page 5

498 77 2
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCweMTaFag7ZSEaLUhajelHQ.

Wattpad @68billygaladanchi.

*Kindly subscribe to our YouTube channel and follow us on wattpad.*

*DAN BATURE*

*BILLY GALADANCHI*

*NASO SANYA ALK'ALAMINA ACIKIN DUBBAN ALK'ALUMAN DASUKAYI KARAKAINI WURIN GIRMAMA RANAR HAUSA TA DUNIYA, SEDAI TSARIN MAHALICCI YA SHALLAKE NA DUKKANIN WANI K'ANK'ANUWAR HALITTA, NA JARABTU DA ABINDA YA DACE NAWA ALLAH GODIYA KASANCEWAR ABUN MAKARKARAR ZUNUBAI NE WATO CIWO, NAGODE ALLAH MAHALICCI DAYA K'ARENI DA LAFIYA YANZU.*

*BANHAU KAN TUDUNBA BARE NA ZAME, BAN D'AUKA DA ZAFIBA BARE NA K'ONE,BAN FITO FARAUTAR KOMAI BA BANDA LAHIRATA TA INGANTA,MENENE ZE DAMENI DA WAIWAYEN HAUSHI IRIN NA KAREN MAGUZAWA?, HAUSA TA HAIFEMU DA BAZARTA MUKE RAWA,BAZAMU FASA D'AGA ALK'ALAMINMU DAN RASHIN TADDAWA ME KAURI WURIN YIN AIKI DA HAUSAR MU BA, ME RUWANMA ZATAYI KAURI KOKUMA TA BIYA BUK'ATA A HAKAN.MUNA NAN DAI MUNA ZUBA IDO HAUSAR TA WADACEMU ALLAH KA IYA MANA, BAMA WAIWAYE INDA MUKA DOSA KURUN MUKE HARA KARKAYI TSAMMANIN ALK'ALAMIN CIKAKKIYAR BAHAUSHIYA YANA NUNI NE DA ABOKIN HALITTA, GABA GABA DAI HAUSA DA HAUSAWAN USUL ALLAH YA K'ARA D'AUKAKA HAUSAR MU.*

05

kallon juna sukayi bayan sun zauna a mota ta sauke nannauyan ajiyan zuciya, magana takeso tayi amma dik yanda tayi k'ok'arin murza labb'anta se harshenta yak'i bada had'in kai dan kuwa baya lank'wasuwa, lura da yanayin datake ciki ya sanya Lamir yace

"Base kince komai ba ranki ya dad'e na fahimci halin dakike ciki, nakuma san kina tunanin cewan akwai matsala zuwan wancen mutumin ko? Jinjina kanta tai alamun E kawai batare datayi magana ba, bataso had'uwar ta dashi ba, bataso sam ya gantaba, taso ace tayita aiwatar da abubuwan ta acikin sirri, a hankali ta baiwa motar wuta ta d'aga daga wurin datake ta daidaita akan babban titin ta balbala aguje!

Bature kuwa motar yabi da kallo shida me gadin sa,yana mamakin me yarinyar tazoyi gidansa, kanta yana mata ciwo yanaga, jini irin na bature ya sanya kwata kwata be cewa me gadin komai ba, azuwan babu ruwansa da abinda dik be shafe saba.

**************
            kallon sama tayi lokaci d'aya ta dafe goshinta da hannunta  d'aya ta ce

"Ohh God hadarine agarin har haka ban saniba? lallai ma nayi shirme, kanta k'arasa maganar ma ruwan ya soma sauka a hankali, waigawan dazatayi ta hango Abdul a zaune wurin da ake fitowa dasu domin shan iska shishi kad'ai, mamaki tayi domin ta sani k'a'idane ba'a barin dik wani mara lafiya wurin shak'atawa shishikad'ai, kallon ruwan ta kumayi yana sauka a hankali amma shi ko gezau beyiba hasalima lilon dayake kai yadena juyawa dashi ya k'urawa iya wuri d'aya ido yana kallo, takawa tayi a hankali har zuwa inda yake tace tana kallon sa, dukda a tsorace take tasan wasu masu irin lalurarsa bayan kurzar kansu hadda duka suke, gashi dama an sanar mata shi yana yakushin mutane da iya k'arfin sa

"Abdul ka tashi mune ciki ruwa yana sakkowa" kallon ta yayi yace

"To muje" tare da sakkowa daga saman lilon bayan ta rik'e masa igiyar" kallon sa tayi yanda yake tafiya, askin nan data masa seya dawo tamkar wani me hankali gashi cikin shiga ta alfarma kaman me kafiya ahaka

"Naga baka d'aga k'afa, ko baka tsoron ruwan sama ne?" kallon ta yayi hadda fara'arsa

"Yau kuma sophie ni kike tambaya akan ruwan sama, sanin kanki ne babu wani yanayi danafiso kamar wannan, bansan mesa ko yanzu kikeso intafi ciki ba, nafiso nayi wasa acikin ruwan sama,kafin kizo inata tunanin ki" kallon mamaki tayi masa wani zubin seya d'inga abu tamkar me hankali, koda yake rashin hankaline kam ambatar wata da sunan wata

"Ea kawai ina tsoron kayi zazzab'ine" dakatawa yayi ya kalleta

"Nida na tashi acikin ruwa, yaushe wani ruwa ze sanyani zazzab'i ya kikeyin abu ne tamkar baki sanni ba, niki barni nayi wasan ruwa" shiru tayi dan batasan me zatace masa ba, kawai se ruwan ya goce da k'arfi sosai, hannunsa taja amaimakon yabita su ruga seya tizgota ta fad'o jikinsa, acikin ruwan ta d'ago ta kallesa batako gani sosai shikuwa ya sakar mata murmushi

DAN BATUREWhere stories live. Discover now