MIJINA NE! ✅

Aishatuh_M tarafından

92.4K 12.2K 1.9K

Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? ... Daha Fazla

Daya
Biyu
Ukku
Hudu
Biyar
Shida
Bakwai
Takwas
Tara
Goma
Sha Daya
Sha Biyu
Sha Ukku
Sha Hudu
Sha Biyar
Sha Shida
Sha Bakwai
Sha Takwas
Sha Tara
Ashirin
Ashirin Da Daya
Ashirin Da Biyu
Ashirin Da Ukku
Ashirin Da Hudu
Ashirin Da Biyar
Ashirin Da Shida
Ashirin Da Bakwai
Ashirin Da Takwas
Ashirin Da Tara
Talatin
Talatin Da Daya
Talatin Da Biyu
Talatin Da Uku
Talatin Da Hudu
Talatin Da Biyar
Talatin Da Shida
Talatin Da Bakwai
Talatin Da Takwas
Talatin Da Tara
Arba'in
Arba'in Da Daya
Arba'in Da Biyu
Arba'in Da Uku
Arba'in Da Hudu
Arba'in Da Biyar
Arba'in Da Shida
Arba'in Da Bakwai
Arba'in Da Takwas
Arba'in Da Tara
Hamsin
Hamsin Da Daya
Hamsin Da Uku
Hamsin Da Hudu
Karshe.

Hamsin Da Biyu

1.4K 184 15
Aishatuh_M tarafından

Sunyi kukan, sunyi dariya da labarin abubuwan da suka faru a cikin rayuwarsu watanni uku da suka shude. Ramlah tun tana so ta nuna fushin abun taga Lubnah nata janye jiki da maganar sai ta kyaleta. A lokacin data shaida mata cewar tanada juna biyu kuwa babu irin ihun da Ramlah batayi ba. Zaune take a kitchen Ramlah kuwa tana girka masu abincin dare, dan kuwa Rayyan yace sai bayan isha'i zaizo daukarta.

"Yanzu ke Lubnah, wayyo Allah na, na kasa yarda wallahi cikin nan gareki." Dariya ita Lubnah abun ya bata, yanda Ramlah take magana sai ka daka ita bata taba haihuwar bama.

"Kema idan aka bibiya wannan cikin naki tabbas akwai ajiyar Rayyanu ciki." Mamaki take can kasan zuciyarta yanda babu ko digo daya na san Rayyan daya rage a ciki. Dadi ma takeji yanda Allah yasa har tunaninta na ta sadaukar wa Ramlah da wannan wahalalliyar soyayya yazo mata, dan idan baccin haka ta tabbata da bazata taba yin farin cikin da take ciki yanzu ba. Kuma alamu sun nuna itama Ramlar tana cikin farin ciki.

Hararar wasa ta galla mata kafin ta rage wutar gas din ta dawo ta zauna gefenta, "Lubnah, nagaji da yanda kike basar da maganar nan. Bazan taba samun natsuwa ba idan har bamuyi maganar nan ba, Dan Allah." Yanda taga fuskarta ta sauya zuwa alamun yanayi na rashin jin dadi yasa Lubnah ta juyo a hankali ta riko hannayenta tana bata dukkan hankalinta waje daya.

"Ina jinki, Ramlah. Maganar mecece wannan da take neman saka man ke kuka? Ko fada kukeyi da Rayyan dinne har yanzu?" Yar dariya tayi Ramlah ko kafin ta bude bakinta hawaye sun sauko kan kuncinta. "Ke kike sakani kuka, Lubnah kullum banida kwanciyar hankali. Bansan meyasa kikayi abunda kikayi ba bayan ni shaida ce irin soyayyar da kikewa Rayyan, dan Allah meyasa kikayi haka?"

Kallon hawayen dake bin kuncin Ramlah tayi kafin tayi kokarin danne nata, dan idan ta biye mata suka fara kukan wannan abun yanzu babu mai iya tarosu. "Ramlah, yanzu ke miye amfanin wannan maganar dan Allah? Ba komai ya wuce ba? Yanzu kuma kowa yana cikin farin ciki? Kalli fah, ni ciki ma gareni." Dariya suka fashe da ita a tare ganin yanda tayi maganar kafin Ramlah ta kafeta da idanu alamar dole fa sai ta amsa mata. "Toh, ranar danace kije ki kai mashi abu a daki yana parking? Na biyoki da wayarki Dr Aliyu yanata kira naji duk abunda kuke cewa..." Jikin Ramlah saki yayi gaba daya dan bata taba tsammanin abunda yasa Lubnah tayi abunda tayi ba kenan. Allah sarki bawan Allah ta dauki alhakin shi, taita cewa shi yaje yace mata Ramlah yakeso.

