RAYUWAR JIDDAH ✔

By DielaIbrahim

10.3K 856 277

RAYUWAR JIDDAH Labari ne akan rayuwar wata ya' mace mai suna Hauwa'u Jiddah. Let embark on the journey togeth... More

01
02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
AL'ADARMU
UMMI KWARAS
AL'ADARMU
AL'ADARMU

26

218 19 5
By DielaIbrahim

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/6

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________
Hospital
10am

"The next day""
Misalin karfe goma kowa yazo hospital har da Leemarh Amma ta bar su Daddy agida...Hafiz kuwa yana nan babu inda yaje abinshi, a cewar shi Hauwa'u tana bukatar sa a kusa da ita don haka babu inda yaje sai dai da aka matsa masa da magana sai yayi wanka a bandakin dake cikin ward din, sannan Leemarh da zata zo sai ta  taho masa da kaya, hmm Oga kenan 😎 anan yasanya kayan sannan sukaci abincin da Ummi ta dafawa Jiddah, tare ma suka ci a plate daya ko kunyan mutanen wajan basayi."

Suna zazzaune abinsu suna hira aka kira wayar fatima, aka sanar  matà cewa first semester results dinsu ya fito, habawa tuni suka rude ita da Jiddah, da sauri Jiddah ta kunna data na wayar ta, whatsApp messages suka fara shigowa, ta shiga class group dinsu mai suna "BCH CLASS OF 15" Fatima tazo ta zuna suna dubawa tare har suka zo kan matric number dinsu, kasancewar accordingly ne Jiddah 1134, Fatima 1135, babu abinda suke fadi sai Alhamdulillah bakin su ya kasa rufuwa, suna ta fadin munyi passing" Faisal yace mugani, Jiddah ta mika masa wayar tana kallon Hafiz dayake murna shima yace "Congrats dear" tace thank you"
Ana ta taya su murna, suna farin ciki Fatima tace Jiddah sauran mu second semester and it's the final semester Allah ya bamu sa'a" Jiddah tace Amiin ya rabbi"

**************

Da misalin karfe goma sha biyu na rana 12pm dakin ya cika da mutane ana ta faman hira kuwa sai Muhammad yace Ammi abamu labarin please ana ta ja mana rai😣
Ammi tace wa badai ni ba, ta dubi Ummi tace gareki Ummi, 'ya'yan ki nason jin labarin ki"
"Ummi tai murmushi tace yaran kadai zan bamawa saboda haka manyan should excuse us, Momma tace dama ni kam gida nayi, Ammi tai saurin cewa jira ni mu tafi tare Momma, haka su ka fita harda Abba, Abba yace da Ummi zai fita wajan abokinsa, tace to Allah ya tsare"  Ummi ta lura kaman Abba ya sauko daga kan kujeran mulkin daya hau kwana biyunnan, ko dayake dama ba halinsa bane ara yayi ya yafa😂" Tana ta wannan tunanin, sai taji Saifullah na cewa Ummi we are all ready"
"Ya dawo ta ita daga cikin trance din data shiga, ta waiga sai taga daga ita sai yaran, Ummi ta tashi ta nufi gadon Jiddah, ta zauna very comfortable  sa'annan ta jingina da bango sannan ta kwantar da Jiddah a laps dinta tana shafa mata wuya" Ummi ta kalli Jiddah wacce hannayen ta na cikin hannun Hafiz ya rikesu dakyau kamar ance za'a kwaceta a gudu da ita" ahankali Ummi tai murmushi sannan ta soma.

******************************
TUNA BAYA

Shekaru Arba'in da suka wuce tunda ayanzu shekaran Hafiz 31 Jiddah kuma tana 21...............

