RAYUWAR JIDDAH ✔

By DielaIbrahim

10.5K 875 277

RAYUWAR JIDDAH Labari ne akan rayuwar wata ya' mace mai suna Hauwa'u Jiddah. Let embark on the journey togeth... More

01
02
03
04
05
06
07
08
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
AL'ADARMU
UMMI KWARAS
AL'ADARMU
AL'ADARMU

09

247 30 2
By DielaIbrahim

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/09
Mallakin DielaIbrahim

***********
Juma'at Mubarak🕌to you all👏
********
The following morning " Jiddah" bata jira yaya faisal ba tayi wucewarta hospital....ko daya fito yasamu momma zaune a palour gaishe ta yayi sannan ya nufi dakin Jiddah sai dai bai sameta ba ya fito ya duba kitchen nanma bata nan, Momma na kallonshi yana ta dube duben sa bata ce masa kala ba. Sai da ya gaji ya dawo palour yace Momma where's Jiddah?
Momma ta amsa masa kai tsaye "she left early today"
Faisal ya dan zare ido kadan alamar mamaki yace shine bata jirani ba Momma and kuma kika barta ta tafi ita kadai"
Momma ta dan kalle shi sannan tace ni kaina sai data gama shiri,sallama tamin kawai kuma ko abinci bata ci ba.......""ohhh Jiddah what wrong with her! Momma hada min breakfast dinta na kai mata, bai kamata ta fita batareda tasa wani abu a cikin ta ba.
"Uhmm indai Jiddah ce kada ka damu kanka "tana fita ta kirani tace zata ci abinci inshallah idan ta Isa hospital din"
Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace Momma hada min nakai mata, fushi takeyi dani kuma ni bana so tana fushi dani.
Hakanan Momma ta tashi ta nufi kitchen ta hada breakfast a food flacks mai kyau ta mika masa hade da cewa good luck.
"Thank you Momma"sannan ya tafi cikin sauri.

