RAYUWAR JIDDAH ✔

By DielaIbrahim

10.3K 856 277

RAYUWAR JIDDAH Labari ne akan rayuwar wata ya' mace mai suna Hauwa'u Jiddah. Let embark on the journey togeth... More

01
02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
AL'ADARMU
UMMI KWARAS
AL'ADARMU
AL'ADARMU

22

223 21 6
By DielaIbrahim

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/2
Mallakin DielaIbrahim

__________________________________
__
"On that very sunday"
*Daddy da Hafiz sukayi joining Mom a parlor dasu granny, zama sukayi suna ta hira cikin wasa da dariya har granny ke sanar da Daddy wai tayima lema miji"Daddy yace ahahhh Masha Allah ashe autana ta kusa zama Amarya itama
Leemarh ko tayi saurin rufe fuskarta tana kara shigewa jikin Mom, Hafiz yace Daddy ai brother din inlaw dinka shine sirikin namu,
"Daddy bai dauko zancen dakyau ba yace Come again son"
"Hafiz yace matar da zan aura to yayanta shi ke son Leemarh, shima jira yake ta gama NYSC ya turo ayi maganar aure, granny ta kara da cewa kuma mutumin kirki kuwa, sai ma ka ganshi wlhy"
"Daddy Koh baki yaki rufuwa tsabar murna, Autanshi ta samu miji dukdama baiyi binciki ba, Amma dagajin yadda su hafiz suke magana yasan yaran yayi 💯"gyaran murya yayi yace auta wai haka, to gaskiya hadawa za'ayi dana Hafiz Koh"

"Leemarh ta rufe fuska ta tashi ta ruga daki tana abin autanci, Mom na dariya tana cewa mara kunya da atsakanin mu nee da yanzu kin ishe ni da labarin shi.....kowa dariya yake tayi sannan suka canja hira, suna haka ne wayar Hafiz yasoma ringing yana dubawa screen din wayar, bakowa bace illah Hauwa'u Jiddah Junaid" His Final Choice"
Murmushi yayi ya dau wayar ya tashi ya fita, Mom ce kadai ta lura da yanayin shi,ta dago mai Kiran nashi.

"Dakinshi ya tafi, ya kirata back,bugu daya ta dauka......ya bude baki kenan zaiyi magana sai yaji siririyar muryar ta mai ratsa jijiyoyin jikin shi😘 ""Yaya Hafiz kazo yanzu please"" sai kuma ta kashe wayar, da sauri yasake dialing contact dinta amma har yayi tsinke Bata daga ba, ya kira yakai so biyar no answer.
Hakan yasa ya tashi ya shirya, cikin wani suit material maroon da wando milk color yasanya wrists watch ya gyara suman kanshi sannan ya dau car keys da phone dinshi, da sauri ya Isa parking lodge ya nufi daya daga cikin motocin shi, nan da nan escort dinsa suka biyo shi suna shirin shiga motar gabanshi, saurin daga masu hannu yayi fuskar nan babu annuri ko kadan, yace no need ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo, sanin halinshi baya son naçi sai kawai sukayi yanda yace.

"Minti 30 talatin yayi kafin ya isa gidan su Jiddah, yayi horn, gate man ya bude ya shiga, yayi parking sannan ya fita, bai tsaya kiran layinta ba, sai ya kira na Faisal bugu uku ya dauka hade dayin sallama cikin girmamawa yace sirikina"
"Hafiz ya shafa sumar kanshi kaman Faisal na gaban shi, yace Yayan mu an yini lafiya?
"Lafiya lau In-law yasu Mom da Leemarh?
"Alhamdulillah duk suna lafiya"
MashaAllah how may I help you In-law?
"Hafiz ya sake shafa sumar kanshi sannan yace dama nazo gida ne kuma na kira ta bata daga ba.....
Faisal yace batayi picking ba, toh ko bata kusa ne,
"Wlhy ban sani ba"
Alright"Bari na gwada kira ka dan kara jira Koh"
"Okay babu damuwa"

""Tun farkon shigowarshi harabar gidan take kallonshi kasancewar window dakinta yana facing compound din gidan gaba daya, amma ba lallai kagane akwai mutum tsaye a wajan ba, yau dinnan tsokana takeji kuma akan Hafiz take son saukewa hakan yasa ta samu paper full sheet ta zauna ta yaga kana na kana na, ta dauko fararan duwatsun data debo a garden dinsu ta rinka sanyawa a cikin paper tana dukunkulewa, har ta tara kusan guda ashirin sannan ta tattaro su ta dawo bakin window ta fara jefa masa tana yi tana boyewa jikin purple cotton din dake dakinta.