"Sunana Halimatu wacce kuka fi sani da Ummi" tun Ina shekara goma Momma ta dauko ni daga katsina wajan Ammi, na dawo zama awajanta tun Uncle(Abban Faisal) baida kudi, har Allah ya bashi rufin asiri sosai, da farko dai unguwan dosa suka fara zama daga baya lokacin an haifi su Isma'il da Idris dasu Maimuna sai ya koma Unguwan rimi, ya gina gida na gani na fada, Uncle shike daukan duk wani responsibilities dina, ayayin daya hana Momma kashe ko sisin ta akaina, Lallai Uncle mutumin kirki, mutumin arziki har na gama secondary school bai dena dawainiya dani ba, sannan ya biya mana Hajji mukaje gaba dayanmu, dawowar mu kuwa bada jimawa ba (27th December,1980 na samu admission a Kaduna Polytechnic (Kadpoly) , dukda kuwa rayuwa bata tsada lokacin, shi kanshi jami'ar ma ba kowa ke zuwa ba saboda karancin wayewa, dukdama ilimi ya dade da shigowa amma neman ilimin baiyi yawa kaman zamanin yanzu ba, shiyasa muka kasance mu goma(10) a class dinmu, inda suka bani Business Administration.....Allah sarki Uncle, Allah ya jaddada rahama agaresa, shine yai tamin registration da komai ma, har na fara zuwa lectures,, kullin cikin maida hankali nakeyi a makaranta, Ina dawowa kuwa zan samu Uncle ya taya ni yin assignment sannan ya kara yimin  bayanin darasin da aka koya mana.
Ana haka muka fara test, Ranar da muka fara test itace ranar da har yau bazan taba mantawa da ita ba a rayuwata........Ummi ta dan tsagaita ta dubi yaran duka Wanda sukai shuru suna sauraranta tace lokacin sallah yayi, yakamata ku tafi masallaci" after zuhr prayer sai mu cigaba Koh!

" Toh Ummi suka amsa gaba dayan su, suna masu niya da haramar tafiya masallaci ayayinda fuskokinsu ya nuna alamar son Jin karashe labarin" Mata anan cikin ward din sukayi tasu sallar.

Karfe daya da kwata 1:15pm suka dawo sa'annan Ummi ta gyara zaman ta wannan lokacin tana zaune saman sallaya ne ta jingina da bango Leemarh da Fatima suna gefenta sai Jiddah kuma tana kwance gabanta tayi matashi da kafar Ummi, mazan suma dai kasa suka zazzauna wannan karan sannan Ummi ta soma.
*************
1981/03/01
1st March,1981
Wannan itace ranar dana fara haduwa da Abubakar Yusuf, kuma ranar dana rasa Abbana, and also my Birthday., abin ya faru ne kamar haka...

7 - 8am muka fito test, Yan class dinmu kuwa suna ta tsokanata wai suna min wishing kasancewar mu goma ne bamuda wani yawa,, nikam sauri sauri nakeyi na isa gida saboda Momma tace zata hadamun birthday cake.

Ina hanyar tafiya gida nida wasu daga cikin yan ajinmu mu uku kasancewar duk hanyar mu Daya, muna takawa don alokacin sai mu taka muje har cikin unguwan rimi  da kafafun mu, dukdama akwai mai mashin din dayake kaini kullin ya dawo dani, amma wani zubin sanaji dana tsaya jiranshi gwara na bi yan hanyar mu, mu taka muje gida, toh  ranar bayan mun iso junction din da kowa zai rabu, nai ma sauran sallama, sannan na kama hanya ni kadai, Ina tafiya ta cikin natsuwa, bayan nazo wajan wata bishiyar mangwaro sai ko mangwaro ya fado bisa kaina, na ko sa ihu Ina mai dafe kaina alamar zafi, sai na kalli mangwaron, lokaci daya na saki murmushi ganin mango din ya nuna sosai kuma babba ne  gashi yayi red red, yellow yellow haka and kuma bai fashe ba, nako Sanya hannu na dauka Ina kakkabewa da hijab dina, Ina gama kakkabewa nakai baki zan gyatsa sai naji ana cewa Yaya Abubakar, Yaya Abubakar zoka ga yarinyar nan, abun mu ya fado kuma ta dauke mana"

Na waiga banga Abubakar din da aka kira ba, sai na maida hankali na ga mai maganar wanda akallah zai bani shekara biyu, na tura baki gaba, nace kayi hakuri wannan mangwaron akaina ya fado kuma wallahi banga mai hanani shanshi ba, beside today is my birthday kuma mango yana daya daga cikin favorite dina, don haka dole sai na sha" na kai baki kenan sai naji an rike min hannu ana saukar min dashi ahankali.

Da sauri na waiga don ganin mai sauke min hannun, alokacin idanuwana suka sauka a idanun Abubakar wanda tuni shima ya kafe ni da ido....alokacin shekarun sa ashirin da bakwai 27 a duniya nikuma Ina goma sha bakwai 17 shekara goma ya bani.

Saida ya saukar min da hannu sai yace, kin wanke ne kike neman sanyawa a baki?

Zazzakar muryar sa ta doki kunnuwa na, ahankali na soma  girgiza kai, alamar aa"
" Sai ya harare ni playfully" sannan sai naga ya waiga yace Yusuf je dauko goran ruwan da Mummy ta bamu, na wanke mata" ba musu ya tafi ya dauko ya mikawa Abubakar din, ya amsa yana wanke min cikin natsuwa, ni kuma ina ta kallon su, sanye suke da rigan jersey sai black jeans da canvas gefen su kuma Ball ne sai bag dinsu da kuma wani basket wanda anan naga suna tara mangwaron.

Ina nan tsaye ya miko min, yace ungo sha, da sauri na amsa nakai baki abuna  ina sha Ina lumshe ido tsabar dadi sannan Ina kallen su ta gefen ido, sannan na nufi wajan basket din danaga mangwaro dayawa na sa hannu kuwa na dau guda uku masu kyau, sai na dawo inda suke tsaye nace musu na dauki wannan zan kaiwa Momma ne, da Abba.

Babban ne ya gyada kai (Abubakar din) karamin kuwa sai ya harare ni, Ni kuwa sai na mishi gwaliyo na tafi cen wani gefe na samu dan dutsi na zauna, na sha mangwaro da kyau sauran na sanya su a jaka, Ina kallon yadda suketa baro mangwaron gwanin ban sha'awa, nima naji watarana Ina so nazo na barowa Abbana daya ke katsina saboda yana son mangwaro shima, na tashi Ina shirin barin wajan.
Sai Abubakar din yace ki kula da hanya fah"Na dan waigo da mamaki kuwa Ina kallonshi, sai yayi min murmushi, Nima kuma na mayar masa sannan na tafi.

Ina zuwa gida kuwa da murna ta, nake nunawa Momma mangwaro amma sai naga kaman tana hawaye, kuma da alama kaya take hadawa, banma lura da Uncle ba ashe shima yana dakin shike ta faman hada kayan""Na zauna kusa da ita nace, Momma, Aunty Maryam meya sameki kike hawaye?
Da alama Momma bata lura da shigowata ba, shiyasa ko data ji nayi magana, ta firgita sosai tafara share sharen hawaye, tana cewa hawaye kuma aa Halimatu, wani abune ya fadan min cikin ido, dubamin kigani ko ya fita"

"Niko naita dubawa banga komai ba, Uncle na gefe yana hada kaya , Yana kuma jinmu Amma baice komai ba, har ya gama, sannan yace Halimatu Katsina zamu tafi yanzunnan, na hada kayanmu duka harda nasu Isma'il.
"Uncle me za'ayi a katsina kuma?bamuyi hutu bafah!
"Babu komai kedai tashi kiyi wanka ki shirya, ki shirya su Isma'il sai mu tafi"
" Nace toh"

