Page 8

381 26 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

 
   *Page* 8

"Ɗakinshi Daddy yakaishi domin ɗaukar makullin,  suna zuwa Bilal yaɗauko makullin har zai mikawa Daddy amma kome yayi tunani Oho, sai yace Daddy ina hanunka ga makullin,  hannu Daddy yamika mishi yakarɓi makullin yana wani irin murmushi wanda shi kaɗai yasan ma'anarshi. Azuciyarshi kuwa yace gaba kaɗan rayuwarka zaka bani Yaro"
************

Da yamma  suna Zaune afalo Daddyne yashigo falo a rikece yana kiran Bilal?  Bilal?  Bilal,   Hajiya Salamatu ce ta amsa tace lafiya kuwa kake kiran Bilal da ihu haka?

Hajiya ina Bilal yau Allah yatona Asirin Wanda suka aikata mishi haka,  yana faɗin haka ya karaso inda suke ya buɗe wata Video awayarshi yace kalli kugani wanda kayarda dashi shizai cuceka, 
Sa Videon yayi a handsfree yanda kowa zeji me ake cewa,
Wasu mutanene guda biyu sun rufe fuskarsu da baƙin kyalle suna cewa Ai Latif ne ya aikasu su watsawa Bilal Acid a idonshi sabida wani dalili nashi wanda basu sani ba.

What!!! Latif cewar Bilal,  no Daddy ban yadda ba Latif bazai taɓa cutar dani ba..... Dakata!!!  inji Daddy kai wani irin mutum ne?  Baka jin abunda suke faɗane?  Ko sharri zasuyi mishi?  Aina suka sanshi dazasuyi mishi sharri?  Shi kaɗaine aduniyar dazasu tsallake kowa suzo kanshi?

"Kalamun Daddy sunyi matukar tasiri akan Bilal,
Magana yakeson yayi amma bakinshi yana rawa tsabar firgitan dayayi.
ganin haka yasa Daddy juyawa yasaki wata murmushi wanda shikaɗai yasan dalilin yinta.
azuciyarshi yace Yanzu aka fara wasan"

*************************

"Minal tana cikin kuncin rayuwa, babu inda Umma bataje neman aiki ba amma takasa samu,  kamar kullum yauma suna zaune acikin gida suna hira Minal ce tace Umma?
Umma tace Na'am 'yata.
Umma inason in fara zuwa BARA....  Bara kuma Minal?  Yaushe kika fara son duniya? Meyasa bazaki hakura da halin damuke ciki ba?.

Minal ce tafara zubar da hawaye tace "Umma ya bazanyi bara ba?  Kiduba irin halin damuke ciki abinci ma neman gagararmu take,  hannayenta biyu taɗaga tace ya Allah ka karɓi rayuwata, Allah kana ganin duk abinda yake faruwa,  Allah ka gaggauta ɗaukan rayuwata kafin ta ɓaci gaba ɗaya...  Ta karashe maganar tana wani irin kuka mecin rai,  rungumeta Umma tayi sukaci gaba da kukan tare gwanin ban tausayi"

"Latif?  No... Kodai mafarki nake ne Daddy?  Bilal durkusawa yayi agaban Daddy yarike kafafunshi yace Dan Allah Daddy kafaɗan gaskiya Latif ne yake neman hallaka rayuwata?  Latif ne ya makantar dani?"

Ɗagoshi Daddy yayi ya rungumeshi yana bubbuga bayanshi yace "my son idan baka gani ai kanaji,  kasan dai babu yanda za'ayi mutanennan suce shiya aikesu, may be ma kuɗinsu ne be basu ba,  amma insha Allah yau Latif baze kwana agida ba,  agidan yari ze kwana sabida yayi kokarin kisan kai"

Aa Daddy kar ayi saurin yanke hukunci,  ayi bincike tukunna kar muzo muna dana sani.... Enough! Karka kara samin baki acikin maganarnan,  kai Amana ne awajena idan har nazuba ido wata rana kasheka zasuyi,  wallahi, Wallahi,  wallahi,  nayi rantsuwa sau uku kuma nasan muhimmancin rantsuwa,  bazan bar Latif da Abbanshi ba dukansu saina kai karansu kotu kuma dolene ayanke musu HUKUNCIN KISA!!! sabida sunyi kokarin kashe ran da babu hakki.

idan kaga Daddy alokacin zakayi zaton babu masoyin Bilal kamarshi,
Bilal gyara glass nashi yayi yaci gaba da kallon Daddy aɓoye,  dashike yanzu yanasa baƙin glass irinna makafi.
Yace "to Daddy duk abinda kayanke daidai ne sabida kai amatsayin uba kake awajena, bayan iyayena babu wanda nakeso saikai Daddy, 
Na Amince akama Latif  amma ina neman alfarma ɗaya awajenka"

Faɗi alfarmar dakake so nikuma nayi maka alkawarin zanyi maka.

"Bilal  yace Daddy dan Allah  kar ayiwa Latif HUKUNCIN KISA!!! Ayi mishi horo iya abinda yayi niyan aikatawa......

_✔ote comment & share_

✍🏻   *JIDDAH S MAPI*

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now