"Yana gama wayar ya koma ya tsaya jikin motar shi, yana dannan wayar sa, ji yayi an wurgo mishi paper an dukunkule ta da dutse,yayi saurin dagowa yana duba ta Ina aka wurgo masa, Amma baiga kowa ba, ya koma ya jingina ya cigaba da tapping phone dinshi, sai aka kara wurgo wata again, Nan ma ya sake dubawa Amma baiga kowa ba,ya koma ya jingina.
Haka aka ringa mishi har sau goma ana sha daya ne Faisal ya kirawo shi yace Guy na kirata fa bata daga ba, I think bata kusa da wayar ne"
Hafiz yace okay toh ba damuwa"
"Faisal yace Amma na Kira Momma gatanan zata dubata, ka kara jira."
"Toh yayanmu godiya nake*
"Bakomai"
Yana kashe wayar aka sake wurgo masa, wannan karan Hafiz ya kulu dukdama bai da tabbacin ko Hauwa'u ce, Amma ranshi na bashi she is the one"hakan yasa ya kashe wayar ya sanya ta a aljihu sannan yayi folding hannunshi ya daure fuska yana ta kalle kalle ko zai kama mutum, har ya tsura ma window din dayake suspecting daga nan ake wurgowa.

"Ko da taga yana kallon window din sai taja baya ahankali ta kwashe duwatsun tayi hanyar fita, sai taci karo da Momma tsaye abakin kofa, da alama da jima awajan tana kallonta, sosai ta tsorata Amma sai ta wayance tace, ahhh Momma na kece!
"Momma shuru ba answer sai sakon harara "Jiddah tayi magana har ta gaji, sai da Momma ta ga dama sannan tace zaki wuce kije ki same shi ko saina bata miki rai"
"Jiddah tayi saurin boye duwatsun ta kutsa ta gefen Momma ta wuce"
Momma ta girgiza kai, ita kanta abinda taga Jiddah nayi ya bata mamaki, Jiddah kaman wata karamar yarinya dai, ta kalli dakinnata dayake gyare tsab sai faman kanshin turare yake yi,as usual tace acikin ranta kullin dakinnan agyare babu ko kaya guda daya,komai yana ajiye a muhallinsa,Jiddah ce fah, ta juya tabar dakin.

...Yana nan tsaye Yana ta waige waige yaji an wurgo masa ta bayan shi, da sauri ya waiga amma wayam babu kowa, Hafiz dai ya kulu , kaman ya koma cikin mota Amma sai ya fara zagaya motar amma baiga kowa ba"

Ashe ta kasan motar ta hango kafafunshi yana shirin zagayowa, sai tayi saurin zagayawa itama Amma aduke tayanda bazai gane ba, har tazo inda bata iya ganin kafafun nashi sai ta tashi taga baya kallon wajan sai ta wurga yana juyowa ta duka Amma abinda bata sani ba shine ya ga shatin veil dinta, hakan yasa ya zagaya ahankali har ya iso bayanta with out her knowledge ta tashi, tana shirin wurga wani sai taga baya Nan, waige waige tafarayi har tazo wajan motar shi ta bude ta leka baya ciki tana dago kai ta hada ido dashi, gashi ta bude tafin hannunta ana ganin duwatsun, zare ido tayi sai tayi saurin jefar da duwatsun ta fara ja da baya.