Naje na  shirya su tsab, na shirya nima sannan muka tafi, ahanya na baiwa su Isma'il mangwaro Daya nace yasha shida Idris, sauran kuma na boye, burina idan naje katsina na baiwa Abbana"
Karfe hudu 4pm muka Isa katsina "kerau itace unguwan dasu Ammi suka fara zama kafin daga baya suka koma Barhim Estate" gidan mu, nayi mamaki kwarai danaga mutane dayawa abakin gate, sun zazzauna saman tabarma,, mai makon uncle yayi parking acikin gida sai naga yayi parking awaje, na ko sauka irin ko ajikina, nayi cikin gida Ina kwalawa Abbana da Ammi kira, karo na fara ci da mutane wanda suke ta faman kallo na, banyi tunanin rasuwa akai ba dukda kuwa naga wasu yan uwanmu suna ta kuka, na cigaba da tafiya sashen Ammi bayan na shiga sashin Abba bangansa ba, kai tsaye dakin baccinta na nufa bayan na tsallake mutane a falo ko gaishe su banayi kaman wata karamar yarinya dukdama alokacin ba kuruciya ke damuna ba Autanci ne irin na JIDDAH", Ina shiga kuwa na sameta zaune saman carpet tsakiyar yan uwanta tana ta faman hawaye, na ruga izuwa gareta na dane cinyarta nace Ammi na me ya sameki kike hawaye?
Inayi Ina goge mata hawayen"

Ganina yasa kukan nata ya soma tsananta to which wata goggo na (goggo saude (kanwar Abbana) ita ta janye ni a dakin takaini part din Mama inda nanma sauran Yan uwa na, na gani suna ta faman kuka, ciki harda aunty Maryam(Momma), sai alokacin na soma tunanin ko rasuwa akayi ne sai alokacin Autancin ya fara sake ni, na dawo cikin hankali na?
To inma rasuwa akayi waye ya rasu haka, da ake ta kuka?
Daga karshe danaga bani da amsoshin tambayan sai na nufi wajan aunty maryam, na zauna Ina ta bata hakuri, ta rungume ni tana hawaye, daga karshe nima na soma kukan saboda Ina da raunin zuciya ganin takiyin shuru kuma bansan meyasa suke kukan baa" kuka nakeyi sosai Wanda ya ja attention din mutane ya dawo kaina, har Mama ke cemin Halima kukan me kike? yi shuru ya Isa hakanan"
Sai nace Mama Aunty Maryam takiyin shuru sauran ma duk sunki yin shuru ne kuma ni har yanzu bansan kukan me sukeyi ba"
Mama ta girgiza kai ganin kaman yarinta na damu na, asalima kowa ya hana a fadi min ne saboda sun san cewa zanyi bori sosai. Hmmmm abin dariya maimakon na zauna agida abuna, sai ma na fita makota gidan wata kawata sa'adarh, na iske sa'adarh na ta kuka ita ma gani na yasa ta share hawayenta takama kirkiro ayyukan dole, tana yi, ni ko na nemi gu na zauna ina bata labarin kaduna da school din Dana fara zuwa....ba laifi tana taya ni hiran amma sama sama, daga karshe nayi bacci to which ban farka ba sai magrib Ina tashi kuwa na nufi gidan mu ko sallama banyi wa kowa ba, saboda wani mummunan mafarki danayi akan Abbana, kai tsaye part dinshi na nufa anan nayi alwala a bayin shi nayi sallah a prayer mat dinshi kuwa nai masa addu'a sosai sannan na hau kan sofa din dayake kwanciya as usual idan ya dawo daga aiki" , na kwanta Ina wasa da mangwaron dana kawo masa, Mama ce ta shigo ta kawo min abinci tace Autar Ammi ashe kin dawo, budan baki na sai nace Mama nikam har yanxu baba bai dawo ba, nifa na gaji da jiransa zan bishi kasuwan tunda kunce kasuwa yaje, Kuma dai naga kasuwannan idan dare yayi ma kulle ta akeyi, to me yasa har yanzu bai dawo ba ?
" Mama ta basar tace yanzu tashi kici abinci tun da kukazo bakici komai ba"
"Na kuma budan baki akaro na biyu nace Mama tare da Abbana nake cin abinci duk zuwan da zamuyi and you knew it , nikam zan jira sai ya dawo.....haka Mama tagama lallabi amma naki ci, daganan aka fara zuwa ana lallabani naci abinci Amma na kulle kunnuwana, naki sauraransu....har Ammi tazo da kanta"
Ammi kam bazan iya mata musu ba, bansan lokacin dana fara ci ba  saboda ta taho da wata katuwar shaula wato bulaliya,you habawa tuni na soma ci don nasan ita ba lallami na zatai ba, Ina cin abincin Ina mita Ina  cewa wlhy idan Abbana ya dawo sai na fada mashi sun tursasani cin abinci batareda shi ba😢 haka dai har naci rabi.
Ranar a part dinshi na kwana nida Ammi, wasa wasa har tsahon kwana ki uku babu Abba babu labarinsa, nayi mitar dawowarsa har bakina yayi ciwo, daga baya na koma yi musu kuka safe, rana da dare bana bacci, na daga musu hankali na tsahon kwanaki shiddah (6) kafin aka sanar dani "Abbana ya rasu" Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un" da fari cewa nayi karya sukeyi, Amma daga baya danayi tunanin lokacin da muka zo naga gidan a cike harda yan uwan Abba suna ta kuka, da abokanan sa, hakan yasa na gasgata maganar su, Hakika mutuwar ta taba ni sosai, maimakon na yi bori kamar yadda sukayi tsammani, sai sukaga na zauna waje daya cikin natsuwa tare da fadin Abbana Allah ya gafarta maka" Abbana Allah yasa mutuwa hutuce agareka" Abbana Allah yai maka rahama" Abbana Allah yàsa ka shiga Aljannah haka nai ta faman zayyano Addu'o'i Ina masa, har na tashi na shiga daki (part din Abba) ko dana shiga key nayi wa kofar na shige kuryar daki anan na dukunkule a lungun gadon sa wajan bedside na sanya kaina cikin gwiwa ta  sai alokacin hawaye suka soma zubowa, sai alokacin nayi kuka, hakannan Ina jin ana bubbuga kofar Amma naki budewa, Ina Jin Ammi na ce musu su kyale ni kuka nakeyi, su kyale ni zan fito da kaina.