Ranar batayiwa kowa magana ba ko Fatima ma tayi magana har ta gaji ta rabu da ita, itanan fah aganinta hakan ne zaisa taki haduwa da Hafiz Amma it turn out to be bad day for her as she thoughts..
Tana zaune a Phlebotomy babu patient sosai ranar,kawai sai gashi an kawo mata form har uku, guda biyu taje ward ta ansa sample daya kuma taje A&E, ta shirya komai a tray ta tafi with full of confidence and excitement, ward tafara zuwa ta gama sannan ta nufi A&E tana shiga gabanta ya fadi sakamakon jin kamshin turarenshi Wanda tun ranar da suka fara haduwa taji kamshin and from that day inta hadu dashi saitaji thesame scent na perfume din, ko data shiga bata tsaya kalle kalle ba sanin cewa yana cikin ward din sai kawai ta nufi wajan doctor ta nuna masu form tazo ansan blood sample take suka nuna mata patient din, tabi da idanunta direct inda matar take pointing.
Zaune yake kusa da patient din yana rubbing hannun patient,
ta maida idanunta kan patient din wanda yake kwance sanye da kakin sojojin army idanunsa a rufe, ta sake duba form din wajan da aka rubuta rank anan taga rank dinshi patient din wanda captain ne....ahankali ta nufi wajan fuska daure kaman bata taba dariya ba dan dimple din dayake fitowa ma ko shi ba'a gani, tana zuwa wajan sallama ta farayi Assalamualaikum!
Ya dago kai yana kallon ta muryar ta kadai yaji ya gane itace, amsa sallamar yayi ciki sannan ya maida kallonsa ga tray din hannunta ita kanta ma ba kallonshi takeyi ba patient ma take kallo abinta.....Hafiz yayi murmushi ya mika hannu ya amsa tray din, Handgloves ya sanya ya dauki tourniquet ya daure hannun patient din sannan ya soma kokarin Sanya masa 2ml syringe, "Jiddah tana kallon sa batace mashi komai ba, tana ganin yadda yadda aiwatar da aikin perfectly dama ya iya jan jini,har ya gama ya rubuta sunan a containers din sannan ya mika mata batareda yace komai ba..ganin ya gama ta amsa tray din zata tafi sai taji yace "Hauwa'u" come let me send you to my office please!"
Jiddah taji magana kaman daga sama,ita batasan dalilin daya sa yake kiranta da Hauwa'u ba although sunanta ne amma ayanzu rabon da wani ya kirata da sunan har ta manta sai dai Jiddah, gashi sunan yayi suiting din bakinshi sosai saboda aduk lokacin daya kira sunan saitaji wani abu aranta ta waiga tana cewa me?
"Yes you"ya bata amsa.
Haushi taji sosai aranta kaman  taki zuwa, hakanan ta dawo ta same shi aranta tana cewa badan halinka ba, don Allah nayi.....Shikam ko a kwalar rigarsa tana isowa yace mata taje office dinshi, zataga wata mata, please ki taimaka mata ki kaita Lab dinku FBS za'ayi mata, kice mata aiki ne yamin yawa anan and you will take care of everything.
Hakanan ta tafi tana tura baki gaba, har dawani cewa I'll take care of everything aikuwa zaigani, ko data kusan kaiwa ahanya ta iske course mate dinta, habawa sai kawai tabi su suka koma Lab dama ta taho da tray din samples din tana zuwa takai cikin Lab sannan ta koma wajan zaman ta, ta fara ansan samples,
Fatima ce tashigo tana ce mata, An kawo mata sako yana common room, batareda ta saurari me Jiddah zata fada ba tayi wucewarta.
'Jiddah tunda taga reaction din Fatima tasan lallai ta batawa besty rai, tayi sauri ta gama ta dau excuse kasancewar ba ita kadai bane a phleb din, zuwa tayi bench din Fatima ta janyo hannunta suka tafcommon room sai da suka zauna sannan tace" bestyna,teemah na,fushi kike da Jiddah?
Fatima tayi banza da ita tana danna wayarta, Jiddah ta fizge wayar sannan tayi fuskan tausayi tace please am sorry!
Fatima tace ya wuce ai karki damu bani wayana.
"Jiddah ta make shoulder tana cewa sai kin saki ranki tukunna"
Fatima tace na saki, bani
"No smile please"
Fatima ta bude hakwaranta ta hade su waje guda sannan tayi dariya kaman haka😬
Jiddah ta zare idanu😲tana cewa is this a smile haba bestyna bansanki da fushi ba fah!
Fatima ta harareta cikin wasa taja kunnanta tana cewa naughty girl zaki sake....Jiddah tayi kara kadan sannan tace am sorry ma'am fatima I'll never do it again"ta fada tana kallon ta "sai Fatima tace nooo not ma'am it's sister oyaaah say it har lokacin tana rike da kunnan" da sauri Jiddah tace am so sorry sister Jiddah ta fada tana hade hannayenta waje guda..........
