MIJINA NE! ✅

By Aishatuh_M

91.9K 12.2K 1.9K

Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? ... More

Daya
Biyu
Ukku
Hudu
Biyar
Shida
Bakwai
Takwas
Tara
Goma
Sha Daya
Sha Biyu
Sha Ukku
Sha Hudu
Sha Biyar
Sha Shida
Sha Bakwai
Sha Takwas
Sha Tara
Ashirin
Ashirin Da Daya
Ashirin Da Biyu
Ashirin Da Ukku
Ashirin Da Hudu
Ashirin Da Biyar
Ashirin Da Shida
Ashirin Da Bakwai
Ashirin Da Takwas
Ashirin Da Tara
Talatin
Talatin Da Daya
Talatin Da Biyu
Talatin Da Uku
Talatin Da Hudu
Talatin Da Biyar
Talatin Da Shida
Talatin Da Bakwai
Talatin Da Takwas
Talatin Da Tara
Arba'in
Arba'in Da Biyu
Arba'in Da Uku
Arba'in Da Hudu
Arba'in Da Biyar
Arba'in Da Shida
Arba'in Da Bakwai
Arba'in Da Takwas
Arba'in Da Tara
Hamsin
Hamsin Da Daya
Hamsin Da Biyu
Hamsin Da Uku
Hamsin Da Hudu
Karshe.

Arba'in Da Daya

1.4K 214 31
By Aishatuh_M

Ko kafin ta kwankwasa sai taga kofar ma a bude take, shida tayi tana kaffa kaffa da tray din da yake hannunta har ta ajeshi saman tebur kafin ta dago tana kallon madaidaicin falon. Zata iya irga zuwanta bangaren Rayyan, kuma duk zuwan da zatayi zaman da take bai wuce na minti biyar. Tana shirin kiranshi a waya akan ya fito sai taji motsin mutum kila yaji alamun shigowarta.

Furkarshi har yanzu babu alamun annuri kwata kwata tattare da ita sai taji itama tatta duk ta kara rashin dadi. Mutane biyu da tafi so a rayuwarta duk da alamu suna cikin kunci. Zama yayi, wanda duk kokarin Rayyan akan yaga ya mata murmushi kasawa yayi, saidai itace ta mishi murmushin, "Abinci na kawo maka, kwana biyun nan ka saba kwana da yunwa, Rayyan."

"Allah sarki, kin kyauta kuwa." Tray din ya jawo gabanshi yana budewa, "Sannu kinji? Allah ya miki albarka." Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta. Tasan Mama kusan kullum sai tace mata Allah yayi mata albarka amma jin hakan daga bakin Rayyan ba karamin sanyaya mata rai yayi ba.

Murmushi tayi kafin tace 'Ameen.' Tana kallon yanda ya fara cin abincin cike da natsuwa dukda duk yanda yaso wajen ganin ya boye damuwarshi hakan ya gagara. Kasa jurewa tayi tace "Wai Rayyan me yake damunki? Na lura tun bayan dawowarku Lagos kake dawainiya da wani abu a ranka. Menene?" Kallonshi tayi taga ya tsaya ma da cin abincin nashi, "Dan Allah kar kace zaka boye man, kaji?"

A hankali Rayyan ya dago yana kallonta, shi yasan Lubnah ko tsufa tayi tabbas tana cikin jeran matan nan da suke mutuwa da kyawunsu. Shidai kawai bata mashi ba, Allah bai saka mashi santa ba. Baya ga kyaun da Allah ya mata sai kuma ya bata kyakyawar zuciya da halaye wanda zasuyi wuyar samu a zamanin nan, amma dukda haka baiji yana santa ba. Meyasa zuciyarshi zata mashi haka? Mai yasa zai fada soyayyar wacce bama ta san yanayi ba? Haram ne ma a yanzu yace yana san Ramlah tunda ko babu Yasir, an riga da an saka ranar aurenta da Aliyu.