Haka kuwa akayi,bani na bude kofar ba sai washe gari da yamma likis, kallo daya zakai min ka hango ramar danayi na kwana daya kacal idanuwa na kuwa sun kumbura saboda kuka gashi ko bacci banyi ba.

Wajan Ammi na nufa na kwanta acinyarta nace Ammi yunwa nakeji, haka Ammi ta tashi dakanta ta zubo min abinci, ita ta rinka bani abaki Ina ci ko da muka hada ido da ita sai naji sabon kuka ya kubce min, taita tapping baya na trying her best to comfort me tana bani hakuri
Ya Isa Autana, ya Isa Halimatuna, Abba addu'a yake so ba kuka ba"
Hakika tundaga lokacin na soma yimasa addu'a kullu yaumin, har muka koma Kaduna saboda school dina dana yara kuma,
Ranar Monday na tafi school yan class dinmu sukaita min gaisuwa kasancewar sunji labari daga wajan kawata. Ranar mun gama lectures na kama hanyar gida, ko danazo daidai bishiyar mangwaron nan, sai naga yau babu kowa awajan Amma na hango sandar danaga suna baro mango dashi, hakan yasa na nufi wajan na dauko sandar na soma kokarin baro mangwaron, amma na kasa, ga wahala danasha har nayi kusan awa biyu ina abu daya, da kyar na ajiye sandar na koma gefe ina haki Ina share zufa, daga kan dazanyi sai na ganshi tsaye cikin shiga irin ta rannan Amma yau white jeans ne da jersey mai layi layi red and white, sai canvas red yai masifar yin kyau to which na shagala da kallon sa,

Har ya zo inda nake yace, baiwar Allah me kikeyi anan ke kadai, shin baki ko tsoron wasu su kamaki, ko wani abu ya sameki?
" Nace ni ni magwaro nake son baro wa"