"Hafiz yace karki kara taku daya daga inda kike,hakannan ta koma ta tsaya tana watsa da yatsun hannunta ta kasa kallon shi, ahankali ya soma takowa har inda take tsaye, har ya matso kusa da ita ya tsura mata idanu kaman me neman wani abu a fuskar ta, cikin sanyayyar murya wacce Jiddah kadai yake mawa yace"HAUWA'U"
"Tuni Jiddah ta rude tayi saurin rufe idanunta zuciyarta na dukan uku, ita dai tasan yanzu bata tsoron shi, kawai dai tsokanan datayi ne take tsoro kada yayi punishing dinta gashi dama ance sojoji idan akai masu laifi, frog jump suke sanya mutane"
Tana nan tsaye dabara ta fado mata tayi saurin bude ido da kyar ta kalle shi sai ta saki murmushi 😁 sannan tace Uhmm Yaya Hafiz yaushe kazo ashe kaine tanayi tana rawa da kafarta tana zare takalmi, Duk Yana kallon ta, sosai ta soma bashi dariya acikin zuciyarshi....a fili kuma yayi frouning fuskarshi ya koma ya jingina da motar shi yayi folding hannunshi sannan yace" Kince nazo, and gani nazo ya akayi?
Jiddah taji wani sanyi aranta Jin ya canja topic din, atunaninta ya hakura ne ta juyo tana washe baki to which kana nan dimples dinta suka baiyana, sai kuma ta Bata rai ta turo baki gaba tana cewa, ni..... ni..... ai dama Ina so ne naganka, yau kwana nawa ban ganka ba "Mi Alma"
Yaso ya biye mata Amma sai ya sake daure fuska yace, do you mean ba wani abu serious bane yasa kika kira ni Hauwa'u"
Jiddah ta zare ido tace kana nufin missing dinka ba abu mai muhimmanci bane dazaisa naji Ina son ganinka"ta kura masa idanu kuwa"
"Still Hafiz bai sauka ba ya daga mata kafada ko ajikinshi sannan ya duba wrist watch dinshi yana cewa,Shine danazo ai kike ta wurga min stones "Idan you are serious about it ai Ina zuwa zaki fito kizo ki ganni"ya fada cikin sigar shagwaba, any way ni zan koma gida bye ki gaishar min da Momma"
Har ya juya zai shiga mota tayi saurin binshi, tana langwabar dakai ta fara bashi hakuri" Amma Hafiz yayi kaman baisan tanayi ba, sai da yadau tsahon minti biyu kafin yace idan kina so na hakura sai kinyi "frog jump"
"Tashin hankali awajan Jiddah kaman me, ruwan masifa taso yi masa, Amma sanin darajar Hafiz da Kuma matsayin da zuciyarta ta bashi shiyasa tayi shuru da bakinta, sannan tasan laifinta ne don haka dole ta karbi punishment....ta soma bashi hakuri Amma ya kafe akan sai tayi frog jump"(Hafiz na son gwadata yaga shin zatayi idan ya sanyata)"

Hakannan tayi fuskar tausayi baiwar Allah ta duka zata fara kenan Hafiz ya taso shima ya tsugunna agabanta hade da rike hannayenta wanda ta kama kunnenta dashi....ya sanya idanuwanshi cikin nata yana kallon kwayar idon ta, yace cikin sanyayyar muryarshi mai zaki
" Lahhhhh, ban Isa na sanya sarauniyar da take mulki acikin zuciyar Hafiz Abubakar ba"ban isa nayi fushi da Hauwa'u ba infact Hauwa'u bata laifi awajan Hafiz, ko tayi laifin ma Hafiz mai Afuwa ne agareta, ako dayaushe Hafiz ya yafe mata laifin da tayi da kuma wanda zatayi nan gaba"Hauwa'un Hafiz"
"Jiddah ta saki baki tana kallon yadda Hafiz ke ta zayyano kalamai, sosai tayi farin ciki dajin abinda ya fada, ahankali ta sanya hannu ta rufe idanuwanta ta kasa ce mishi komai ta tashi  zata shige cikin gida, sai datayi nisa sannan juyo tace "You look good Yaya Hafiz"and nagode dakamin afuwa" tana kaiwa nan ta shige gida da sauri abinta.
"Hafiz yai murmushi ya shiga mota, ya sauke ajiyar zuciya mai dadi yace  Alhamdulillah nima nayi farin ciki dana ganki Hauwa'u"My day will never be dull when you are with me".....ya cigaba da tunanin yadda Jiddah take aiwatar da soyayyar ta gareshi, Hakika bata taba fitowa ta fada masa tana son sa ba, Amma action dinta ya nuna, moreover tanayin soyayyar cikin kunya da tsari babu rawar jiki irin ta yan matan yanzu".... HAUWA'U JIDDAH JUNAID Allah ya bani ke amatsayin mata kuma uwar 'ya'ya na" Yana kaiwa nan  yabarbar gidan.

Momma na kallonsu tun fitar Jiddah har suka gama drama dinsu, tana Jin dadin yadda suke tafiyar da soyayyar su, Addu'ar ta daya Allah ya barsu tare, Allah yasa su auri juna, tana jin soyayyar Jiddah acikin zuciyarta tasan akwai ranar da dole Jiddah zata tafi gidan mijinta, tana tunanin yadda zata iya jure rashin Jiddah, ahankali ta share kwallarta ta bar dakin cikin sauri don tasan Jiddah zata iya shigowa yanzu.

"Hafiz ya koma gida ya samu Mom da granny ya uzzura musu wai su fadawa Daddy yaje ya nema masa auran Hauwa'u" ranar Mom taga tabara kala kala, tace Babana ko kunyana bakaji, ya sosa keya yana cewa Mom ba haka bane, sai kuma ya tashi ya tafi daki yana mai Jin kunyar abinda yayi.....granny ko dariya ta ringa yi tana tsokanar shi wai zai mata kishiya.lol

After 2days
Ranar Wednesday aka tashi da azumin watan Ramadan" wata mai albarka, watan da ake yanta bayi,"Jiddah na kwance saman kujera a sitting room din Momma iska mai dadi ne keta faman shigowa dakin, waya takeyi, kallo daya zakai mata ka hango tsantsar farin cikin da take ciki, waya takeyi babu wani tashin hankali, kuma kowacce magana sai ta tauna ta kafin ta fade ta,,, ba da kowa take waya ba illah Hafiz wanda ya nutse sosai cikin kogin son Jiddah, barinma idan tana masa kalamai, bai taba sanin haka Hauwa'u ta iya kalaman soyayyah ba....yace Hauwa'un Hafiz azumi nawa zakiyi?
"Jiddah ta bude baki alamar tambayar tai mata girma, tace duka inshallah"
"Hafiz yace anya ba azumin bakin randa zakiyi ba, nifah kaman ma Yaya Faisal yace karfe sha biyu (12pm) kike shan ruwa, idan Kika sha sai washegari zaki sake dauka shima ki karya 12pm.... wai awajanki kinyi guda daya kenan"""ya karashe maganar fuska a murtuke kaman ba shi yai maganar ba.
"Jiddah ta rasa me zata ce mashi, sai tace Yaya Faisal ko, shine zai kala min sharri, ta karashe maganar kaman mai shirin fasa ihun kuka" sai da Hafiz ya lallasheta kafin yace toh Allah ya baki ikon yi duka"
"Ameen ta amsa tana wasa da yatsun hannunta"
"Hafiz ya kira sunanta, ta amsa, sai yace" Daddy yace na tambaye ki yaushe zasu zo a nema min aure a gidan ku"
"Jiddah ta rufe fuskarta kaman Hafiz na kallonta, sannan tace aa Yaya Hafiz bani ba" sai dai kazo kuyi magana da Momma da Yaya Faisal"
"Hafiz ya gane kunya takeji sai yaita tsokanar ta, tana masa shagwaba "Nikam Yaya bana so Allah, ka bari" Amma Ina haka yaita tsokanarta har ta kashe wayar tana cewa na shiga uku Yaya Hafiz bazan iya ba😂

***************
10th of May,2019
Yau kwana goma sha shidda (16)days da azumi, and yaune ranar da Daddy da brother dinshi Alh.Yusuf suka shirya zasu je gidan Momma kai gaisuwa, gidan Daddy kuwa ya cika da Yan uwa, babbar yar Daddy (Khadija first daughter din granny) wacce take aure a London tazo don ita dama once in a year take zuwa kuma da Ramadan tayi sallah sannan su koma da yaranta, sai kannen Daddy  Maryam da Fatima wanda suke aure a Abuja, sukan dau lokaci suma kafin su zo gaida granny..... Kamar yauma tare da jikokin granny sukazo yadda kasan biki ake agidan.
"Kowa yasan Hafiz yasan cewa shi bamai yawan son magana bane a Family,Kuma ba kasafai ya fiya shiga harkar mutane ba sai dai Leemarh kadai yake shiga harkarta sosai, Amma yau labari yasha ban ban, yau Hafiz shine harda hira da yara mata cousins dinshi sosai ya sake dasu ba mazan ba,ba matan ba....Mummy Khadija tana da yaro babba "Imran" and sa'an "Hafiz" ne so tare dashi sukaita yawo don shima auran zumunci zasuyi da daughter din Mummy Maryam.
Family din dai acan acan ba hayaniya kuma gaba dayansu a gidan suke sauka saboda babban gida ne Wanda yake dauke da bangarori daban daban, kuma wannan duk plan din Daddy ne, shi ya siya filayen gefen sa ya hade ya Gina.......shiyasa yayi yayi Alh.yusuf ya dawo su zauna tare Amma ya kiya, sai shi ya zauna a malali....wannan kenan.