Idan yace zai cigaba da dawainiya da soyayyar Ramlah tabbas ya cuci kanshi kuma zai cuci matar da zai aura, amma ta ina zai fara? Kullum cikin fada yake ma zuciyarshi akan ta daina wannan wahalalliyar soyayyar amma taki ta daina, karuwa ma san Ramlah yake kullum a ranshi. Da kyar ya samu ya kalato murmushin daya sakarwa Lubnah, "Nagaji ne, Lubnah. Hidindimu sunman yawa, ga shirin biki duk banda natsuwa." Baisan ta inda zai fara ba. Bama wannan ba, bazai taba gaya mata wai Ramlah yake mutuwar so ba koda kuwa ace zai mutu, ya gwammace ya mutu da abunshi a rai, dan koba komai Lubnah bata cancanci haka daga wajenshi ba.

"To stress ne duk zaisa ka zama haka, Rayyan? Kaga yanda ka koma kuwa? Ka rame, idanunka duk sun fada, har baki fa kayi. Ba wani stress Allah, indai da wani abun dan Allah ka fada man."

Yar dariya yayi kafin yasha drink din data kawo mashi, "Ciwon so yake damu na, na kosa a daura auren kowa ya huta." Cak! Zuciyarta ta tsaya, ya lura duk sanda ya mata magana makamanciya data soyayya rasa inda zata saka kanta tayi. Shi idan ba yanzu dayace hakan ba ya manta yaushe rabon da suyi magana irin ta masoya ko wanda suke da shirin yin aure nan da yan satika ba.

Yar dariya tayi da alamar jin kunya kafin ta daga mashi kai, "Naji, banda wannan kuma fah?"

Juyowa yayi yana kallonta, "Inaso na bar kasar nan, ina zamuje honeymoon? Zan duba ma naga idan zan samu aiki wata kasar, akwai mutanen da bansan gani yanzu." Dariya ta fashe da ita. "Ji dan Allah kamar wanda akewa wani mugun abu a nan din? Honeymoon kuma muje maldives, inaso naje amma ban taba zuwa ba. Naga ma suna tallar wani couple package, zan duba mana, ai passport dinka yana nan ko?"

Tsayawa yayi yana kallonta, ita batasan wai koda yaje honeymoon dinba so yake ya gudu daga garin nan dan kar yaga Ramlah da koma waye zata aura? Baiso ya kuntata ma Lubnah ko ya sanyata cikin kunci, hakan yasa yake zullumin auren nan. "Yana nan, idan kin tambayesu da visa da komai sai ki fada man. Nasan halinki yanzu kina iya ceman har ticket kin siya kinyi booking komai."

Yar dariya tayi, "Ai sai mun samu time din da zamu dauki hutu sosai kaman wata daya tukunna." Murmushi tayi idanunta na budewa, kyanta yana kara bayyana, "Ko muje tare dasu Ramlah? Akwai abubuwan da nakeso na nuna mata a can." Ai kuma, ita batasan abunda yake gudu kenan din ba? Ramlar dai da take kauna shi kuma itace silar kaucewar duk wani farin cikinshi.

Amma baisan ta ina zai fara ce mata kar su tafi tare dasu Ramlah ba, hakan yasa ya chanja akalar maganar gaba daya. "Kwana biyu ma I've been so busy bamuyi maganar Ramlah. Ya suka kare da wancan mutumin? Ya yarda zai saketa din ko kuwa? Ni abun nasu da rudani fah."

Ajiyar zuciya Lubnah ta sauke tuno halin da Ramlah take ciki, "Ko yanzu dakyar na samu na lallasheta. Bakaga uban messages din da yake turo mata ba, azabar Allahn dake kanta yen yen yen. Tsofaffin hotunansu dana Hanan wanda bata dasu tunda kaga da ba waya ma gareta ba. Ta rikice ta rasa ina zata saka kanta. Ga hakuri idan ya fara jero mata message din hakuri sai yai mata yafi talatin, cikin kwana biyun nan gaba daya ta hargitse. Tana san Dr Aliyu amma kuma Yasir yana amfani da Hanan wajen karkato hankalinta." Shidai kallonta kawai yake, baisan cikin maganganun nata biyu ba wanne yafi sakashi cikin damuwa. Fadin da tayi tana san Dr Aliyu ko kuwa Yasir din da hankalinta ya fara karkata akai?