" Sai ya fashe da dariya yace sai akace miki haka ake baro mangwaron, wahala zakisha fah, kalli fa bishiyar tsayi gareta ga ta da manyan reshe, taya yaya ma zaki iya baro mangwaron ke kadai"
" Kawai sai nayi rau rau da fuska ganin har lokacin dariya yakeyi" sai nace mashi to ni ya zanyi, ai ba iyawa nayi ba, na barshi awajan na nufi hanyar gida abina, da gudu ya biyo ni ya kama hannu na, yace taho kigani in koya miki"

Haka muka juya Ina kallonsa ya hau bishiyar mangwaron, ya kado kusan guda bakwai masu kyau sannan ya sauko, ya kwaso ya sanya su aleda sannan ya mika min, yace bawai na nuna miki bane ko saboda wata rana kema ki hau" aa kada ki sake hawa kina jina, duk randa kike son mangwaro ki jirani anan da karfe hudu zanzo sai na baro miki kinji"

" Nayi murmushi nace mishi to na gode "Yaya"Ina ta washe baki"

" Yace waya ce miki suna na yaya ?
" Sai nace to ai kai babba ne ka girmeni, kuma kana baro min mangwaro"

" Yayi murmushi yace toh naji Amma ni sunana "Abubakar Yusuf" kinji.
" Na gyada kai"sannan nace mishi ni zan tafi gida sai anjima"
"Sai naji yace toh ai baki fada min sunan kiba"Murmushi nayi nace masa sunana "Haleematu"
"Yace MashaAllah gaskiya sunan akwai dadi" zaki bani aron sunan na sanyawa yarinyata ? " Nikam sai nace ehh mezai hana, nabaka halak malak" na fada Ina murmushi" Ranar dai ba da wuri na koma gida ba saboda hira da mukai tayi da Abubakar.

"Tundaga ranar kullin sai nazo na jira shi ya baro min mangwaro, to which a lokacin sai na fara sabawa da Abubakar na sake dashi, kuma shima ya sake dani sosai ya dauke ni tamkar kanwa awajan sa, so da dama zan zo na sameshi awajan yana zaune yana jirana, muyi hira, muyi assignment dina, ya koya min karatu kuma sosai nake fahimta, zamuyi ta hira har karfe biyar kafin sai na wuce gida......har takaiga Abubakar ya fara rakoni har gida , sai alokacin nasan shima Kadpoly yayi Electrical Engineering" shekara hudu ya hada ND, da  HND har yayi NYSC, yana koyarwa ne  a private school presently ""kuma duk sanda zan ganshi da kayan jersey ya dawo daga buga ball ne, wanda ball shine favorite hobby dinshi".....Kwata kwata watan mu daya alokacin amma gaba daya little memories dinda mukayi making tareda shi yakasa daina yawo a kwakwalwata, shakuwace mai tsanani ta shiga tsakanin mu wanda bamu san da haka ba, mukawai muna ta tsunduma kanmu acikinta hankali kwance.
kuma alokacin mukayi hutu, Momma ta shirya min kayana wai zani Katsina hutu," kasancewar duk hutun dazanyi a katsina nakeyin shi" hakan yasa ta hada min kayan, Amma to her own surprised sai taji nace mata bazani ba"
"Tayi mamaki kwarai, tayaya lokaci daya zance bazani wajan Ammi ba afterall duk holiday sai nayi kuka nace zanje naga Abbana, zanje naga Ammi na har tsokana ta sukeyi suyi ta cewa bazani ba" Amma yau nice nake cewa bazani ba"
Bata cikani da tambaya ba tunaninta saboda Abbanmu ya rasu ne, nace bazani ba, batasan akwai wata akasa ba" don kuwa
bana so nayi missing din Abubakar....ko da mukayi hutu nayi kusan kwana biyar banganshi ba , kuma dai ni ba'a barin naje ko Ina sai school Kuma munyi hutu, sai na kirkiro sabuwar karya nace ance muringa zuwa tutorial duk Saturday" kuma suka amince batareda wani bincike ba kasancewar basu matsamin saboda sanin Ina da natsuwa fiye da tunanin mai karatu.