"To aini bakiji nace ina sanshi ba ko? Dan me zaki sadaukar da soyayyarki a wajena? Lubnah tunda nake ban taba ganin mutum irinki ba." Kuka sosai Ramlah takeyi, dan ta tabbata kaf cikin rayuwarta babu mai mata irin soyayyar da Lubnah take mata.

Yar dariya Lubnah tayi, amma duk yanda taso ta danne hawayenta saia suka sauko. "To ai shi so ba sai ka furta a baki ba, Ramlah. bazance ga ranar daya fara sanki ba amma saida abun ya faru na lura da abubuwa da yawa wanda ya kamata ace na lura dasu, Rayyan yana maki soyayyar da bazai taba yiwa wani mutum ita ba a duniya. Kema kina sanshi, kuma kar kiman gardama," Ganin yanda Ramlah ta taso yasa ta fadi haka da yar dariya. "Kina sanshi sosai ma ba kadan ba, dukda ke karfin taki soyayyar baikai na yanda nashi yake ba, zaki iya hakura dashi amma kuma zaki dade cikin kunci dukda cewar bama ki gane kina sanshi dinba. Ko kuma kin gane a zuciyarta amma wani sashi na zuciyarki yana fada maki cewar haramun ne kiso wanda nakeso." Ajiyar zuciya Lubnah ta sauke, tana tunano irin bakar azabar da tasha lokacin da abun ya faru, saidai yanzu jin komai take kamar bai faru ba, babu  komai a zuciyarta banda zallar farin ciki.

"Rayyan ya riga daya furta bazai taba yin rayuwar aure cikin jin dadi tare dani ba, ke yakeso bani ba. Koda bai fadi hakan ba Ramlah bazan iya zama dashi ba saboda a kalamanki na tabbatar kina sanshi ni kuma a duniya banga abunda zan hana maki shi ba, koda kuwa Rayyan dinne a lokacin." Ganin yanda Ramlah ke kuka kamar zata shide har dariya yaba Lubnah, "To duk miye na kukan? Ke dallah malama ki saki ranki kishi soyayya da mijinki kinji? kar nayi aikin banza wallahi." A tare suka fashe da dariya.

"Toh, naje nama Haidar magana, shima yace ya yarda. Saboda dukkanmu babu abunda mukeso wanda ya wuce farin cikinki, Ramlah. Mun yarda mu auri juna kawai dan kar yan biki su gane an fasa bikin daya daga cikinmu, shima kar danginshi suga an fasa auren, and it turns out to be the biggest blessing of my life. Dan na tabbata da Rayyan na aura bazan taba samun irin wannan farin cikin ba." Rungume ta kawai Ramlah tayi tana dizgar kuka, tunani ma ta fara in har ya halarta mutum yama wani wanda ba dan'uwanshi na jini ba irin soyayyar da Lubnah takewa Ramlah.

"Allah ya saka maki da mafificin alkhairi, Lubnah. Bansan me zance maki ba, wannan soyayya da kike man Allah yasa ki shiga Aljanna. Allah ya bani ikon maida maki koda kwatan abunda kikai man ne." Addu'a take mata tun Lubnah na cewa amin tana dariya har ta tureta tace, "Ke ni dagani, wannan addu'ar ko makka na biya maki sai haka." Dariya kawai sukayi kafin Lubnah cikin dabara ta fara nusar da ita yanda zamantakewar rayuwa take, dan ta lura har yau ita da Rayyan din sai a hankali, dan ko yau saida sukasha bala'i tukunna ta taho.

Ramlah kuwa Allah Allah take Rayyan yazo ko dan ta roki yafiyarshi, dan babu abunda yasa wani lokacin kawai haka nan sai ta juye ta fara mashi rashin mutunci face in har ta tuno cewar kiri kiri ba kunya ba tsoron Allah yaje yacewa Lubnah wai ita yakeso, ashe ba haka abun yake ba. Tana dakin Lubnah ta sallame sallar isha'i taji muryar Dr Aliyu a parlour, saida gabanta ya fadi, ita koda tayi niyyar yau ko za'a tada duniya sai tazo taga Lubnah shaf ta manta da waye mijin, mi zata ce mashi? Lubnah dai ita ta yamutsa al'amuran nan.

Tana jin muryarsu suna magana gwanin ban sha'awa sai murmushi take ita kadai, can taji an fado dakin da gudu batayi aune ba taji mutum ya fada jikinta. "Ammiiii!!!" Da wani irin mugun ihu Hafsah tayi maganar, nan take idanun Ramlah suka ciko da hawaye ta rungume Hafsah tsam kirjinta.

"Hafsah am, oh Allah nayi missing dinki kamar kamar me, Hafsah." Da dariya me kayatarwa Hafsah ta dago tana kallon fuskar Ramlah, "Ammi kin kara kyau." Dariya Ramlah ta fashe da ita, "Kema kin kara kyau da girma diyar Ammi." Tun Hafsah na surutun da Ramlah ke ganewa har ya zamana bata ganewa binta kawai take da eh da kuma Aa. Har kasan zuciyarta take rokon Allah ya kara bata yara, wani bangaren na zuciyarta na tsoron kar ta kara haihuwar mai cuta dukda ta tabbata cewar Rayyan zai zama uban da kowane da zaiyi alfahari dashi, amma bataso ace yaronta ya kara jin zafi da radadin ciwo irin yanda Hanan taji. Tana san yara sosai, kuma tana tsoron haihuwarsu.

Jim kadan sai ga Lubnah ta shigo da kyakyawan murmushi, da muryar zolaya Ramlah ta furta, "Amarya bakya laifi, ko kin kashe dan masu gida." Dariya tayi tana mika ma Hafsah hannu, "Tashi kije Abba na kiranki kici abinci, yanzu zai maidaki wai." Nan da nan ta turbune fuska zatayi kuka, "Ammi anfa bamu good friday easter monday a school, nafa fada mashi, har jakar kayana tana mota." Rike hannuwanta Lubnah tayi, "Na bashi hakuri ai, amma yace sai kina cin abinci on time, maza kafin yace ya fasa bari ki kwana." Da gudu ta ruga ta fita tana tsalle.

"To ta dawo zama daku mana," Ramlah ta furta tana nannade dardumar da tayi sallah akai. Da ajiyar zuciya Lubnah ta zauna bakin gadon, "Babu yanda banyi dashi ya barta ba yaki, karshe ma dai yanzu su Hajia ne suka hana, wai kar in takura daga yin aure a kawo man diya. Nayi rokon har nagaji." Zama Ramlah tayi gefenta, "Allah sarki, idan an sauke tazo ta tayaku raino." Dukan wasa ta kai mata ta goce suna dariya.

Jim kadan sai ga kiran Dr Aliyu tana dauka ta juyo tana kallon Ramlah tana murmushi, "Yace wai tunda baki zuwa ku gaisa ga mijinki nan yazo yanzu kin fito ai." Abunda ta furta kenan bayan ta aje wayar, "Na shiga ukku, ni da wane ido zan kalleshi?" Gyale Lubnah ta zaro cikin wardrobe ta juyo tana kallanta da wasa, "Da wadannan tsiwatattun idanuwan da kika kalleni. Ke bansan munafurci, dazu ina kallonki kina ma Rayyan text wai yazo kinyi missing dinshi, tashi mu tafi malama."Da kyar Lubnah na dariya taja hannunta suka fita. Kanta kasa suka shiga falon suka hango mazan biyu already saman dining suna cin abinci, ita dai Ramlah mamakin karfin hali irin na Rayyan take, yama saki jiki hankalinshi kwance wai.

"Ah ah, Hajia Ramlah manyan baki. Nace ai tunda ga angon naki yazo kila kin fito a gaisa." Daurewa tayi tana yar dariya, "Ina yini Dr? Ai ina can da diyata anata bani labarin school, kuma ta kawo man kararku kunki kawota wajena." Zama sukayi a tare saman dining din. Yanda suka saki jiki suna fira yasa duk yanda Ramlah taso ta nuna wani abu kasawa tayi, dole ta koma itama kamar babu abunda ya faru, kamar dama tun can farko haka tsarin soyayyar ya fara har sukayi aure.

Suna kallon Dr Aliyu sai ririta Lubnah yake, abincin ma kamar ya tauna mata tanayi tana murmushin jin kunya, wani abun ma idan yace nunawa take bataji ba ko ta galla mashi hararar wasa, ita dai Ramlah murmushin jin dadin irin farin cikin da Lubnah take ciki takeyi, ko babu komai ta samu farin ciki mai dorewa. Ta kasan table din taji hannun Rayyan ya riko nata, juyawa tayi ta sakar mashi da wani kayataccen murmushi.

"Mu tashi mu tafi gidanmu muma," wani irin turbune baki yayi kaman karamin yaron dayaga abokinshi da abu shi baida shi. Itama shagwabe fuska tayi tana girgiza kai, "Amma nace maka nan zan kwana ko? Ga diyata ma can." Yanda ya kwalalo ido kaman wanda ta caka ma wuka yasa ta fashe da dariya, wanda hakan ya juyo da hankalin su Lubnah kansu. Neman zare hannunta take amma Rayyan yayi hanzarin mikewa tsaye tare da ita, yanzu ma sai ya sargafo hannayenshi saman kafadunta.

"Bari mu barku haka nan naga dare yayi." Ita dai Lubnah banda dariyar mugunta babu abunda take mata, har tazo zata shiga mota Lubnah ta mata rada a kunne, "Kawata ki saki ranki mana, nasan duk wannan kame gidan dan a gabanmu ne ko? Ayi maza inji kyakyawan labari." Juyowa tayi zata kai mata duka Lubnah tayi baya ta boye jikin Dr Aliyu wanda ya rungumeta a hankali.

"Aa Ramlah, a biman mata a hankali." Dariya suka fashe da ita har Rayyan suna masu saida safe da alkawarin zasu samu time suzo.

Suna fara tafiya ya juyo yaga shi take kallo ko kyaftawa batayi, rage gudun motar yayi yana kamo hannunta a hankali, "Ya dai, yan mata? Ba mun shirya ba tun dazu? Ko mun kara wani fadan ne ban sani ba?" Dariya ma maganar ta bata, wato har ya saba da fadansu yanzu. Dukan wasa ta kai mashi saman hannu yana dariya, "Ai nasan halin masifarki, fada man tun yanzu in baki hakuri ba sai anjima ba."

"Dan Allah ka daina." Hararar wasa ta bishi da ita, "Me kakesan ci? Muje na sai maka wani abu." Kamar wasa duk yanda yayi da Ramlah taki ji, snacks ta sai masu da yawa wanda yasan saidai su aje fridge su rika warming, karshe ma wani supermarket ta shiga, ko wajen da kayan mata suke bata kalla ba ta rinka kwasar mashi kaya kaman me saida ya nuna mata da gaske fada zasuyi idan bata daina jidar kaya haka ba. Wajen biya kau dama yanda ta hade rai yasan ba huruminshi ba ita ta biya kayanta yanata mamakin meya faru haka kawai.

Saida ya gama shigar da kayan cikin gida tukunna ya isketa kitchen tana jera wanda bazasu iya ci ba cikin fridge, katuwar robar ice cream kadai ta rage a gabanta, "Shima wannan ya mana yawa ai." Rufe kofar fridge din tayi ta juyo tana kallonshi da murmushi, kanta ko dan kwali babu, "Kwadayi nakeji yau na rasa me zanci kuma, muje muna kallo zakaga mun shanye shi." Dariya yayi ya riko hannayenta biyo yana zagaye nashi around her waist, "Fada man gaskia, kodai munyi nasu Lubnah ne muma?!" Dariyar da yakeyi yasa ta kai mashi dukan wasa tana zillewa, "Muje kar su fara maimaicin drama dincan, Rayyan. Kuma hakuri zan baka, ka tsaya ka saurara tun kafin yan bada hakurin su fasa." Binta yayi cikin falon yana dariya, "Haba, nidai nasan waccan siyayyar akwai cin hanci tattare da ita. Wannan soyayya haka?" Cokalin hannunta ta jeho mashi ya kauce yana dariya.

Okumaya devam et

Bunları da Beğeneceksin

1.2M 63.4K 50
အမိန္႔စည္း+သခြပ္႐ိုး ( ႐ွင္မႈန္းနံ႔သာ) အမိန့်စည်း+သခွပ်ရိုး ( ရှင်မှုန်းနံ့သာ) ခြင့္ျပဳခ်က္မရပဲ ငါ့အနားကထြက္ခြာခြင့္မျပဳနိင္ဘူး အသက္နဲ႔ခႏၶာတည္ျမဲေနသ...
12.7K 901 40
labari mai cike da cakwakiya, soyaayya mai zafi hadi da zanan kaddara. yaro dan shekara goma sha biyar ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa...
3.6M 362K 38
ခူးဆြတ္ဖို႔မေလာပါနဲ႔ တစ္ခ်ိန္မွာအလိုက္သင့္ေႂကြက်ေပးပါ့မယ္ အဲအခ်ိန္က်ရင္သာ တယုတယနဲ႔ေကာက္ယူပါ ေမာင္ရယ္
395K 24.6K 73
Labarin Zaid da Zahrah...."Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mai zaka amfana dashi acikin rayuwarka ? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci ? Na...