"Tun jiya nace mata akwai wani friend dina lawyer ne zan kirashi ya kai mana kara shari'ah court amma tace kar nayi tukunna, wai sai tayi tunani. Yanzu dai tana da aurenshi a kanta bata san ma me zatayi ba. Har kiranta fa yakeyi, tun bata dauka har ta fara dauka, ni abunma ya fara bani tsoro. Tama daina kula Dr Aliyun yanzu, idan nace meyasa sai tace idan ta kulasu su biyu lokaci daya kwakwalwarta juyewa zatayi saboda rudani. Wai ma zunubi ne yanzu yin magana da wani bayan tana da aure."

Hmmm, abunda Rayyan ya iya furtawa kenan. "Ko abinci bata iya ci fah, magana ce ta Hajia sai ta Hanan, har shi kanshi Yasir dinma sai zakulo labaran lokacin da suke cikin jin dadi take tana bani."

Ajiyar zuciya Rayyan ya sauke, "Mutumin nan ba san Ramlah yake ba, Lubnah. Akwai wata aniyar a ranshi amma bawai dan yana kaunarta ba."

Da damuwa a fuskarta ta daga mashi kai, "Babu yanda banyi na nunawa Ramlah haka ba, Rayyan. Kuka ma ta saka danace mata ta daina bari yana wasa da kwakwalwarta dan kawai yaga ta soshi a baya kuma yana amfani da Hanan wajen yanjo hankalinta. Wai ita duk ta rude, yanzu dai har mafarkin Hanan take kuma duk akan shi Yasir din."

Mamaki ma daya cika mashi zuciya kallon Lubnah kawai ya tsaya yanayi, "To yanzu miye abunyi? Dan in banda wahala da kunci babu abunda zata tsinta wajen mutumin nan. Kuma in har ta koma mashi ta tabbata bata da zuciya abunda kuma zai mata nan gaba sai ma yafi wanda ya mata a da."

"Ya kau zamuyi da ita? In tace shi takeso koda an riga an daura mata aure dole fa a raba auren ta koma mashi balle ma ba'a daura ba. Nidai nayi iyakar yanda zan iyayi na ma Ramlah bayani ta dawo cikin hankalinta amma na kasa. Sai dai kai ko zaka gwada, dan naga wani lokacin ma tafi saurararka." Da yayi niyyar har ayi bikinsu bazai kara bari su hadu da ita ba, amma yanzu yaji bazai iya zama haka kawai yanaji yana gani ba taje ta komawa wancan mutumin.

"Zata iya fitowa yanzu?" Abunda ya furta kenan yanajin yanda zuciyarshi ke mashi wani irin nauyi.

"Anya? Kuka fa ta gama shabe shabe, ni abun ma har haushi ta bani dazu yanda kasan na kamata naita bugu. Saidai ka kirata a waya, amma ka nuna mata bakasan komai ba, ita da kanta zata fada maka komai." Kara tattaunawa sukayi a kan maganar kafin Lubnah ta mishi saida safe ta tafi.

Wanka ya shiga yayi, duk abunda yakeyi cikin dakinshi tunanin Ramlah yana nan ya hanashi sukuni. Tunani yake yanzu idan tace ita dole Yasir din takeso dole fa hakan za'ayi ko? Yanzu shi da ace ta komawa wannan Yasir gara ta auri Dr Aliyu zaifi mashi sauki, dan komin banza yasan Dr Aliyu zai kula da ita amma wancan dan iskan saidai ma ya ida rikita mata rayuwa.

A hankali ya zaro wayarshi ya kirata, saida wayar ta kusa tsinkewa tukunna ta dauka, murya can kasa alamar tasha kuka ta koshi. "Sannu," abunda ta furta kenan da kyar, baisan yanda akayi ba saidai ya tsinci kanshi da wani irin murmushi, jin muryarta kadai ya rage mashi radadin da yake kwana yana tashi dashi. Rayyan ya dade da tabbatar ma kanshi cewar koda soyayya kadai Allah ya barka ta isheka azaba.

"Sannu kawai, Ramlah? Yau ko yar ina yinin ma bazan samu ba halan?" Idan ba da zolaya ya fara ba wayar bazata mashi yanda yakeso ba, dole sai ta fara sakin jikinta tukunna zai samu wani maganganun ta yarda tayisu dashi.

