page 8 of part 2

370 58 11
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCweMTaFag7ZSEaLUhajelHQ.

Wattpad @68billygaladanchi.

*Kindly subscribe to our YouTube channel and follow us on wattpad.*

*DAN BATURE Book 2*

*BILLY GALADANCHI*

*JINI YAFI RUWA KAURI✍️✍️✍️*

            *08*
Ringing na wayartane ya farkar da ita daga baccin daya soma fizgarta, cikeda kasala ta zaro wayar daga gefen bed side ta k'ura lambar dake kiranta ido, sabuwa lambace a wayar kana true caller yana nuna mata sunan Abdul D'an bature b'aro b'aro, cikin hanzari taso d'aga kiran amma kash wayan ya yanke mata,gauron numfashi ta sauke tana fatan cewar ba kizo yake mata ba, rik'e wayan tayi tana tunanin kotabi bayan kiran nasa daya yanke sega wani kiran ya kuma shigowa, da azama ta d'aga lokaci d'aya takai wayar a kunnenta

"Assalamu Alaikum" Abinda ta fad'a kenan cikin dakakkiyar murya Db ya ansa da "Wa'alaikissalam"  Ajiyan zuciyan data sauke harshima sanda ya jiyo ta

"kina lafiya" Jikintane yayi sanyi da yanayin yanda yake mata magana tace cikin rashin kuxari

"Lafiya lau" Jinjina kansa yayi tamkar tana ganinsa

"Mashaa Allah, how are you feeling now? kwantar da kanta tayi gefe d'aya

"Am getting much better Alhamdulillah"

"Kinci abinci kuwa?"

"Basu kawoba har yanzu"

"Su waye?" ya tambaya cikin d'anjin haushin abun

"Masu aikin gidan amma nasan idan mommy ta basu dasun kawo, dole seta bada zasu kawo kuma tun wuraren 11:am na mata waya akan inajin yunwa" Tsaki yaja

"Subhanallah haka ake jinya  to dama Daddy na yace yau zaki zo gidanmu, ba yanda zasuzo su barki da yunwa, ya dace mara lafiya ya kasance akwai me kulawa da shi, ina duk 'yan aikin gidan hope dai bake kad'ai bane a d'aki?  Murmushi me zafi tayi, aranta tace kaidai kaga mutum dan kawai kana ganina cikin dakiya kowane Lokaci bakasan me nake ciki ba

"Karka damu da wannan Yaa Abdul ainasamu sauk'i" ta furta muryanta yana rawa alamun tabbas kuka takeso tayi, goshinsa ya dafe kansa yana sara masa batare dayace komai ya datse kiran, befasan gariba karyazo ya b'ata, badan yasoba ya kwana biyu bashida labarin ta sunje sokoto ne shida Dad da Granny akan zancen auren da yayi, tun akan sophie ya dena sakaci akan macen aurensa, ko bayason Bilkisu ko wane zunubin ta aikatawa mahaliccinta indai ta tuba anwuce gun awurin sa, abu d'ayane baze iyaba shine kwanciyar aure da ita, yana k'yank'yamin mazinaci sama da komai, duk tashin sa a turai be hanashi zama jajirtacce kuma me rik'on addinin saba, bece ya aminta zinar tayi ba ya yadda fyad'en aka mata amma shin tana budurwarta haka ai yara akafi yiwa fyade ba manya ba, tana me akan me zata b'oye masa labarin ciki kuma? akalar motarsa ya juya zuwa wani restaurant data tab'a kaishi ya siya mata abinci sannan  ya naushi hanyar gidan dabashida tabbacin ze gane ko baze gane ba.

***************
    Da yaa khali ya fara cin karo a gate kuma tabbas khalil ya shaidasa, da fara'arsa ya k'ara gunsa ya bashi hannu suka gaisa sannan D'an bature yace dashi

"Amm Bilki fa? Juyawa yayi yana fad'in

"Muje na kaika gunta" Ata babban parlor suka ratsa zuwan saman har d'akin datake yakaishi, inda suka sameta a zaune da b'ingilalliyar rigan bacci, da alama ko wanka bata samu tayi ba, shigowan Khalil be sanya ta motsa ba amma ganin D'an bature atare dashi ya sanyata diriricewa ta shiga neman abun rufe jikinta, atake ta shiga lakube inda tayi karo da zanin wata atamfar momy da aka kawo mata sanda ta buk'aci hakan! rufe jikinta tayi sannan ta soma gayar da D'an bature be ansa taba ya nemi wuri a k'asa datake zaune rungume da tray  na abinci shima yayi zaman tamutela ya k'ura mata ido dik ta rame ta fad'a ainun tayi bak'i ma, khalil juyawa yayi yafita yaja musu k'ofar gaba d'aya

DAN BATUREWhere stories live. Discover now