page 28

359 18 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 28...

"Janyota jikinshi yayi ganin yanda ta tsorata"

Yace "beauty kidaina janyo ina miki tsawa wallahi banason wani yaji tsorona ko kad'an"

Jikinta rawa yake sosai tunawa datayi, akwai watarana da Madina tace mata idan mutum yana binka a hankali to akwai abinda yake bukata,
Azuciyarta tace "nashiga uku yau na lalace, Ashe da gaske yankani zaiyi? Subhanaka inni kuntu minazzalimin"

Bilal janta yayi zuwa cikin toilet yahad'a mata ruwa me zafi, yace "shiga kiyi wanka ina zuwa"

A tsorace takeyin komai harta gama wankar, Bilal ne yashigo da towel babba da karami, d'aura mata yayi kafin yariko hannunta yakaita cikin d'akin, mai yashafa mata tareda sa mata sleeping dress yace "ki kwanta kihuta kafin gobe muje Mumbai Dan acan me yankan kai yake zama"

Firgita tayi zata tashi Bilal yayi saurin maidata yace "haba beauty ina zaki? Kefa bakya tsoro kin manta lokacin da kike min rashin kunya a Company? Ai dama barinki nayi sai yanzu zan rama"

Minal sai kikkifta idanu take, jin yace zai rama abinda tayi mishi, cikin murya me sanyi tace "yaya Bilal na rantse da Allah Madina ce take zugani Amma bazan kara maka rashin kunya ba Dan Allah kayi hakuri"

Kiyi kwanciyarki nidai bazan hakura ba, yana fad'an haka yashiga toilet d'in shima yayi wanka daganan yayi Alwala yazo yayi sallah raka'a biyu kafin yashafa lotion nashi mai kamshi, taje suman kanshi yayi, shima yasa rigan bacci yahau gadon tareda rungumeta, Minal tanajin ya rungumeta tafara mutsu mutsu Amma yaki sakinta saida ta hakura Dan wuya.

_Asuba tagari_

"Acan gidansu Bilal kuma hankalin Sabir ya tashi sosai ganin Bilal bai kwana agida ba, zuwa d'akin Daddy yayi yace " Daddy banga yaya Bilal ba bai kwana agida ba, ko kasan inda yaje? Hankalina duk ya tashi"

Daddy yaji maganar kamar Almara, "badai Bilal yayi zuciya bane yabar gidan? Nashiga uku ina yakai takaddun gidajenshi da company nashi?"

Cikin firgici yacewa Sabir "kadubashi a garden?"

Sabir yace "babu inda ban dubashi ba Daddy"

Daddy yace "OK kacewa duk mutanen gidan damasu aiki su had'u a babban falo ina zuwa"

"OK Daddy"

Da ma'aikata da mutanen gida duk sun taru a babban falo, kowa yana addu'an Allah yasa lafiya,
Daddy ne yashigo falon yasamu kujera ya zauna, gyaran murya yayi yace "a cikinku wayasan inda Bilal yaje?"

Shiru falon yayi babu Wanda ya Amsa,
Cikin tsawa Daddy yace "ba tambayarku nake ba?"
Baba me gadi ne yace "Alhaji jiya da safe naga yad'au motarshi yafita".

What?
Yafita da mota?
Kai wani irin jahilin me gadi ne?
Kana sane da shi Makaho ne kuma kabarshi yafita?
To duk inda yake kaje ka nemoshi Dan bar shirya rabuwa dashi yanzu ba"

Baba me gadi ne yace "Alhaji Dan Allah ayi hakuri zan nemoshi"

"Karma ka nemoshi"
Cewar Daddy.
Kowa ya watse a falon ana tirr da halin Daddy na rashin girmama na gaba dashi.

Bilal kuma da Asuba ya tashi Minal yace "oya tashi kiyi wanka mutafi don mutane dayawa suna zuwa"

Minal zuwa wannan lokacin ta Riga tabarwa Allah komai, wankan dayace tayi shi tayi sannan ya taimaka mata tasa kaya,
Shima yayi wankar tareda sa kaya me kyau,
Sallan Asuba sukayi kafin Bilal yariko hannunta yace "muje ko?"

Binshi tafarayi kamar statu.

Motar haya Bilal yakama musu zuwa kwalkwata, sun sauka a City Hospital Kwalkwata dake cikin Kasar India,
Hannunta Bilal yarike suka shiga wani babban office, Sallama Bilal yayi kafin suka shiga, wani Ba indiyene zaune akan kujerar doctor, ganin Bilal yasa yafara murmushi tareda mikewa yace "you're welcome Mr Bilal"

Bilal dariya yayi yace "thank you Dr Shekhar"

Dr shekhar ne yace "namastey Mr Bilal"

Bilal yace "namastey"

Juyawa yayi wajen Minal yace "namastey ma'am"

Minal jin yaren take kamar na jinnu, lalub'o Bilal tayi ta b'uya a bayanshi.
Tace "yaya Bilal Dan Allah kabasu hakuri banajin yaren"

Dariya Bilal yayi yace "to ai saiki fad'a musu ko?"

Dr shekhar yace "have a sit"

Zama sukayi Bilal yayi mishi bayanin duk abinda yafaru da harshen India.

Suna gama maganar Dr shekhar yakira wata nurse yace mata Asawa Minal uniform yanzu za'ayi mata aiki sabida idan an ba'ayi da wuriba zai iya zama babban matsala.

"Okay sir"
Shine abinda Nurse d'in tafad'a,
Tareda riko hannun Minal tace "let's go ma'am"

Minal taki sakin Bilal sai kuka take da rokanshi Dan Allah yabarta araye.
Dariya kawai yske, dakyar ta sakeshi suka tafi da nurse d'in.

_✔ote & comments_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now