Turbune baki tayi, "Ina yini? Mantawa nayi bance ba,"

"Lafiya lau yan mata. Ya gidan? Kwana biyu ban ganki ba, kina lafiya ko?"

"Eh, lafiyata lau. Kai fah? Kana cin abinci? Ya aiki?" Dukda cewar wannan tambaya ce wadda zata iya yima kowa ita amma hakan bai hanata faranta mashi rai ba.

"Baki kara nemana ba ai, ya kuke ciki da mijinki?" Saida tayi shiru na wasu yan mintuna tukunna tace, "Yana nan, bansan ya zanyi ba, Rayyan." Kamar wasa hawaye suka fara taruwa a idonta, "Kaga ko? Ji nake har yanzu ina sanshi, ga Hanan, ga Dr Aliyu da Hafsah, na rasa yanda zanyi. Nasan da munje kotu idan nace bana sanshi ko dan abunda yamun dole a raba auren amma tausayi yake bani." Reversed psychology yayi using a kanta. Ita daya kamata aji ma tausayi yanzu ita take ma tausayinshi.

Dukda yanda zuciyarshi take mashi ciwo haka ya daure ya fara magan cikin natsuwa. Duk ta inda ta bullo mashi yana da amsar da zai bata. Tun tana kuka har tayi shiru tana saurarenshi kuma da alama maganganunshi suna tasiri a zuciyarta wanda yasan daga Lubnah har Aliyu babu wanda zai iya mata magana ta fahimta haka inba shi ba. Akwai wani abu dake tsakaninsu wanda ita bata gane shi ba amma shi zuwa yanzu ya gama tabbatar ma kanshi soyayya ce, saidai soyayyar shi kadai yake yinta ita akwai wadanda takeso.

Yana cikin magana tayi hanzarin katseshi. "Kaga yanzu ma shi yake kirana. Sai na fara jin haushin shi daya fara magana sai naji duk ya bani tausayi."

"Karki dauka. Tun yanzu zaki fara kokarin yakice shi tunda keda kanki kinsan so kawai yake yayi amfani dake, Ramlah."

"Toh idan maganar Hanan zai mun fah? Idan wani abun nata ya gani ko ya tuna yanaso ya fada man fah?" Ya lura da Hanan yake amfani yana abunda yaga dama da zuciyar Ramlah, tunda duk wanda ya santa yasan Hanan ce weak point dinta.

"Duk maganar da zaiyi cikinsu akwai wacce zata maido da Hanan duniya?" Kamar yana gabanta haka ta amsa da 'Aa,'. "Kin tuna yanda kike kuka a Maiduguri kina fada mashi cewar Hanan dinku ta rasu?" jira yayi saida ta amsa da eh tukunna ya cigaba, "To a lokacin ya nuna ya santa ko kuwa ya nuna wani na cewa diyarshi ta mutu?" Aa ta kara cewa, "To kin gani, wannan kawai ya isa yasa ki gane amfani kawai yake da sunanta dan cimma burinshi Ramlah.

Shiru tayi kamar mai nazarin wani abu, "Ki zaba yanzu, zaki katse wayar mune ki dauki tashi ko kuwa zaki bari ya gaji da kira har ya hakura?" Shirun dayaji ne yasan yasan ta gama yanke nata hukuncin, haka kuma duk maganganun daya dade yanayi suka zama na banza a zuciyarta.

Indai baki cikin whatsapp group dinmu an barki a baya🥳💃🏼💃🏼

Continue Reading

You'll Also Like

723K 55.9K 81
It is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny...
110K 12.4K 40
The story of A'isha and Suleiman, the fated lovers who were born be each others company! Hausawa sunce mahakurci mawadaci ne tabbas Maganar take duk...
349K 8.7K 80
"ပူတင်းလေးကဘာလဲ" "ကိုကို့အပိုင်" "ကိုကိုတို့ကရောဘာလဲ " "မောင်နှမ" "ဟာ..."
2.8M 143K 58
Start Date>>>> 1.4.2020 End>>>20.5.2020 ကိုယ့်ဘက်က အချစ်တွေပေးခဲ့လည်း ပြန်ရခဲ့တာက နာကျင်မှုတွေတဲ့လား မင်းအမုန်း​တွေကိုထပ်ပြီးမခံစားနိုင်တော့လို့ ငါထ...