****KINKINAU*****
"Daddy, Alh.Yusuf,sai abokanan Daddy guda biyu suka yi sallama a kofar palor, gidan Momma, Faisal shi yai masu jagora shida Yaya Idris da Isma'il, sukai masu tarba na mutunci sosai sukaji dadin tarbar dakai musu dukda lokacin azumi ne, sannan sukayi magana da Momma....inda Momma take cewa mahaifin Jiddah yana katsina, and cen yakamata suje,Amma yanzu ya nema musu sauki....  Momma ta kara da cewa munyi waya dashi yace mu amsa gaisuwan anan, idan sukazo neman auran Halima wa muhammad sai asanya rana alokacin.
"Alh.yusuf yace Alhamdulillah, MashaAllahu hakan yayi godiya muke Allah ya saka maku da alkhairi,Allah ya sanya Alkhairi a wannan hadin da za'ayi", Allah ya kade fitina"
Ameen kowa ya amsa, haka sukai ta godiya daga karshe Alh.yusuf ya bada umarni a shigo da kayayyakin gaisuwan haka kuwa akaita shigowa da kwalayen biscuits, sweet, kullin goro irin manya manyan nan yakai dauri goma, ga kudi da suka bayar dubu dari biyu wai kudin gaisuwa"
Momma tace aa kudin sunyi yawa Ina laifin dubu goma, Abu na mutunci"
" Daya daga cikin abokin Daddy yace aa Hajiya kuyi hakuri ku amsa wannan gaisuwa ne, idan yaso sadake sai ku yanka mana adadin kudin da kuke so"
Hakanan suka amsa" sannan Momma tasa almajirai suka kwashi kaya su cake, doughnuts, katan na juice da ruwa aka Sanya musu a mota, wai tukwici, suna ta godiya kuwa.

Ranar Jiddah bata gida tana Unguwan rimi gidan su Fatima, sai aranar Fatima ke sanar da ita Yaya Faisal na sonta,....wayyo Allah karkuso kuga yadda Jiddah ke murna Besty zata auri Yayanta...har da rawa tana tsalle abinta.
Fatima tace dallah ji sai wani murna kike, to ni haryanzu ban sanya araina zan amince ba......
"Haba yarinya karyarki wlhy, kin ma isa" yayan nawa guda daya, ya zabe ki cikin dubu ki watsa masa kasa a ido" Besty baki isa ba fah"
"Fatima ta ce tohhh sannu uwa ta, sai kawai inyi abinda zuciyata bata ra'ayi, nifa banga Wanda ya Isa ya sanya ni dole ba eheeee babu ruwana dawai Yaya Faisal ne, ai shi so baya duba wannan, wani son lokaci Daya yake shiga, wani Kuma ahankali yake shiga, Amma nikam haryanzu ko daya ban jiba.

"Sosai maganganunta suka bawa Jiddah mamaki ta kasayin magana,tayi shuru tana son ta fahimci Fatima, tace Fatima me kike nufi kenan?
"Fatima tace kamar yadda kikaji na fada Jiddah, zuciyata bata aminta dashi ba, nayi nayi nasanya shi araina Amma na kasa Jiddah"

