NADAMATA! PART ONE

Por Basira_Nadabo

2.8K 352 53

Labari ne akan Baseera Bashir Bilal, ku bi yo ni don jin yadda za ta kasance. Más

POST TWO
POST THREE
POST 4
POST 5
POST 6
POST 7
POST 8
POST 9
POST 10
POST 11
POST 12
POST 13
POST 14
POST 15
The Cast
POST 16
POST 17
POST 18
POST 19
POST 20
POST 21
POST 22
POST 23
POST 24
POST 25
POST 26
POST 27
POST 28
POST 29
LAST POST 30

POST ONE

373 19 0
Por Basira_Nadabo


MIKIYA HAUSA WRITERS KADUNA STATE

Almost True Life Story

Basira Sabo Nadabo

PART ONE

POST ONE

Sadaukarwa: Sani Ahmad Giwa

13/08/2019

     BARKAN MU DA SALLAH. TaqabbalAllahu Minna Wa Minkum fans.

KADUNA/ HAYIN RIGASA

Sunana Baseera Bashir Bilal Kawaye na min inkiya da triple B. Na kasance mace mai son ado da kwalliya sannan ina son saurayi dan gaye mai daukar wankan da zan iya shiga da shi cikin kawaye na. Ga ni Allah ya yi ni da son kudi haka ina son zuwa bikin girma da 'ya'yan wane da wane suke halartar bikin, wannan dalilin ya sa bani da kawa 'yar talaka duk da nima Allah bai sa na fito a cikin 'ya'yan masu kudi ba, mahaifina Malam Bashir mai gyaran takalmi ne don da kyar muke iya cin abinci sau uku a rana, d'ayar ma da ya ya ake samun ta balle har uku, wannan ya sa na tsani kaina dana fito a 'yar mai gyaran takalmi, Umma ta surfe ta ke yi a biya ta naira ashirin ko sama da hakan mu uku ne a gurin iyayen mu, Yaya Sani da Yaya Bilal sai ni 'yar autar su kuma ni ce Allah ya yi ni mai dogon buri ga shegen son kudi, ga shi bana kawance da 'yar talaka dai-dai ni don gani nakeyi ajina zai fadi warwas a kasa. Yau ta kama ranar sallah ranar da kowa yake farin ciki da murnar saka sabbin kaya, amma ni a gurina ba hakan bane don bani da abin sakawa, zaune nake a akurkin dakin mu wanda ya kasance ni da Ummata yayin da Abbana da su Yaya Sani dakin su daya. Da kyar muke malejin biyan kudin hayar dakunan guda biyun da muke zaune, kara kallon akwatin karfen da Umma ta bani na zuba kayana a ciki nayi , tsaki nayi mai cin rai daga cikin zuciya ta tsakin ta fito kara tsanar kaina nayi dana fito a gidan talakawa irin Malam Bashir mai gyaran takalmi. Sura da siffar jikina na bi na kalla ba wai nafi kowa kyau ba ne amma kuma ba za a sakani a layin munana ba, sannan ina da diri dai-dai jikina hips dina bayyi yawa ba kuma bai yi kadan ba, ni ba doguwa ba ce kuma ba gajeriya ba, sannan ni ba fara ba, ba kuma za a kirani baka ba, in ina tafiya babu abinda ke jan hankalin maza zuwa gare ni sai yadda kuguna yake juyawa. Ba don ni nake yi da kaina ba sai don haka halittar ta ke, ina da dogon hanci da dan fadaddan baki ba shi da tsawo kuma ba shi da girma, idanuna farare ne tas kamar takarda, ina da gashin ido dara-dara da tsawo haka ma gashin kaina yana da tsayi amma ba har gadon bayana ba, dukiyar fulani na a cike suke dai-dai jikina ni kaina ina na kalla suna birgeni balle kuma maza da yawancin su abinda ke kawo su gurina kenan, ina da son duniya da abinda ke cikin ta amma Allah bai yi ni mai bin maza ba, sai dai d'an abinda ba za a rasa ba kuma ina kiyaye kaina da kokarin kaucewa hakan, ba na saurayi talaka kuma ba na saurayi mai roba-roba sai masu kudi da mota kirar Benze ko Honda EOD, sannan kyakkyawan saurayi ajin farko na shiga biki da kere wa sa'a. Kara kallon kayan nayi don babu wanda zan iya sawa a ciki in fita zuwa in da zani, Umma ce ta shigo tare da 'kare min kallo sannan ta ce.

"Me zan gani haka ke nan Baseeratu?"
      Kallon jikina na fara yi sannan na ce.

"Me kuma na yi Umma don Allah? Kuma ke kullun sai ki dinga ba ta min suna wai Baseeratu haba don Allah!"
    Ta yi maganar kamar mai shirin kuka

"Yo to dama me zan kiraki da shi ko ba da shi ubanki ya yanka miki ragon suna ba?"

"Haba don Allah! Haba yanzu fisabilillahi dan sunan zamanin da ake yayi ma kun kasa samin wai sai tsohon sunan da tuni aka dai na yayin sa wai Baseera, kuma bayan na yarda ina amsawa kuma har da tu kike kara min ni wallahi gidan nan duk kun tsaneni bakwa so na!"
    Sai hawaye sharrrr muryar ta har rawa take yi saboda tsabar bakin ciki, Umma ta tsaya kamar gunki tana kallon ikon Allah ga wani tukikin bakin ciki da ke taso mata ta ce

"Ai bani ce zaki tara da zancen suna ba ubanki me nanin takalmi shi yafi da cewa daki fada masa, domin shi ne ya zaba kuma ya saka miki sunan shiryayyiyar yarinya mai kama da 'ya'yan albarka. Wallahi Baseeratu ki kiyayi duniya wanda bai zo ba ma tana zaman jiran sa balle ke da kika shekara ashirin da hudu a cikin ta."

"Ni da ma an tsaneni a gidan nan babu me sona ga shi nan har baki ake min. Wayyo Allah na shiga uku!"
       Ihun tayi har da daura hannu a ka. Umma ta yi saurin ce wa.

"Ba baki nayi miki ba tunatarwa ce, kuma ban taba jin na tsane ki ba Baseeratu sai dai mugayen halayyar da kika dauko ne na tsana amma ban tsane ki ba."
      Umma ta karashe maganar da kwantar da murya cikin sigar lallashi. Sallamar Abba ne ya sa Baseera saurin hadiye kukan ta, don da ma Abba mutun ne mai zafi baya wasa da yaran shi, in ka gan shi zaune gaban wuta har yana dariya to da Yaya Sani ne, Umma macace mai sanyi ba ta da hayaniya haka zalika ba ta da fada tana da yawan wasa da mu musamman ni, tana kokarin nuna min duniya da rudanin cikin ta amma idona sun rufe har bana iya ganin munin arzikin sai kyawun ta. Dariya Umma tayi ganin yadda a dan lokaci ka dan na shiga cikin rigar nutsuwa, ta ce.

" 'Yar neman albarka ai da kin ci gaba da kukan in yaso in mai nanin ya shigo sai ki fad'a masa mun tsane ki kuma ba kya son sunan daya sa miki sannan kiyi masa kukan shagwabar da kike mi...."
     Baseera tayi saurin rufe wa Umma baki idon ta ya cicciko da kwallar tsoro ta ce.

"Don Allah Ummata kiyi shuru kar Abba ya jiyo ki wallahi zai iya duka na"
     Murmushi Umma ta yi tare da girgiza kai ta ce.

"Allah ya shirya min ke Baseeratu kuma ya baki ikon zubar da munanan halayyar ki."
       Tana kaiwa nan ta yi waje tana murmushi don ta hango tsoro fal cikin idon Baseera, dakin Abba ta shiga bakin ta dauke da sallama, sai dai yanayin fuskar sa kawai ya tabbatar mata da mijin ta yana cikin damuwa da sauri ta koma waje ta dibo masa ruwa a randa mai sanyi ta kawo masa, ya amsa yasha sannan ta zauna kusa dashi hannun sa na dama ta rike tana shafawa a hankali, sannan ta ce.

"Wallahi talauci da damuwa ba masu tabbata ba ne komai yana wuce wa har ya zam to kamar ba a taba yin saba, kayi hakuri da rayuwa a duk yadda tazo maka, kuma kayi kokarin yaki da duk damuwar da zata saka cikin damuwa. Ba zan iya kallon ka a cikin damuwa ba ko kana tunanin zuciya ta zata iya jure ganin cikin takura ne? A'a Abban Baseeratu ba zan iya ba kaima sa nin kan ka ne hakan, ka sa ni Allah shi ne yake d'aurawa kuma yake yaye wa, sannan duk halin da muka shiga da sa nin Allah, in dai don tamu ne iyalan ka mun yafe maka kuma ba zamu in gizaka yin abinda bai dace ba har ka kaucewa Allah. Kayi hakuri mijina muna son ka damuwar ka damuwa ce a gurin mu, kai ne farin cikin mu kai ne hasken dake haskaka mu a duk lokacin da duhu ya lullube mu, karka manta ina son ka kuma ba zan taba daina son ka ba har karshen numfashi na."
       Tunda Umma ta fara magana Abba yake kallon ta lokaci daya kuma bakin ciki da damuwar da yake ciki suke raguwa, farin ciki ne mara misaltuwa ke dawainiyya da shi har zuwa karshen maganar ta, da d'ayan hannun shi ya riko hannun ta da shi ya ce.

