MIJINA NE! ✅

Bởi Aishatuh_M

92.4K 12.2K 1.9K

Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? ... Xem Thêm

Daya
Biyu
Ukku
Hudu
Biyar
Shida
Bakwai
Takwas
Tara
Goma
Sha Daya
Sha Biyu
Sha Ukku
Sha Hudu
Sha Biyar
Sha Shida
Sha Bakwai
Sha Takwas
Sha Tara
Ashirin
Ashirin Da Daya
Ashirin Da Biyu
Ashirin Da Ukku
Ashirin Da Hudu
Ashirin Da Biyar
Ashirin Da Shida
Ashirin Da Bakwai
Ashirin Da Takwas
Ashirin Da Tara
Talatin
Talatin Da Daya
Talatin Da Biyu
Talatin Da Uku
Talatin Da Hudu
Talatin Da Biyar
Talatin Da Shida
Talatin Da Bakwai
Talatin Da Takwas
Talatin Da Tara
Arba'in
Arba'in Da Daya
Arba'in Da Biyu
Arba'in Da Uku
Arba'in Da Hudu
Arba'in Da Biyar
Arba'in Da Shida
Arba'in Da Bakwai
Arba'in Da Takwas
Arba'in Da Tara
Hamsin
Hamsin Da Biyu
Hamsin Da Uku
Hamsin Da Hudu
Karshe.

Hamsin Da Daya

1.6K 190 59
Bởi Aishatuh_M

Zaune take tana dan juyawa tana kallon yanda office din yake, Lubnah tasan ba yau bace rana ta farko data fara shigowa office dinshi ba amma kuma sai yau ta natsu take lura da yanda wajen yake, ko dan kyaun da wurin yayi da tsari? Ko irin tarkacen takardun nan da likitoci ke tarawa shi nashi a kimtse suke waje daya. Murmushi tayi, a zuciyarta kuma Allah Allah take ya taho, ta kirashi yace a bude mata office din yaje ward round gashi nan yanzu zai gama.

Tana cikin wannan tunanin ta jiyo maganarshi a corridor din da alama hanzari yake dan umurni yake badawa kafin ya bude kofar. Kamar wata karamar yarinya haka ta mike da tsalle ta rungumeshi. Dariya Dr Aliyu yayi kafin ya rungumota yana rufe kofar office din da kafarshi. "Nayi missing dinki sosai da sosai, Lubnah." Wani taro taje port harcourt kwananta biyar. Duk kwanakin da tayi bata gida ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya bita, kullum cikin waya suke idan kuma aiki ya mishi yawa to tabbas suna chatting.

Dariya tayi tana kara makalkaleshi, "Kasan yanda nakeji wai? Kamar zuciyata ta fito." Dariya yayi ya dako da ita yana kallon fuskarta, har zuwa yanzu hannayenshi na rungume da ita. "Kinyi haske kin kara kyau, kodai wayau kika man kikaje kina cin dadinki?" Dariya tayi tana girgiza kai kafin a hankali taji saukar labbanshi saman goshinta.

"Ba nace ki kirani nazo na dauke ki a airport din ba? Ko duk missing din nawa ne yasa bazaki iya jira ba?" Daga kai tayi tana lumshe idanu dan sai yanzu data ganshi hankalinta ya kwanta ta gane irin gajiyar da tayi ga wani baccin wahala da yake neman karya jikinta. "Na kosa na ganka sai nayi bolt kawai nazo nan. Mu tafi gida, ko baka gama ba?"

Dariya yayi yana aje abu saman table dinshi kafin ya dauko makullin motar. Hannayensu rike dana juna kowannnen su farin cikin dake zuciyarshi bazai misaltu ba. Watansu ukku da aure amma irin farin ciki da kwanciyar hankalin da suke ciki basu taba tunanin zasu sameshi ba. Shi ya bude mata kofar saida ta shiga ta zauna kafin ya zagaya ya shiga mazaunin driver yana tada motar. Fita sukayi daga asibitin ya juyo yaga yanda ta lafe kan kujerar, dukda cewar da murmushi kan fuskarta amma kallo daya zaka mata kasan ba karamar gajiya tayi ba, idanunta rufe ruf alamar bacci.