"Ai Jiddah kasa magana tayi ji tayi Kaman a cire mata wata jijiya a jikinta, tayi tagumi tana tausayin Yaya Faisal, taji dadin good news din da Fatima ta bata, Amma bataji dadin amsar taba, though bata isa tayi forcing dinta ba, tasan kowa yana da choice kaman yadda itama ta samu choice dinta,, shurun da tayi tana tunanin to solution ne,tace da Fatima toh Amma Yaya Faisal miye baidashi fatima, indai kyan hali ne to nayi imani yana gaba gaba, idan wajan kyau ne,Ilimi kuwa basai an fada Miki ba kinsan Yaya Faisal har Sanawiyyah yayi kafin ya tafi POLAC kinsani sarai Yaya Faisal ba baya ba wajan kyau da iya dressing, saboda kyakkawa ne na karshe dukdama  Baki ne Amma kyan nashi baya boyuwa, sannan idan kudi ne kinsani fatima Yaya Faisal ya tara kudi yayi karatu Yana da aikinsa, ayanzu bukatarshi yasamu macen da zata so shi tsakani da Allah,ta kula dashi tsakaninta da Allah, Fatima meya kike son guje mishi ne, koh dai baki so ki shigo Family dinmu ne?
"Fatima ta kura wa Jiddah idanu, sannan take " ban damu da auran Namiji kyakkyawa ko mai kudi ba, burina na samu miji na gari wanda zai kula dani ya soni har karshen rayuwarshi, Jiddah bawai bana son shigowa family dinku bane,Noooo duk macen da ta samu family kaman naku Kuma tayi dacen miji kaman yaya Faisal toh hakika tayi dace, Jiddah matsalar bana jin soyayyar Yaya Faisal araina, bansan yadda zanyi ba Jiddah"

" Jiddah ta fahimce ta, ta busar da iskar bakinta, tace Na fahimce ki Fatima, zan baki shawara ki dage da addu'a, sannan kada ki nuna masa baki sonsa, da sannu Allah zai kawo miki mafita, don Ni a tunani na , da ka auri mijin da kaine kake sonshi, toh gwara ka auri wanda yake sonka kuma kake da tabbacin zai kula dakai dari bisa dari, so Ina so ki zauna kiyi tunani da zuciyarki ki fahimci wane ne Yaya Faisal, inshallah komai zai zo miki da sauki kinji kawata.

"Fatima ta rungumeta tace nayi missing shawaranki besty, Kinga yau kin kwantar min da hankali Kuma inshallah zan bi yadda kikace, thank you dear"
"Jiddah tace don't mention tsakaninmu babu godiya"
Ranar dai a gidan su Fatima ta kwana, Hafiz kuwa ya kira line dinta yafi akirga Amma batayi picking ba saboda tasanya wayar a silent, Kuma dazata kwanta bata bi takan wayar ba.
Sai ta suka tashi yin sahoor taga Miss calls,shine ta kirashi.....Kuma bugu daya ya daga, ta bashi hakuri yace karta damu dama yana son yaji ko tana lafiya ne"
Daganan kuma sukai ta hira har aka kirawo sallar asubahi, Fatima nata tsokanar ta wai masoyan asali HAUWA'UN HAFIZ  Jiddah tace Hmmm fadi ki kara yarinya sunan a rubuce yake😂

***************
Kwanaki nata tafiya, lokaci yana ta gudu, gashi yau take Sallah, kamar yadda kukasani ko wani gidan masu kudi hidima sukeyi Sosai ranar sallah to hakan ta faru a gidan su Hafiz da gidan su Hauwa'u.
Bangaren Jiddah kuwa.... Tsaye na hango ta sanye da apron da hular,hannunta kuwa yasha kunshi traditional henna yayi mata kyau kuwa dukda duhun fatar ta, tana ta faman aikin salad, ta gama ta hada special juice daban daban, ta gama ta karasa fried rice din da Momma keyi ita Kuma Momma tayi party jollop rice, tanayi tana cewa Yar aikin Momma ta duba tukunyar alale ko tayi, haka sukaita kokarin karasa aikin har karfe takwas tayi lokacin Yaya Faisal ya fito sanye cikin farar shiddah harda babbar riga kallo daya zakai masa kasan shaddar Mai tsada ce, ga cover black hular kanshi ma abin kallo ce.....""Jiddah ta tsaya kallon shi tana dariya tace Yaya Faisal ka ganka kuwa, kamar ranar auranka wlhy😘
"Faisal yace Allah kohh"
"Yeah wlhy kayi kyau, kaje ka dawo in cire maka hoto mai mugun kyau" yayi dariya yace alright sai da yaje ya manna wa Momma kiss a forehead sannan ya fita yana cewa Jiddodooo ki tabbatar kafin na dawo kin shirya sboda ki amshi barka da sallan ki da hujja.
"Jiddah tayi dariya tace inshallahu kuwa yanzunnan Yaya, Yana fita suka cigaba da aiki zuwa karfe tara sun gama shirya komai a warmers sboda jikokin Momma na hanya don ko wacce sallah gidan cika yakeyi da Yan uwa da abokan arziki.
"Jiddah tayi sauri ta nufi daki tana cewa Momma zanje nayi wanka tun da mun kare aikin.
"Momma tace okay "

