page 12

370 23 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

      By
Jidda S Mapi

Page 12...

Yaya tunanin me kakeyi? Ai kamata ace kayi farin ciki tinda burinka yacika koba hakaba? Cewar Sabir, eh hakane Sabir ai yanzuma ina cikin farin cikin Kaine baka luraba, Sabir ne ya ajiyewa su Minal abincin Untyna kuci Abinci bismillah, zama sukayi suka fara cin abincin, kallonsu Bilal yayi tacikin glass d'inshi, azuciyarshi yace "wayaga Amarya da kawarta Allah yakyauta"

Minal kuwa cikin ziciyarta tana tunanin yanda zatayi zaman Aure da wannan mugun mutumin, Idan nayi mishi rashin kunya nasan zasu fasa fitar dani kasar waje aduba idona, Idan nabishi ahankali kuma zai rainani dayawa ya zanyi?
Madina taga cowslow dayaji bama da cocumber sai tura abincin take kamar ba gobe, Madina zafi nakeji kayan jikina sunyi nauyi wallahi bazan iya bacci ahakaba, to yaya kikeso muyi minal? Ina zan shiga in nemo miki kayan bacci? Idanun Minal ne yafara cika da hawaye tasan da tana gidansu da Umma ta canja mata kaya zuwa na bacci Amma yanzu haka zata kwana da kayan jikinta...kiyi hakuri Minal Idan yaso gobe saiki tambaya subaki ko?
Gyad'a kai kawai Minal tayi,
Suna gama cin Abinci Madina tafitar da plate d'in, suna hira kad'an kad'an har bacci ya d'aukesu awajen."

Bilal kuma yana shiga d'aki ya kwanta agado yana tunani ya akayi yarinyannan ta makance? Wata kila garin Neman tsokana ta tsokano wanda yayi mata illah, tab'e baki yayi yace "Anyway matsalarta ce bata shafeni ba, kuma koda tana makauniya Idan tayimin raini sainaci ubanta"
Shima ahaka bacci yad'aukeshi.

Hajiya Babba kuwa aje Afrah tayi tana koya mata kissa da kisisina da munafinci kala kala saida ta tabbatar Afrah tahau layi kafin takyaketa sukayi bacci.

_washe gari_
Minal ce zaune akasa tarike gyallen Madina kemkem tana kuka wallahi Madina babu inda zaki nasan Umma bazatayi fad'a ba,
Minal wai bakida hankaline? Agidan mijinkifa kike ya za'ayi muzauna tare?
Suna cikin haka Hajiya Babba tashigo d'akin wai ina Makauniyar take? Kinzo kin zauna ad"aki baki iya gaida mutane bane? Ko agidanku ba'a baki tarbiyya ba? Koda shike ina zaki samu tarbiyya awancan akurkin gidan, tashi Minal tayi tana cewa gani Hajiya kiyi hakuri,
Bazanyi hakurin ba kifito kidafamin shayi me citta sabida nan gidan d'ana ne zanyi yanda naso.
Madina haushi gidan yafara bata bata kara cewa komai ba ta d'auki jakarta sai tafiya, Minal batasan ta tafiba.
Rike sandarta tayi tana laluben inda zatabi, dakyar tasamu kofa tana tafiya tana lalube, dab kofar falo taji karar tafiyar mutum, tsayawa tayi tana tambaya Dan Allah inane kitchen? Kitchen kikeso kisani Makauniya? Bataji dad'in sunan da ake fad'a mata ba tace eh, okay kibi hannun damanki zakiga wata kofa saiki shige ciki kinji?.
Minal tace "to nagode"
No need cewar Afrah wacce take murmushin muginta.

Hanya Minal tad'auka har inda akayi mata kwatance, tana zuwa tabud'e kofar tashige, shiganta keda wuya taji kare yafarayi mata haushi, rud'ewa tayi jikinta yafara rawa har sandarta yafad'i, jin Karen yana shunshunarta yasa tafara ihu tana bubbuga k'ofar amma taji an rufe kofar daga waje,
Afrah ce tarufe kofar tanata dariya yau bazan barki ba harsai karennan ya cinyeki mayya kawai,
Suna cikin haka motar Daddy tayi horn jin Daddy zai shigo yasa Afrah sake kofar tashige falo dagudu,
Minal kuwa ganin kofar yaki bud'uwa yasa tafara tsalle acikin d'akin tana ihu tsakaninta da Allah, Daddy ne yaji ihun yayi yawa sai kawai yabud'e kofar Jin anbud'e kofa yasa Minal fita dagudu mamakine yakama Daddy meya kawota d'akin kare? Cheww wannan wawiya ce wallahi  ke...ke ubanme kikeyi ad'akin kare? Minal ko jinshi batayi tsabar tsorata. Tsawa yakuma daka mata keba tambayarki nake ba? Ubanme kike ad'akin kare?
Ki..kitchen nake nema, kitchen d'in anfad'a miki nan gidanku ne? Mayya wayasan ko nama kikazo nema.
Wallahi ba nama nake nemaba Hajiya babbace tace min in dafa mata shayi....la'ila ha illallahu ke Aljana bakya tsoron Allah, nida nake d'aki tin d'azu ina bacci taya zance miki kibani shayi cewar Hajiya babba, wacce take tsaye abayan kofa tin shigar Daddy.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now