"Anya kuwa Lubnah? Tun kafin ki tafi kike wannan yawan kasalar balle ace gajiya ne." Sauri tayi ta bude idanunta, dan ita kam batasan yan maganganun nan. Lura da yanayin fuskarta yasa ya fashe da dariya, "Ba daidai na fada ba, koma kiyi bacci ranki ya dade ai kin gaji dayawa." Yanda yayi maganar sai ya bata dariya. Pharmacy ya tsaya ya siya bau ita dai bata san menene ba, daga nan kuma taga yayi parking kofar gidan Hajia.

"Na dauka gida zamu nayi wanka na chanza kaya." Dan girgiza kai yayi a hankali, "Hajia tace mu biyo mu karbi abinci tunda yau dai kam bazakiyi girki ba ai. Hafsah kuma ta dameni idan kin dawo nazo na kawota, to idan mukazo yanzu ta ganki shikenan ba sai na dawo anjima ba, sai muyi zamanmu har dare tare." Murmushi kawai tayi suka fita suka shiga gidan tare. Sai ta tuno ranar data fara zuwa gidansu Aliyu, tsabar fargaba dakyar take daga kafa tana tafiya dan ita a tunaninta bazasu taba amsarta ba tunda su kam Ramlah suka sani.

Amma tunda take bata taba ganin mace mai mutunci da kirki irin na Hajia ba, bata taba ma nuna mata cewar ai ba ita da Aliyu zai aura ba. Karshen soyayya tana ganinta wajen baiwar Allar nan, dan wani loacin haka kawai zata kirata tace mata tayi abincin gargajiya yau ba sai tayi girki ba tunda ga aiki, kawai idan ta tashi tunda tana rigan Aliyu tashi ta biyo ta karbar masu abincin. Lubnah ba karamin dace tayi ba da rayuwar aurenta, dan koda auren soyayya tayi kila sai an samu matsala. Amma yanzu watansu ukku da aure ko sau daya basu taba samun sabani dashi ba.

Zaune suka samu Hajia falo ga Hafsah gaban tv tana kallon tana cin abinci ita kuma Hajia tana latsa wayarta. Dagowa tayi ta gansu da hanzari Lubnah ta zare hannunta daga nashi. "Mutanen port harcourt, Allah yayi?!" Murmushin dake fuskar Hajia wani irin kayatacce ne. Lubnah takawa tayi har inda take ta duka zata gaisheta Hajia ta mikar da ita tsaye ta rungumeta tana dariya, "Lubnah na fada maki bani san yan duke duken nan. To ya hanya? Kamar ma ko gida bakuje ba?"

Zama Lubnah tayi gefenta ko kafin ta amsa mata Hafsah ta rugo ta rungumeta tana dariyar farinciki, "Ammi!!! Nayi missing dinki sosai, kullum in Abba yazo nace ya kiraki sai yace wai kinyi bacci." Wani irin mugun kallo Lubnah ta bishi dashi yayi hanzarin daga hannuwa sama alamar rashin gaskia.

Dariya kawai Lubnah tayi tana rungumo Hafsah jikinta, "Kiyi hakuri diyar Ammi kinji? Yaushe zamu roki Hajia ta bar mana ke to?" Da hanzari Hajia ta girgiza kai a tare suka fashe da dariya, "Na fada maku wannan diya ta zama tawa, ta daizo maku hutun sati daya in anyi hutun makaranta, wannan zan bari." Su Lubnah har sun gaji da rokon Hajia, tun Hafsah na kuka saboda kin barinta da Hajia keyi taje gidansu har ta hakura. Shi kuma Aliyu yasan ba komai yasa hakan ba Hajia tanaso sai sun gama fahimtar junansu tukunna.

A nan gidan sukayi Sallah ta danyi abinci kafin Hajia ta hada masu da har abincin dare tukunna suka tafi Hafsah na ihun Ranar juma'a da an tashi makaranta can zata biyo. Sun kama hanya Lubnah ta dan sauke ajiyar zuciya, "Wai meyasa bazaka roki Hajia ta ba mana Hafsah ba? Tana san zama damu Allah."