Tsahon awa daya ta dauka tana shiryawa, sanye take cikin lace mai tsada peach color dinkin yai masifar amsan jikinta tana ta faman shiri har dai tafara Jin hayaniyar su Yaya Isma'il, tace lahhh har sun dawo uhmmmm, bawani make up tayi ba gaban gashin kanta ta gyara ta zauna tayi daurin Dan kwali na gani na fada, tana tsaye sai ga yara sun shigo da gudu suka rungumeta,
"Ita ma ta rungume su tana cewa hope kun kawo min barka da sallah na?
Babban cikin su yaran Idris mai sunan Ayman yace Aunty Jiddah, ai Daddy yace ke zaki bamu happy sallah"
Jiddah tace uhmmmm to ku fada min me kuke so na baku yanzu"
Mai bi ma Ayman tace Aunty Jiddah park zaki kaimu "Fantasy park" Jiddah tace okay zamuje park Amma sai gobe yanzu Bari na baku barka da sallan ku dana ajiye muku .....sai suka fara ihu yaaaayyyyy, yaaaayyyyy, yaaaayyyyy suna tsalle, haka ta basu sabbabin yan hamsin hamsin, suna ta murna, tabi bayansu suka tafi palour....ta gaishe dasu yayyin nata, suka ci suka sha, daganan sukafara hotuna as usual akayi family photo.
Ranar dai Jiddah tana cikin farin ciki sosai don Hafiz ma yazo yako kawo mata sallah gift, taso taki karba Amma yace bawai ya bata saboda yana sonta bane, ya Bata ne saboda tana matsayin kanwa agareshi, sai ta amsa.
The next day ranar biyun sallah ta kwashi yaran , driver din Momma shi yakaisu park din, they had fun sosai sai yamma suka koma gida.
The next day
Fatima tazo, haka Leemarh ma tazo gidan su Jiddah, Jiddah taji dadi sosai, Kuma sosai ta sake dasu suna ta hira, tana fada musu itama ai KASU tayi yanzu NYSC takeyi" Fatima tace aahhh kinji dadi muma Allah ya nuna mana ranar da zamu gama mu Sanya uniform din...suka amsa da ameen ya rabbi.
Da zata wuce kuwa Momma tai Mata kyauta, harda sako wai takaiwa granny da Mom....sosai Leemarh take godiya, sannan Momma tasa driver yakai Leemarh gida tare da Fatima suka tafi....sai da aka ajiye Leemarh sannan aka kai Fatima itama.
********
1 week later

Abba da Family dinshi suka dira a kaduna, dama yasa Faisal ya nema mishi babban gida,ya siya aka gyara aka sanya furnitures, toh yanzu su Ummi a gidan suka sauka abinsu dasu Muhammad da Saifullah sai dai su Jiddah da Momma suka bisu cen "Marafa Estate" niki niki da warmers na abinci, anan sukaita hira har bayan sallar isha'i sannan Momma ta koma ta baro Jiddah.
Bayan kwana biyu Abba yasa asanar da Daddy wai zasu neman auran Halima"Leemarh"
Kuma Daddy yace kada su damu, zasu zo ayi komai agidan Abba, Abba yace haka za'ayi"
Daddy yace inshallahu....Abba yace to ba damuwa sai ku sanya ranar da zaku zo Koh"
Ranar Friday suka shirya zuwa, agidan Momma aka shirya haduwa, Ammi da Mama suma aun iso, ranar gidan babu wanda bai zoba gidan ya cika makil da yan uwa, Jiddah da Fatima suna cen kuryar daki bama za kasa da akwai hallitar su acikin room din ba, saboda ahankali suke magana abinsu.

*******************

Vote
Comment

Continue Reading

You'll Also Like

Daisy By Sin

Fanfiction

2.8K 128 9
TokyoRevengersXQinShiHaung!Fem!Reader PAUSED
1.4M 117K 110
Kalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka...
185K 3.6K 15
"Darling, you're the one I want." ranked #3: beckoliver (3/7/2022)
2.3K 231 15
Saboda yadda mahaifin mu ya din ga saka Mana suna Fatima, har se da nayi tunanin ko Muna da alaka da shi'a ne, saboda Naga yawancin sune mutanen da k...