page 12

438 69 8
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCweMTaFag7ZSEaLUhajelHQ.

Wattpad @68billygaladanchi.

*Kindly subscribe to our YouTube channel and follow us on wattpad.*

*DAN BATURE*

*BILLY GALADANCHI*

*JINI YAFI RUWA KAURI...*

*Never explain your self to anyone.Because the person who likes doesn't need it and the person who dislikes you won't believe it*

        
     

         *12*

Da azama Dad ya rik'o hannun sa

"Abdul don't be rude mana, calm down. I promise you everything is gonna be alright ok? Sauke hannunsa yayi tare da wata lafiyayyiyar ajiyar zuciya

"Dad these people are so mean wlh, kawai daga zuwa gunsu suna neman had'amu da masifa, wannan ma ai masiface" Zaunar dashi Dad yayi yace

"Your a man behave like one mana" shiru yayi shikuwa Hafeex yace

"Dad ka gaya musu nifa babu wata Lamimi take ko Laminde dazan aurah, kawai daga sama sesu had'amu da wasu kucakan mata, wad'an nan yaran ma se yaushe zasuyi auren? gaskia bazan iyaba" Baba kamalune ya kalle sa

"Kai Hafixu nine na zab'awa ubanka auren Tumba, sannan kaima nine zan zab'a maka mata, ubanka be gagareni ba kai bazaka gagareni, tsohon d'an duniya nake nan dakake ganina, bar ganin kai kamar wani d'an duniya ne naci ubanka a duniyanci, kuma ka sani auren nan bazan tab'a fasashi ba ko duniya duka zaku tara akaina, juma'a i war haka duk na aurar daku ga zab'in danawa ko wannenku" Murmushi Dad yae

"Baba kamalu sedai idan ba adalci akeso ayiba, kokuma idan ba zumunci akeso ayi na Allah da annabi ba, dan kuwa nine uban yaran nan, kuma daga kan Hafiz har safiyya babu wanda ban zab'awar abokin zama ba a matsayina na uba, dan haka kuwa bazan tab'a bari ku ha'intar mun da yara ba, Hafix dai 'yar gidan Yawale Dikko aminina na nan garin ze aura, Shikuwa D'an bature safiyya ze aure" zabura Baba mudi yayi

"Ba d'an bature ba d'an baturiya da jakar uba, zanga shegen daya isa ya hana auren da malam kamalu ya  shirya, babu shi, ada ka zuba mana iskanci iri iri mun k'yale ka a yanxu wlh baka isaba  d'an yarinya kawai" wani yawu me d'aci Daddy ya had'iya sabida zafin da maganar tayi masa amma seya kanne ya kalli Baba kamalu yace

"Baba, nifa na gama magana ta, angwaye kuma kowa nabashi b'angare d'aya a gidan kara, yaje ya zauna da amaryarsa idan lokaci yayi, na ware Naira miliyan goma sha biyar zan baku kuyiwa ko wacce acikin matayen kayan d'aki ku bata jari take sana'a acikin gida, mazajen su kuwa ko wanne zan bashi Naira miliyan uku uku yaje yaja jari, Baba kamalu da Baba Mudi zan baiwa ko wannenku miliyan goma goma idan amince da sharad'ina amma" Kallon juna sukayi

"Karka Rainawa kutane hankali, kana ambatar miliyan sekace naira goma goma?" Murmushi yayi

"Baba Mudi karkayi mamakin dan wlh abinda nake dashi, bekosan na rab'esaba dannayi wannan kyautar, kasan ance ita kainuwa dashene na Allah, duk wad'an nan abubuwan zanyisu ne kaibtsaye, idan kuka janye zancen auren su hafix da yaran dakuketa laftawa sunaye ni nama kasa rik'ewa, idanma baku janye dan kud'i ba kodan Allah ta k'arfin tsiya zan k'wace, dankuwa wlh bazaku takurawa yara da wadannan kazantar ba" dikda zagin daya musu haka suka shiga meeting a take suka kammala meeting d'in da idanuwansu kawai!
Gyaran zama Baba kamalu yayi

"To banda abinka Lawal dama mu koba zancen kud'i ai bawai zamu tilasta bane, munyi ne sabida a samu kyakyawan zumunci kuma inhar Hafiz ya auri 'yar wajen yawale shi d'inma ai zumuncinne me k'arfi dan kuwa yawale d'an uwane shima, to kuma bare sahiya da Audu na wajenka, wannan ai 'yar gidane me kankata koya kace Malam mudi" ya k'arashe maganar yana dariya yana kallon Baba mudi, shi d'inma washe baki yayi ya shiga surutai.

DAN BATUREWhere stories live. Discover now