Murmushi ya mata mai kwantar da zuciya kafin a hankali ya riko hannunta cikin nashi, "Tun ranar data fara zuwa gidanmu na fada maki bazata dawo ba sai ta samu kani ko kanwa, shima ba wai taita zama ba, Hajia da Alhaji bazasu bari ba, kila koni ban kaisu san yarinyar can ba." Dariya suka fashe da ita a tare tana girgiza kai.

"Rowa dai kake man, maganar kani da kanwa ai bata taso ba dan yanzu." Shidai baice mata komai ba yana dariyar mugunta ciki ciki har suka isa gida. Kitchen yakai komai ya aje kafin ya sameta daki har ta cire kaya daga ita sai towel tana zare ribbon din kanta.

"Wai kasan ribbon dinnan dana fada maka baya matse man kai ya bace? Bansan yanda akai ba na wahala a port harcout dincan. Wannan ma duk yanda na sakashi sai inji ya tamke mani gashi." Ranar daya fara ganin gashin kanta har mamaki yayi, wata irin cika gashin gareshi wacce bai taba gani ba, ga uban yawa ga tsawo kuma yayi da ita tayi relaxing tace ita tafiso. Wani lokacin in tana sharce kai har kuka take dan azaba gashi ko kitso batayi saboda jin zafin kai gareta.

Shigowa yayi ya aje yar ledar dake hannunshi saman gado kafin ya zaunar da ita yana kama gashin, "To kiyi kitso mana, Lubnah? Wannan gashin yana wahalar dake."

Dariya tayi tana tayashi warware inda gashin ya curkude, "Ni banma san yanda zanyi ba, tunda na tafi ban kara sharce shi ba, Haidar, yau nasan sai nayi ciwon kai tsabar wahalar da zansha." Gashi dai tana san gashin amma kuma komai nashi wahala yake bata. Yana kaunar yaji ta kirashi da Haidar, duk duniya ita kadai kece mashi haka da wannan sassanyar muryar tata.

"To ko a wanke gashin yau? Zan tayaki nasan bazaiyi zafi ba." Dariya tayi tana kwantawa saman gadon, bata damu da cewar towel ne jikinta haka ta kwanta tana kallon yanda yake kallonta da murmushi, "Nagaji, kuma wanka nakeso nayi kafin nayi baccin."

Ledar ya dauko yana kallonta, addu'a yake Allah yasa hasashenshi gaskia ne. "Wai miye cikin ledar nan kaketa rikeshi kamar rai?" Ita da wasa tayi amma shi har zuciya abun yakai. Zama yayi yana yunkuro da ita saura kiris towel din jikinta ya balle, "Haidar!" Yanda ta wani kidime sai abun ya bashi dariya ya mika mata ledar. Budewa tayi tana ganin PT strip ne ta dago tana kallonshi. "Wannan abun fah? Ni fa tun ranar da mukayi yace negative ban kara sakawa raina ba, Haidar. Banso na saka rai yazo ya zama negative, ga yanda ka damu ranar, ni har kuka nayi da daddaren."

Dan rungumo ta yayi a hankali yana sauke labbanshi saman bujawar gashin kanta, "Na sani, amma wannan karan ina tabbatar da cewar akwai. Kije ki gwada mugani, idan ma babu ai ba wani abu bane, kawai kar ace akwia ne kuma bamuyi taking preventive measures ba." Bata san tana mashi gardama, amma ita dan ta itace to bazata kara dubawa taga ko tanada ciki ba. Ko wata biyu basuyi ba taga bataga period dinta ba ta fada mashi, da ihu da murna sukaje suka siyo PT strip saida suka gama saka rai aka gane ba cikin bane, yanzu batasan irin wannan disappointment din.

Abun yana reading tayi hanzarin fitowa daga toilet din ta ajeshi kan bedside drawer ta juya zata koma, dan ita bata damu taga miye result din ba, tasan babu din amma ganin Negative daro daro zai kuntata mata zuciya. Da hanzari ya rikota da wani irin ihu a bakin shi yana dago da abun. Juyowa tayi ta zare ido tana jira taga meya gani. "Menene?" Zuciyarta wani irin bugawa take kamar zata fito kirjinta.