Take kuma suka fashe da dariya suka rungume juna, "Jiddah na cewa Yaya Faisal ne ya bata min rai jiya" yau kuma bana so na hadu da wancan dan iyayin amma sai da na ganshi wallahi "what a bad day for me"
Fatima tace" really a bad day gaskiya" tayi dariya sannan tace ai Yaya Faisal breakfast ya kawo maki kuma yace in tabbatar kin ci saboda bakiyi breakfast ba....and shi kuma wancan kada ki damu dashi ba tashi muke ba kinji" Jiddah ta gyada kai tanamurmushi sannan tace Allah sarki Yaya Faisal ya wanke kanshi tunda ya kawo min abinci kaman yasan ina jin yunwa,Ina abincin toh?
Fatima ta dauko suka zauna sukaci golden yam with egg sauce, samosa sai kunun tsamiya, suna ci suna hira harda shewa suna gamawa suka bar common room din.
Fatima ce ta fara yin gaba Jiddah na baya bata ankara ba taga mutum tsaye gaban ta yana kallon cikin idanunta.
Jiddah kaman zata juya ta koma cikin common room amma ba hali, hakan yasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta....azuciyarta kuma ta tanadi maganganun da zata watsa masa matukar ya fada mata ba dadi. minti biyar kacal yadauka yana kallonta batareda yace kala ba, "Jin shurun yayi yawa yasa ta dago kai ahankali ta kalle shi, sai daga ita din yake kallo.......tace malam lafiya?
"Hafiz yace me kika gani ya tambaya?
"Jiddah ta tura baki gaba tana cewa ka tsareni da ido kaman kabani ajiya na cinye"
Dariya sosai tabawa Hafiz amma sai ya daure fuska  sannan yace me nace miki dazu, ba aikenki nayi ba?
"Yes aike na kayi amma ai ahanya ta na zuwa aka aiko kirana shine na taho abuna"tana magana tana juya idanu
"Hafiz yana kallon yadda takeyi da karamin bakinta, idan tana masifa ba karamin kyau takeyi ba tuni ya shagala da kallon kyakkawar fuskarta, "Jiddah ta kutsa zata bar wajan sai taji magana kusa kusa da kunnan ta yace "am not done with you yet" stay back!
"Jiddah taji maganan har cikin jinin jikinta amma sai ta basar ta wuce without saying a word,binta yayi da kallo har ta kure wa idanunsa,ayayinda zuciyarshi take mashi wani magana daban.....yana tambayan kansa meyasa yakejin farin ciki aduk lokacin daya ganta, meyasa zuciyarshi ke tunzura shi akan impossible to be possible, could this thing that am doing called LOVE or what? No no nooooo it can't be possible yayi saurin barin wajan ya koma office ya taho da Mom yana bata hakuri akan aiki ne sukai mashi yawa Amma yanzu he is here for her!
Har suka isa Lab din yamata komai aka bata form ya shigar da ita phleb, Jiddah ce kadai so aje form din yayi tareda gyara kujera yana cewa Mom zauna anan,
"Mom ta zauna hade da kallon Jiddah wacce idanuwanta a rufe suke batamasan da mutane awajan ba don da alama bacci takeyi.
"Hafiz yayi knocking kujeran Jiddah" firgigit ta fadi lokaci daya taji nauyin matar,....sai kawai ta tsinci kanta dacewa "Ina kwana Mama""Jiddah ta kira ta da Mama ne saboda tasan matar ta Isa ta haifeta" ta gaishe ta cike da ladabi idanuwanta da fuskarta suna kallon kasa" to which hakan datayi shi ya birge Mom yarinyar ta shiga ranta lokaci daya ta saki murmushi tana amsa gaisuwar tace lafiya lau, ya aiki.
Alhamdulillah Mama ya karfin jiki?
"Jiki Alhamdulillah Daughter"(Mom ta tsinci kanta da kiran Jiddah as Daughter)
Jiddah tace Mama me za'ayi miki ta tambaya batareda ta kalli Hafiz ba saboda ba taso ta shiga harkarshi ko kadan" Mama tace FBS za'ayi min zan samu yau kuwa?
Jiddah tace yes inshallah ai fasting blood Sugar baya jimawa zan rubuta urgently a form din and zan jira har ayi maki, Amma zaki iya jira ko"
Mom tayi murmushi tace me zai ha na Daughter I'll wait,thanks much dear
Jiddah tayi shuru saboda nau yin matar da take ji aranta"( Ni ko Diela nace su Jiddah dama ana ladabi irin haka kodai don taga sarukuwarta ne😂)"
"Hafiz dai ya zama Dan kallo, hakanan ya lura Jiddah bata ko kallon inda yake, ita kuma Mom saboda tasa mu yarinya shine ta manta dashi awajan"
Jiddah na gamawa ta ce Mama zaki iya jira a reception bari na shigar da forms din"
Okay Mom ta amsa adaidai lokacin data tashi tana yima Hafiz magana, tace son bari na jira sai na kai ma doctor ya duba kawai ayau koh,
Hafiz yace eh hakan yayi Mom, muje reception din ko mu jira acen.

Jiddah bata dawo ba saidata tabbatar anyi centrifuging sample din, taga an dauka za'a fara test din kafin ta wuce phleb, tanayi tana shiga ciki tana checking ko an gama, after 30min ta shiga ta ansa results din  sannan ta kai reception ta bama Fatima ta shigar sannan taba su, Mom tace thank you kinji Allah yai maki albarka"
Thank you ma! Tai mata sallama ta tafi. Faisal kuwa yana zuwa office ya hadu da Isma'il brother dinshi as usual daman ya fada, yace Abban afnan ya akai kamin sammako ne, karan wani ka kawone?
Isma'il yace similar things, kafini sanin abinda ya kawo ni ai, ya fada yana hararanshi playfully yace Faisal ka canja al'amuranka kwanakinnan ,kwata kwata baka nema na,ka dena neman shawara awajena, infact problems dinka ma you don't share it with me.....Faisal Anya babu abinda kake boyewa kuwa wanda baka son kowa ya sani....
Faisal dayayi tsaye Yana sauraron Dan uwan nasa fuskar shi dauke da murmushi cike da annuri, yaace Ismail ba abinda kake tunani bane, as you can see am too busy at office kullin cikin case muke, ba hutu ko kadan, problems kuma babu ne saboda kasan inda akwai you will be the first person to know about it....so wannan ba abun daga hankali bane.
Okay yanda kafada cewar Isma'il sannan yace Amma maganar jiya fah ,is like something is really fishy between you and Jiddah, ya kalli Faisal da yake mashi kallon tuhuma.
Isma'il yace noooo don't look at me in that way am telling you the truth Faisal kasan ni Ina da hangen nesa and I don't hide things,so please my advice here is, Jiddah sister dinka ce idan kasan kana sonta ne, toh you better tell her now, kafin ta fada tarkon wani, kai kuma abarka da sakakkaken baki......Faisal yayi dariya yana cewa Ahhhhh brooo you know girls too much ehnnnnnn a"
Isma'il yace that's the fact bro kanaji kana kallo zata barka ta koma wa wani cen, and kasan dai gida bai koshi ba, ba'akaiwa dawa ba"
Faisal ya dan gyada kai yana tabe baki kaman irin maganar bata shige shiba, Isma'il yace uhmm nidai na gama nawa zan tafi, yauwa maganar tafiya na jibi ne, shiyasa nazo yima Momma sallama zan tafi da mammyn affan ma kasan karatun 2years ne (masters)and gaskiya bazan iya yin 2years without my family ba....Faisal yace kana da gaskiyan ka, kasan dama nace maka idan zaka tafi to is better ka tafi dasu saboda kewa da sauransu, "Isma'il yace yeah nima abinda nagani kenan"tohh bro bari naje office yau na maka sammako,sai munyi waya
Faisal yace alright zan kira ka before you leave."
Okay bye"
*******************
After one week(Bayan sati guda)
Ranar asabar ita ce ranar dasu Ummi zasu zo all the family..hakan yasa tun da asubahi Jiddah ta tashi,ta kama shirin tarban family dinta, SashinYaya Faisal ta nufa sannan to ta taso shi gaba, dama idan zatayi aikin snacks shi take kira don dole take masa saiya taya ta haka zata daura masa apron har da hulan chef suke sanyawa so da dama weekend sukeyin aikin kitchen tare haka abokanan shi idan suka zo weekend zasu sameshi a kitchen da ita Jiddah,sai dai su dauko masu kujerun dinning suce su zauna  sunayi suna taya su hira abin gwanin ban sha'awa.....yauma dai hakan ya kasance tana taso shi karfe bakwai na safe ya tashi yana mata mita, tace nifah Yaya Faisal karkamin wani magana dukwani mita dazakayi kayi saifah munyi aikinnan tare as team kasan dama mun saba Koh ta kanne masa ido daya wanda ba karamin killing Yaya Faisal yake ba, haka ya bita suka soma aikin snacks din which includes samosa, doughnuts and cakes along with different kind of drinks, Momma kuma tana ta fama da girke girken abinci ita da Yar aikinta Ladi kasancewar kitchen din babba ne sosai kowa yakama angle dinsa suna yi suna hira abinsu, "Momma tace karfi da yaji Auta ta maidakai Chef Faisal"
"Faisal yace wallahi Koh momma ai ki bari yanzu fah abokanai na Chef suke kirana wai babu abincin da ban iya girkawa ba, kuma Momma duk aikin Autanki ne ita ta koyamin"
Toh ai taimakon ka tayi kaga idan matar ka bata da lafiya saika tayata aiki da girkin abinci ko ba haka ba Ladi ta karashe tana tambayar mai aikin kasancewar babban macece zata kai shekarun Momma"
Ladi tace kwarai kuwa Hajiya ai ni Ina son naga namiji ya iya girki kada matarsa ta raina masa wayoooo"
Jiddah dai na sauraron su bata sako masu baki ba, "Faisal ne ya kalle ta smiling yayi ya matsa bayanta ya kai bakinshi dai dai setin kunnenta yace ahankali "My little girl tunanin me kike tunani"
Murmushi kawai tayi ta waiga gefen da Momma take tace Momma Yaya zai fasa min kunne kimishi magana Allah!" Momma ko tagansu sanda yake mata magana hakan yasa bata kula Jiddah ba, tunani barkatai ya fara zuwa cikin kwanyan ta akan ko dai akwai abinda yaran suke boyewa ne....sai kuma tayi murmushi tace da ace abinda nake tunani gaskiya ne danafi kowa murna, ta cigaba da aikinta tana ta tunani aranta... karfe sha biyu suka gama komai, Jiddah da Faisal su suka shirya komai a dinning sannan suka tafi daki don su shirya.
Misalin karfe daya da rabi (1:30pm) motocin su Ummi sukayi horn, Mai gadi ya bude musu suka shigo motor biyu ne sukayi parking a bangaren da aka tanadar domin aje motors.  Yayinda motar farko wani kyakkawan saurayi ne ya fara fitowa yana sanye da gizna(shadda) sky blue dinkin kaftan sai hula zanna sai kyalli takeyi, gefen driver seat ma wani saurayin ne ya fito wanda shi kuma ya dara dayan haske sosai to which hasken fata ne kawai zai nuna ma dayan amma banda kyau..... murmushi sukayi alokacin da suka kalli juna sai farin yace ya muhammad kalli su Ummi sai wani soyewa sukeyi da Abba sai kace yau suka fara haduwa🤣sai kuma suka maida kallon su ga iyayensu wanda suka fito tare suma adayar motar, Ummi tace yaran nan akwai gulma acikin ku yanzu me kuma mukayi dayasa ku Smiling?

Wanda aka kira da Yaya Muhammad ya make shoulder yana cewa Ummi me zamuce babu fah, uhmmmm ku shiga muje.
Faisal ne ya fara hangosu habawa tuni ya tare su da murnarsa, suka rungume juna da samarin cike da kewa, Faisal yace Ummin mu Abbanmu sannunku da zuwa, Abba yace yauwa Faisal,Ummi tace Faisal nikam fushi nakeyi dakai fah ta fada alokacin da suke shiga cikin gida, Faisal yace Ummin mu ayi hakuri nasan ni mai laifi ne, don Allah ayafe min ya fada yana hade hannayensa waje biyu.
Abba yace Faisal rabu da Ummi kaji neman rigima takeyi fa duk ta kosa taga Autan tane shiyasa take fadin haka,"Ummi tai murmushi kasancewar ta mace mai alkunya da kawaici sometimes"su Muhammad suka fashe da dariya alokacin da suke karasa shiga palour din.zama sukayi da Momma suna ta Hira cen saiga oga ta fito"Jiddah" sanye take da doguwar rigar abaya black da cover golden, sai black veil da tayi rolling kanta fuskarta babu ko powder kasancewar bata shafawa sai dai kwalli kawai kuma ahakan ma tsantsar kyawuntane ya fito ayayinda Faisal ya zuba mata idanu yana jin wani abu nadaban acikin zuciyar shi.
Just like a small baby da gudu ta rungume Ummi da Abba sannan Yaya Muhammad da Saif tana cewa I missed you all, suma suna cewa sunyi missing dinta,daga nan sukaje sukaci abinci suka huta ,
Jiddah ko da sauran brothers dinta suka fita outing da yamma nan Yaya Muhammad shi yake driving car din Faisal da Saif kuwa suna back seat sai Jiddah a front seat.
"Suna kan titin WAFF ROAD, Yaya Muhammad yana driving da kyau Amma bai ankara ba yakusan banke mutum, bashiri yaci birki wanda kadan ya rage ya banketa, sai alokacin su Jiddah suka farga da abinda ya faru da sauri Muhammad ya fita don duba ko lafiya lau take.
" Sanye take da Atampha doguwar riga tayi daurin zarah buhari sai ta yafa veil babba asaman kanta dukdama baya ganin fuskar nata saboda ta tsugunna sannan ta cusa kanta a tsakankanin gwiwarta alamar ta sadakar ga kuma books dinta da bag dinta dasuka fadi gefe guda, " Muhammad ya tsugunna yace baiwar Allah bakiji ciwo ba ko?
"Ahankali Leemarh ta soma dago kai har ta sauke idanunta akan muhammad,
"Take Muhammad ya furta MashaAllah cen cikin throat dinshi ya kafeta da idanu, itama dai kallon shi takeyi har saida Jiddah da Saif suka fito sun dade suna kallon Muhammad kuma suna mishi magana amma dagashi har ita yarinyar babu wanda ke jinsu hakan yasa said yafara raira waka yana yi yana cewa "Yaya Muhammad ya fada shikenan", Ita dai Jiddah shuru tayi kawai tana kallon Yaya Muhammad, sai ta durkusa ta dafa Muhammad tace Yaya lafiya?
Firgigit yayi hade da kallon yan uwan nasa ya kuma dawo daga wata duniyar daya fada, itama Leemarh same abinda ya faru da ita kenan, tashi tayi tana kakkabe kayanta kafin ta durkusa ta dau books dinta tuni Muhammad ya daukko ya mika mata yana cewa hope bakiji ciwo ba ko?
Leemarh ta gyada kai tana sake kallon mutanen wajan, ahankali ta soma tafiya batareda tace musu komai ba, Muhammad yace  ko zaki zo muyi dropping dinki a gida?
Leemarh ta waiga tana kalloi nshi agaskiya dazasu sauketa da taji dadi Kam,saboda yau din ta gaji kuma at thesame time Mom ta kirata ta aiketa, ta girgiza kai tana cewa Noooo thank you!
Jiddah tace kada ki damu ba sace ki zamuyi ba (Jiddah ta tuno maganar da sukayi da Momma rannan) kizo mu sauke ki ta fada tana mata smiling.
"Leemarh tace okay thanks much to you all.
Muhammad ya shagala wajan kallon beauty hakan yasa Faisal cewa ku shiga muje, Jiddah ku zauna aback saet  kuda Saif.
"Jiddah tace okay"