" To cut the story short" haka na soma haduwa da Abubakar every blessed saturday kuma awajan bishiyar mangwaron nan, idan na fita tun safe haka zan iske shi awajan sometimes shi da Yusuf, zamuyi ta hira har yamma sannan su rakoni hanyar gida🙃

" Tun bamusan soyayyah mukeyi ba har muka zo muka gane tsananin son juna mukeyi sboda watarana bayan shekara daya da haduwar mu, wani hutu da akayi a school sai Momma tace sai na tafi Katsina ko Ina so ko bana so, haka na shirya na tafi kuwa sati na biyu banga Abubakar ba sai zazzabi, ashe shima yana cen yana ta fama da ciwon missing dina gashi babu waya wasika ne ake aikawa kuma shi baisan wa zai bawa wasikar ba haka ya hakura ya cigaba da dakon ciwon shi har nayi wata daya hutu ya kare na dawo"  Ina shiga gida ko hutawa banyi ba na saci hanya na fita Kai tsaye joint dinmu na nufa, na zauna tsahon awa uku babu Abubakar babu alamarsa, har magrib tayi sannan na koma gida, ranar dai nasha fada, nasha tamabayoyi, Ina kikaje?
Amma ko daya ban tankasu ba, na wuce daki nayi kwanciyata"
Washegari haka na fita da sassafe still joint dinmu naje, na zauna awajan har yamma, babu Abubakar.... alalace alalace sai da nayi one week for good Ina zuwa wajan banga Abubakar ba, kuma ban saduda ba, har dai watarana na hadu da Yusuf sai alokacin Yusuf ke sanar dani Abubakar yana gida ba lafiya" ba terada wani tunani ba nabi Yusuf mukaje gidansu Gwamna road that was my first time dana taba zuwa unguwan, ya kaini palour yace injira shi dukda adar dar na shiga gidan, amma daga baya hankali ya kwanta ganin kannensa da mahaifiyarsa danayi sai na saki jikina, Ina nan zaune kuwa suka fito tare da Abubakar din, duk ya rame yayi duhu" na tausaya masa matuka bayan naji daga bakinsa cewa likita yace ciwon zuciya ne ya kama shi, kuma missing dina ne da rashin gani na" Hakika ciwon zuciyar Daddy daga lokacin ya fara wanda yake fama dashi har yanzu kuma nice sanadi" na tausaya masa matuka na soma kula dashi dukda kuwa yana da sisters ga Mummy(granny) Amma sai jininmu ya hadu dasu gaba dayansu, haka zanzo tunda safe nai ta dawainiya da Abubakar, nice dafa masa abincin dazai ci, nice yi masa wanki, nice gyara masa daki na wanke bayi na goge masa kaya" Mummy da Yan uwan shi sun hanani Amma naki ji" har suka hakura suka barni" Ashe abinda bansani ba su Momma da Uncle sun gano inda nake zuwa ta hanyar mai mashin dina da akace ya rinka bina abaya har asan inda nake zuwa" wanda har tambayan mai gadi yayi wai me nake zuwa yi agidan"

lol sorry 😜❤️

Comment
Vote
Share

Continue Reading

You'll Also Like

12.3K 606 53
MAKAUNIYAR RAYUWA- KASHI NA UKU- BABI ASHIRIN### Fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke,alherin Allah ya kai gareku, ubangijin Allah ya biyaw...
2.3K 231 15
Saboda yadda mahaifin mu ya din ga saka Mana suna Fatima, har se da nayi tunanin ko Muna da alaka da shi'a ne, saboda Naga yawancin sune mutanen da k...
186K 9.4K 70
🌹spin off Cinta Lelaki Teragung🌹 Do you believe in fate and destiny? And I believe that you are my destiny.. Eiman Firas x Rhea Sophea Louis She fe...
768K 15.5K 111
Yaszy Romano has been through so much pain and suffering her entire life but it makes her who she is. Dark Angel...Dangerous, Powerful. An Assassin...