"Positive, Lubnah! it's positive!" Sai hawaye, rungumeshi tayi tana wani irin kukan farin cikin da bata taba dauka zatayi ba. Dagowa tayi tana kallon abun taga tabbas positive dinne. Da wani irin murmushi yake kallonta ya kara rungumeta jikinshi, kwantar da kanshi yayi saman kafadarta ya fara magana a hankali, "Thank you for this, Lubnah." Yar dariya tayi tana bugun bayanshi, "Jika kamar ance na haihu yau, mu jira sai wata taran tukunna ayi godiyar ko?" Dariya shima yayi ya dago yana kallonta da wani irin kallon da bai taba mata ba. "I guess ba tun yau ba, na dade, tun kafin ma Ramlah ta shigo rayuwata, I've been in love with you, Lubnah. Kawai ban gane ba ne, sai na ajeki a matsayin abokiyata amma tun ranar dana aureki i've realized i've always felt something for you. And wadannan wata ukun da mukayi tare couldn't have proved otherwise. Ina sanki, Lubnah, kinji?" Hawaye ne suka kara sauka saman kuncinta ta rungumeshi kam kam tana jin yanda wani farin ciki ke sauka saman zuciyarta.

Yau lahadi da yamma tana zaune, Dr Aliyu duk yanda tayi dashi cewar da safe ne taji tanasan taci tantalibo tunda taga wata mata ta saka tana neman inda zata samu amma yanzu ya fita ranta, bai yarda ba saida yasa aka nemo mashi a wani kauye na kaduna aka turo mashi a mota yanzu haka ya fita zaije tasha ya karba. Dariya abun yake bata, yanda yakeyi sai ka rantse bai taba haihuwa ba sai kan wannan babyn.

Kallon da takeyi ya gundure, mikewa tayi zata kashe tv din taji an kwankwasa kofa. Takawa tayi har bakin kofar tukunna tace, "Waye?" a sanyayyar murya, dan ian shine budewa kawai zaiyi ya shigo tunda ba kullewa tayi ba.

Jin anyi shiru yasa ta bude kofar a hankali, wanda ta gani yasa taji lokaci daya hawaye sun taran mata, "Ramlah!!!" Da kuka ta fada jikin Ramlah wacce itama kukan take tunda ta tsaye bakin kofar. Rungume juna sukai suna kuka kamar wadanda akawa aiken mutuwa. Tun ranar aurenshi basu kara haduwa da juna ba, ko a waya Lubnah da sun fara magana taga Ramlah zata mata maganar abunda tayi sai ta zille tace tana zuwa. Daga nan ma ya zamana bata cika daukar wayar Ramlah dan tasan maganar da zata mata ita kuma bataso, ko a chat da taga tana niyar kawo maganar bata kara mata reply sai kwana biyu. So take koda zata yarda suyi maganar da Ramlah sai ankai lokacin da ta fada soyayyar Rayyan tsamo tsamo wanda ko rashin mutuncinta bazata iya mashi ba.

Shigowa sukayi falo Ramlah ta tsaya tana kallonta tana balla mata harara, "Kin gama guje gujen ko kuma in koma nan da wasu watannin in dawo?" Dariya Lubnah tayi tana girgiza kai, "To Anty tsiwatu, nima masifar zaki sauke mani?" Duk yanda Ramlah taso ta nuna mata bacin ranta kan abubuwan da tayi mata kasawa tayi, kara rungumeta tayi suna kuka daga can kuma kowacce da abunda ya sako ranta a tare suka fashe da dariya.

Đọc tiếp

Bạn Cũng Sẽ Thích

32.5K 2.5K 52
Story of two lovers Hamdah and Abdul'ahad who were blindly in love but didn't realize until it was too late for them, yes they are meant to be togeth...
12.7K 901 40
labari mai cike da cakwakiya, soyaayya mai zafi hadi da zanan kaddara. yaro dan shekara goma sha biyar ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa...
115K 11K 62
Labari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//
726K 56K 81
It is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny...