DARE DUBU

By PrincessAmrah

12.7K 1.6K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... More

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 43- Class Rep.
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 30- Visiting

182 24 0
By PrincessAmrah

Page 30

Ina jin Umma ta kira Kawu Danladi ta sanar da shi na samu mai neman aurena kuma yana son ganawa da su, ya ba shi lokaci sannan suka yi sallama ta yanke kiran.

"In ban da addini da al'ada da suka farlanta neman aure a wurin maza kuma makusantan mutum, sannan dangin uba, wallahi da babu dalilin da zai sanya ni komawa ta kan dangin mahaifin nan naku Khairi. Ni ban taba ganin mutane marassa kirkinsu ba, wadanda ba su damu da diyan dan'uwansu ba. Tun da mahaifinku ya bar duniyar nan ko turmin atamfa babu wanda ya taba dauka ya kawo min da nufin in dinka muku, ko kuma wani taimakon daban. Duk da irin kokarin da ya yi da su a lokacin da yake raye.
Har gara matan ma, tunda sukan wanko kafa su zo su duba lafiyarku. Haka lokacin da aka sace ku din nan, da kukana da komai na je neman taimako amma babu kwandalarsu da suka dauka suka ba ni. Shi Alhaji Sambo ma kai tsaye ya ce ba zai bayar da kudinsa ga 'yan fansa ba, haka na baro gidan nashi cike da kunar rai da kuncin zuciya. Shi ya sa ma ko da za a je neman auren Safra ban nufi kiran sa ba sai na kira Danladi tunda ya fi shi kirki duk da shi din ma dai sai a hankali. Amma ko ba komai an tarbe su da mutunci, duk da babu ruwa ko lemo amma shimfidar fuska ai ta fi ta tabarma.
Da alama iyayen Aliyun masu dattako ne in dai yadda yake haka su ma suke, to gara wurin Danladin za su fi samun tarbar mutunci a kan shi wancan mai kudin da ba su da amfani sai gare shi da iyalinsa. Ramin kura ne daga shi sai 'ya'yansa."

Na yi shiru ina sauraren ta har ta kai aya.
Jin na yi shiru ya sanya ta kallo na sai ni ma din na kalle ta, ta gyada kai hade da guntun tsaki.
"Mutum ya yi ta yi miki magana eh ko a'a ma ta gagara. Ni kam na rasa wace irin mutum ce ke."

Murmushi na yi na ce
"Allah Ya ja da ran Hajiya Ummana."
Na fada jikinta.
"Ni daga ni kar ki karya ni ki yi wa autata asara."
Bata fuska na yi ina gunguni,
"Auta ce kadai mutum ai ko."
"Eh mana, daga ke har Safran nan da watanni kadan za ku tafi ku bar ni. Ni da autar dai za mu ci gaba da rayuwa kafin mai jirgin sama ya zo neman aurenta."
Ta karasa tana dariya. Ni ma dariyar na yi ina tuna wasu lokutta can a baya, lokacin da muke zama mu yi nishadi har da Ummu, su hade min kai ita da Umma suna tsokana ni kuma Mama ke shigar min idan tana nan.

"Tashi ki kira min Aliyu in fada masa yadda muka yi da Danladi. Kira shi maza ki hada mu."
Ban musa mata ba na mike na dauko wayata daki na latsa kisan sa.
Ko gaishe shi ban yi ba na fada masa Umma ce ke son magana da shi sannan na kai mata wayar na komawa ta daki. Ban san yadda suka yi ba dai sai wayata da ta kira ni na karba.
Babu jimawa sai ga texts message dinsa ya shigo;
"You're soon to be Mrs Turaki."

Gajeren murmushi na yi ina maimaita karantawa, wato dai Umma ta tabbatar masa da za a ba shi ni shi ya sa ya yi min wannan maganar.

Gani na yi ya kamata in je gidan Anti Maryam, amana ba ta ce haka ba. Yadda matar nan ta yi min halacci ba tare da ko sisinmu ba, bai kamata in yar da ita ba. Don haka na koma waje na sanar da Umma ina son zuwa gidan Anti Maryam ta ce ba damuwa. Sai Safra ta raka ni tunda ita Sadiya tana makarantar islamiyya.

A can muka wuni sai daf da maghriba muka dawo. Ana yin maghribar kuwa Haidar ya kira ni ga shi nan zuwa. Da ma ban sauya kaya ba sai kawai na zauna jiran zuwan sa.
Ba a jima ba ya iso, na ce masa ya shigo ciki. Umma na parlor suka gaisa ta kara jaddada masa zancen Kawu Danladi ya amsa cikin nutsuwa sannan ta ba shi wuri tare da sanya Sadiya ta kira ni duk da ina jin su daga cikin daki.
Bayan na fito na gaishe shi amma bai amsa ba sai wani irin mayen kallo da yake bi na da shi da wadannan mayatattin idanuwan nashi da kullum suke tamkar mai jin bacci. Kunyar kallon na ji na sunkuyar da kai ina tambayar shi Mami.
Sai a sannan ne na samu amsa.
"Mami na asibiti an kwantar da ita, yanzu haka ma daga can nake, na fada mata wurinki zan zo ta ce in gaishe ki kwarai."

Na dago kai na dube shi na ce
"Asibiti? Lafiya dai ko?"
"To da sauki dai za a ce. Hawan jininta ne ya tashi jiya da daddare aka kai ta asibitin shi ne suka rike ta wai sai ta dan huta kafin su sallame ta. Amma dai da sauki sosai gaskiya."
"To Allah Ya kara sauki. Amma me ya sa ba ka fada min ba bayan ko jiyan mun yi waya? Yau da safe ma fa mun yi waya da kai."
"Allah Ya ba ki hakuri 'yar gidan Mami. Ita ma fa ba ki ji yadda ta matsu ta gan ki ba wallahi, don kanwata Nusaiba ma cewa ta yi in kawo ta har nan ta gaishe ki. To dai tukunna, idan an sallame ta daga asibitin sai ta zo ko."
Na daga kai ina jin wani iri, wai kanwar saurayina ce za ta zo ta gaishe ni.
"Zan fada wa Umma, in ya so ko zuwa gobe da safe sai mu je mu duba Mamin da jiki, ni da su Safra. Ko?"

Fuskarsa ta fadada da annuri, da alama ya ji dadin maganar tawa,
"Ba damuwa Allah Ya kai mu."
"Amin."
Na amsa a hankali.

"Kin dai san hutunki ya kare ai ko? Jibi Monday za ki koma aiki."
Na daga kai ina duban sa."
"Better. Don kin san a fagen aiki ba ni da wasa. Ahmad Turaki nake."
Ya karasa maganar da dariya. Ni ma dariyar na yi ina tunanin ta yadda zan ci gaba da aiki a karkashinsa alhali shi ne wanda zan aura. Ga wata irin kunyarsa da nake ji.

Mun dan taba hira kafin ya ce min zai tafi. Na mike na taka masa har kofar gida wajen motarsa. Na jaddada masa goben kafin mu bar gida zan kira shi sai ya kwatanta mana dakin da take.
"Ina ganin ma kawai zan zo sai in kai ku. Kafin dai ku gama shiryawar ki kira ni zan zo mu je tare."
"Okay in shaa Allah. A mata ya jikin kafin mu zo."
"Da yardar Allah zan fada mata. Ki shiga gida Buttercup. Take care kin ji."
Na yi murmushi tare da komawa gidan, ina jin zuciyata tamkar ana busa ta da wani irin yanayin da na kasa yarda soyayyar Aliyu Turaki ce fam a cikinta.

A daren wannan rana dai babu abin da nake sai tunanin Haidar, har kusan dayan dare ina tunaninsa tare da amince wa kaina lallai na tsunduma tafkin kaunarsa. Ko ba komai kyautatwarsa gami da nuna kulawa ya taka muhimmiyar rawa wurin saye zuciyata. Na gamsu, na amince ina son shi har cikin zuciyata, sannan zan aure shi, sai fatan Allah Ya shige mana gaba.

Washegari da safe muka hau shiri, da ma tun a daren na fada wa Umma batun zuwa duba Mami ta kuma aminta. Mu ukun duka za mu je, da har Umman ma ta ce za ta amma na ce ta bari tukunna mu gani idan ba a sallame ta zuwa gobe ba sai ta je ko ita da Sadiya ne.

Ko da muka gama shiryawa Haidar na waje yana jiran mu. Sallama muka yi wa Umma ta yi mana fatan alkhairi sannan muka fice.
Cike da kunya na zauna a gaban motarsa, su Safra suka gaishe shi ya amsa yana tsokanarta wai ashe ita ma amarya ce.
"Komin dai abunki sai mun riga ki aure yarinya."
Ta yi dariya ta ce
"Babu komai, ai ni ma na fi son a yi auren naku manyan yayye don ba zan so yin kara'i ba."
Cike da nishadi muka isa asibitin Dara.

Yana parking na ji wani irin mummunan faduwar gaba, wanda har sai da ya gane sauyin yanayina. Ina kokarin fita ya ce in dakata, sai su Safra ne suka fita.
Kallo na ya yi amma sai na kasa kallon nashi saboda yadda nake ji duk raina babu dadi a dan kankanin lokaci, kamar dai wani mummunan abin zai faru da ni wanda ban sani ba.

"Me ya faru Buttercup?"
Ya tambaye ni da tattausar muryarsa.
"Babu komai..."
"No please. Kar mu yi haka da ke. Ke ma kanki kin san kin sauya, ba haka muka baro gida da ke ba. Ki fada min idan akwai wani abu."
Sai kawai na ji wasu irin siraran hawaye suna bin kumatuna.
A take na ga ya rude,
"Subhanallahi! Buttercup me ya faru? Na yi miki wani abu ne? Please ki daina kuka kin ji, ba na son kukanki ke ma kin sani."

Kokarin dakatar da hawayen nake amma na kasa. Shi kuwa duk ya rikice yana tambaya ta abin da ya faru amma na masa shiru, saboda ni ma idan za a kashe ni ban san me nake yi wa kukan ba, ban kuma san mene ne ya darsa min damuwa ba, illa dai faduwar gaban nan da na ji tun da muka dira cikin farfajiyar asibitin.

Cikin sanyin murya na kirkiro hujjar da ba ta da alaka da sauyin nawa, na ce

"Ba na son asibiti, sai ina tuna mummunar kaddarar..."
"It's Okay to. Da ma jikina ya ba ni dalilin kenan. Ki kwantar da hankalinki kin ji? Ki share hawaye mu shiga kar a gane kin yi kuka."
Ya miko min hankacif dinsa da ke fitar da wani irin ni'imtaccen kamshin turaren darej, na goge hawayen ina jin yadda kamshin ke ratsa hancina yana darsa min wani yanayi mai cike da kaunar mamallakin hankacif din.

"Now, smile."
Dolena na kirkiro murmushi, sannan ya bude gefensa ya fita ya ce in jira shi zai bude min, wai ni Queen ce yau tunda na fito tare da mijina.

Kai tsaye Amenity muka nufa, a Reception muka hadu da wadda na ji ya kira da Nusaiba, ta kuwa rungume ni, fuskarta cike da annuri tana yi mana sannu da zuwa.
"Na gan ki kyakkyawa fiye da yadda na yi imagining Aunty Khairi. Har ma kin fi Yayan kyau."
Ta fada bayan ta sake ni, amma still hannuwanta a cikin nawa.

"Hmm! Hade min kai kuke neman yi da alama. Thank God I have Halimatu that is always after me. Ko Sady?"
Ya fada yana kallon ta yana dariya.
Ta daga kai ita ma dariyar take yi.
Cike da wannan nishadin muka isa dakin.


Amrah A Mashi❤️

Continue Reading

You'll Also Like

8.2K 152 13
Labari ne akan wani rich,young and handsome dr whose mother is igbo by tribe while his father a Fulani..duk dunia babu qabilan daya tsana kaman Hausa...
FURUCI NA NE By Hauwa A Usman

Mystery / Thriller

43.7K 3.6K 37
"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki..... "ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin...
1.6K 73 13
KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not worry, for it was all destined...at what...
77.7K 6.3K 145
Admin ဆီက ခွင့်ပြုချက်မရသေးပါဘူး free တင်တဲ့ အတိုင်း တင်ပေးပါ့မယ် admin တွေ လာပြောရင် ဖျက်ပေးပါမယ်။ Start date -21•4•2024(Sunday) End date-