Leemarh ta fada masu anguwan,kai tsaye suka fasa zuwa inda zasu kasancewar ba hanya daya bane Muhammad ya juya ya nufi gwamna road don dama sunsan anguwannin kaduna saboda duk sanda sukazo kullum sai sun fita outing.
Har kofar gida suka sauketa, Faisal yace yan mata nanne gidanku?
Leemarh tace Eh ahankali tana shirin fita suka hada ido da Muhammad ta mirror, tuni ta sauke kanta kasa ta fita da sauri tana cewa thank you, ta tafi ko waiwaye, Muhammad ko har tashige gida yana kallon ta ji yake kaman ya bita ciki, gaba daya yarinyar ta tafi da zuciyar shi.
Faisal ya daka masa duka a baya yana cewa man you mess up" zaka sa yarinya ta rainaka ai....ji yanda kake kallonta kaman zaka cinyeta"
Muhammad ya cusa hannunsa cikin lallausan gashin kan shi, yana cewa oohh boy am just carried away by her beauty, she is totally beautiful.
"Jiddah tace absolutely Yaya muhammad nikaina na yaba da kyawunta to tell you the truth ina haduwa da kyawawa a school But, I've never come across such a cute girl like her"
Saif yayi gyaran murya yana cewa toh yanzu zamu tafi ne ko muma zamu sauka mu bita cikin gidan ne?
Dariya sukayi gaba dayansu, suna cewa awwwww ashe akofar gidan mutane muke, Faisal yace mubar nan please.
Yawo suke tayi abinsu har karfe goma na dare sannan suka koma gida.
"Jiddah ta saba shiga cikin su duk da ita kadai ce macce a cikin su tun tasowarta, tana da cousins mata yaran kishiyar Ammi,But, Bata cika zuwa wajan su ba, suma ba wani janta a jiki sukeyi ba,  Sai Fatima shiyasa take bala'in son Fatima, some times har tausayi take bawa Momma saboda yadda ta taso cikin maza ita kadai macce, ita kadai take rayuwarta, amatsayinta na ya mace yakamata ta samu yan uwanta mata suyita abinsu tare Amma sai gashi ta taso cikin maza dukda sometimes Momma na hanata shiga cikin su sosai...
" Jiddah" ta raka su Ummie boys quarters dama an gyara ko ina, bata bar flat dinba sai karfe 11:30 shima Ummi ce ta ishe ta da surutu, dare yayi daughter kizo ki tafi ki kwanta, su Saif kuwa dama sunsan makwancinsu bangaren Faisal.
Dukda cewa sunyi hira sosai har bacci ya dauke su, shi kadai ne ya kasa rintsawa saboda ganinta dayake tayi dazaran ya rufe idanunshi, a zuciyar shi kuma da kwanyar shi maganganun Isma'il ne suketa damunshi, Hakika baisan he has gone too far ba da soyayyar Jiddah, Hakika baisan cewa zaman da sukeyi da kuma kulawan dayake bata da kallon kanwarsa daya tilo dayake mata duk zasu canja, bai taba tunanin duk zasu koma soyayyah ba, Lallai ya jima da sanin cewa zuciyar shi  ta amince da ita,sannan ya jima da sanin cewa zuciyarshi tayi wa Jiddah  kyakkawar karba to which Jiddah na shiga zuciyar ta kulle kofa ta tafi da key din shiyasa har yanzu yakasa kallon wata mace amatsayin budurwar dazaiyi soyayyah da ita,babu wacce yake qauna sai "JIDDAH"ya sanya ta aranshi over,yayi ajiyar zuciya hade da gyara kwanciyar shi ya koma hannunsa na dama, sannan ya bude idanuwanshi ya kafe wani hoto wanda yake manne jikin bangon dakin shi babban frame ne "JIDDAH" ce a hiton tana sanye da black abaya tayi rolling hannunta daya na saman kanta yayinda fuskarta ke dauke da make up wanda yai matukar amsar chocolate skin dinta, tana dariya kyawawan idanuwanta kuma suna kallon camera eye lashes dinta zara zara sukayi kaman an watsa masu ruwa....Lallai tayi kyau fiye da tunanin mai karatu.
Faisal yace aranshi, yaushe zaki zama tawa "JIDDAH" when will you be mine?
Ya dade yana saka abubuwa aranshi kafin daga bisani bacci mai nauyi ya dauke shi.
VOTE PLEASE

