"Bilal ya kasayin komai yana tsaye kawai, dayaga tsayuwan bazatayi mishi komai ba, yasa yafara binsu, gani yayi Umma takama Mashin mai K'afa Uku, tasa Minal Aciki itama tashiga sai tafiya"

Cikin zuciyarshi yace "me take nufi kenan?"

Minal ce tace "Umma ina yaya Bilal d'in?"

Shiru Umma tayi mata, takara cewa Umma ina yaya Bilal? "

Umma ce tace "Minal idan kinason kwanciyar hankali na to kada ki kara yimin maganar wannan yaron daya yaudareki, yasa kika Aureshi dasunan za'a gyara miki ido, Madina tafad'a min komai, naji duk irin wulak'anci da cin mutunci dasuke miki, ai Makanta ba hauka bane, kuma maraici ba kaskanta bane"

Minal tasan ran Umma ya b'aci sosai, kuma itama a nata b'angaren hakane, sabida daurewa take tana yiwa Bilal magana, don kar Umma ta fahimci wani Abu.

Sun isa gida lafiya, Umma ce tacewa Minal "muje in miki wanka ko?"
Gyad'a kai tayi tace "to Umma"

Umma ce tahad'a ruwan zafi takai band'aki, zuwa wajen Minal tayi tarik'o hannunta, had'i da kaita band'aki, cire mata kayan tayi, wani irin firgita Umma tayi ganin bayan Minal da shatin Bulala kamar na jaki, Kuka tafara tace "Minal meya sameki a baya haka? Dame suke dukanki? Wannan wani irin zalinci ne?"

Kuka take tsakaninta da Allah Minal tana bata hakuri, da kyar ta lallab'ata har tayi shiru.

Bilal ganin tsayuwa bazai karb'eshi ba yasa yakama Napep shima yatafi gida jikinshi duk a mace.
Yana shiga yaga Hajiya babba a cikin gida ta d'aura d'ankwalin shadda har goshi tana harare harare ita a dole gidan d'anta.
Tana ganin Bilal tafara Tambayarshi "ina mayyar matar taka datayi mana sharrin mun bata guba"?

Had'a rai Bilal yayi ko kala baice mata ba yayi hanyar d'akinshi.

Alwala yayi tareda yin sallar Isha, sannan yayi Nafila raka'a biyu tareda yin Addu'o'i, zuwa kan gado yayi ya kwanta, yarufe idonshi daniyyan yayi bacci Amma me? Sai bacci ya kauracewa idanunshi, tunaninta yafara lokacin da akeyi mata Allura, yanda ta rungumeshi ne ya tsaya mishi arai, filo n daya d'aura kanshi ne akai ya d'auko ya rungume sosai ajikinshi, a hankali ya yace "I miss you".

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now