"Hakika samun ki a matsayin mata babban nasara ce a rayuwa. Ban taba dana sa nin kasancewar ki uwar 'ya'yana ba Aisha, tun da jajayen sahun mu in ina cikin damuwa ko bakin cikin rayuwa kike zaunar dani ki bani ruwan sanyi in sha, sannan ki zauna tare da rike hannun dama ta kina min tafiyar tsutsa sannan kina kwantar min da hankali, ba kya taba bari na har sai kin ga na dawo cikin nutsuwa ta. Da ace duka mata haka suke kamar ki wallahi da maza da yawa sun yi da cen samun mace ta gari, ki sa ni babu ta biyun ki a guri na kece daya tilo Allah yayi miki rahama Aisha, gafarar Allah su ci gaba da tabbata a gare ki nima a ko da yaushe ina son ki kuma ba zan taba daina son ki ba Umman Baseera."
    Tunda Abba ya fara magana Umma take murmushi don dama farin cikin mijin ta shine na ta, kara karyar da murya ta yi sannan ta ce.

"Mene ne ya bata maka rai a wannan rana ta sallah karama?"
     Ajiyar zuciya ya sauke tare da ce wa.

"Wallahi Aisha nayi yawo ko namar dari biyar ne in kawo cikin gidan nan amma abin ya faskara, kuma kina sane da halin Baseera, ban jin ta Sani da Babana (Bilal) sai ta ta. Yanzu zata bi gidan kawaye don cin nama, ni kuma wannan halin ne bana son ta da shi, ga shi har yanzu tunda ta gama difloma (diploma) ba ta kara ci gaba da karatun ba, yanzu kudin da zan aikawa Bilal ma babu ga Sani ya ce min sun kusa fara firojet (project), itama kudi ne ake bukata na rasa yadda zan yi da rayuwa ta duk in da na buga babu, dan gonar guda uku duk mun siyar da biyu saboda rayuwar yaran nan sauran d'aya shi ma mun ajiye ne saboda kar maganar auren Baseera ta taso babu komai. Kina sane da kudin duka yaran nan suka yi karatu kuma da shi nake son siyan wannan gidan, Aishatu rayuwa ta min zafi komai ya tsaya cak wallahi babu in da yake motsi!"
        Da rawar murya ya karasa maganar idon shi sun ja. Umma ma zuciyar ta ta karye amma bata son nuna gazawar ta sai ta yi ta maza cikin jarumta ta na murmushi sannan ta ce.

"Innalillahi wa inna Ilaihir rajiun! Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni min khairan min haa, mijina ka ambaci wannan addu'ar?"
     Girgiza kai yayi

"Dole musiba ta yi mana yawa amma dai yanzu mu ci gaba da karantawa har Allah ya kawo mana mafita."

____________________________

WARNING!!!

Wannan labarin kirkirarre ne banyi don cin fuska ko kuma kwaikwayar wani/wata ba, in hali da suna sun zo irin naki/naka kiyi hakuri ba don ke nayi ba sai don fadakarwa kamar yadda muka saba. Akwai abinda ya faru a gaske daga ban garen labarin kuma nasan wacce abin ya faru da ita, sannan har yau da nafara rubutun nan tana cikin nadama akan abinda tayi a baya. Allah yasa mufi karfin zukatan mu. Amin

Basira Sabo Nadabo Ce

Seguir leyendo

También te gustarán

43.9K 1.8K 18
Story about a married couple who's life was so toxic to live in. ⚠️ !!!𝗔𝗧𝗧𝗘𝗡𝗧𝗜𝗢𝗡!!!⚠️ ♡ This story is going to contain domēstic abu$e and m...
116K 12.2K 71
TaeKook Non Fanfiction #1 nonfic #1 nonfanfiction #1 nonff #1 nonfanfic 2023.12.09 2024.
49.5K 1K 26
loni, is a young girl in her teens who has a disability that effects her everyday life, follow her on her journey to happiness.
40.9K 134 6
ကျွန်တော် ၈ တန်းတုန်းက တစ်ကယ်ဖြစ်ခဲ့တဲ့ ကိုယ်တွေ့ ဆရာမနဲ့ကျွန်တော်ရဲ့ ဇာတ်လမ်းလေးပါ။