******************
JK 🕌to you all
Am so sorry for keeping you guys so long,naso nayi muku update tun Monday unfortunately phone dina ya samu problem... though dama nace friday zannayi muku update, tohm yau kam harda extra update zanyi muku.
Happy Reading

I need comment fans
Please read and share your thoughts!
Don't forget to press the tiny star below.

Continue Reading

You'll Also Like

14.2K 1.4K 86
" දන්නවද අභී..! එයා හරියට වැස්සක් වගේ...!" " වැස්සක් !?...'' '' ඔව් වැස්සක්...එයාගෙ ආදරෙත් හරියට වැස්සක් වගේ...කාලයක් මාව ඒ වැස්සෙන් තෙම්මලා....එයා ය...
22.2K 543 7
Yasmin Monroe signs up for Love Island 2024 looking to find her perfect match.
134K 8.7K 55
Kallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi
50.9K 6.6K 55
"ඒයි ඇටිකිච්ච ඔහොම ඉන්නවා" "නේත්‍ර, නේත්‍ර... මගේ නම නේත්‍ර" "මොකද උඹේ කට ඔච්චර සද්දෙ, මට ඔය වයසට වඩා උඩ පනින්න දඟලන ඇටි කිච්චන්ව පේන්න බෑ. ඒ නිසා මට...