page 15

405 91 10
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCweMTaFag7ZSEaLUhajelHQ.

Wattpad @68billygaladanchi.

*Kindly subscribe to our YouTube channel and follow us on wattpad.*

*DAN BATURE*

*BILLY GALADANCHI*

*JINI YAFI RUWA KAURI✍️✍️✍️*

*Taskar tsakar gida, shinko kin tab'a ziyartar wannan shahararren channel d'in me cikeda albarka da k'warewa wurin karanto muku litattafan hausa? idan baki tab'a zuwa ba kuwa ambarki abaya domin Malam Umar mai sanyi jajirtacce ne kuma gwarzo wurin garin ya nishad'antar daku ta hanyoyi masu d'inbin yawa, maza ku ziyarci wannan k'ayataccen channel domin samun abinda kuke nema.*

*Wannan shafin Tukwuicine agare ka Umar me sanyi, Allah ya k'ara d'aukaka*

*15*
Seda yad'anja fasali sannan yace

"Me kikeso nayine wai Dr? bayan ina ganin laifin kaina akan abinda na aikatawa Saffiyya yanzu kuma akan babynta ma so kike kacokam ki d'aura laifin akaina?" cikin k'araci tace

"Ea mana, laifin kane kam ka sanya jinjirar yarinya ta tashi acikin maraicin rashin uwa da rashin uba, ka fizgo mota ka nufo hanyar dabaka sani ba aguje kazo kayi accident kana tsammanin da ace yauka mutu Allah ze barka ne? k'ank'ance idansa yayi yana kallon ta yanzu kam idan nan ya k'ara rikid'ewa sosai yayi jajir

"To me kikeso nayine Dr.? ki tausayamun mana" Nisawa tayi ta sassauta kukanta da muryanta gaba d'aya

"Bantab'a tsammani cewan akwai abin tausayi haka ba arayuwa, bansan meye matsala ba seta rashin uwa! maraicina kuma ya samu kyakyawan tallafi awurin mahaifina da abokiyar zaman mahaifiya ta, bansan ba ita bace ta haifeni se shekaru uku data wuce shid'inma agun danginta naji, sun gaji sun gagara yimun kara su d'aukeni matsayin 'ya, tunda nake aduniya banji abinda ya tsayamun arai kamar labarin safiyya ba, ban tab'a ji inason mutum sama da yanda naji ina k'aunar marigayiya safiyya ba, ina ma wannan labarin daka bani mafarki nake? inamace labarine kawai na cikin litattafan zamani, inama ace movie nake kalla, kaicona banso ace a zahiri wannan abun ya faru ba bansoba" Ta k'arashe maganar cikin kuka me k'aramin sauti, sunfi mintuna uku babu wanda ya k'ara magana seda dan kanta ta tsahirta sannan ta d'ago tana me shafe fuskarta da hanky

"Allah ya kyauta na gaba, nizanje gida Abdul" kallon ta yayi cikin mamaki

"Mesa zaki tafi? ya tambaya yana kallonta ido cikin ido ita d'inma kallon sa takeyi dik ya fice mata aka

"Mesa bazan tafi ba? ina iyakar labarin kenan? Wasu yawu ya had'iya, ita kad'aice tasan gaskiyar meya faru bayagan marigayiya, taga laifin idan uwarta taji yaya zata d'aukesa? idan Dad yaji mezece masa? mezai gayawa mommy? yaya ze kalli idon granny? yaya Hafiz kuma fa, cikin takaici abubuwan sunaso su sake dawo masa su juyar masa da kansa

"Dr. am helpless, dunno what to do right now, please kije dani gidanku" kawar da kanta tayi batare da wani tunani ba tace dashi

"Tashi muje" Jikinsa ba k'wari ya mike ba komai ajikinsa se jallabiya, dik a takure yakejin kansa silipas dake gaban gadon ya zira yazo ya tsaya kusa da ita

"Inajin yunwa kuma" bata kulasaba tayi gaba yabi bayanta, k'unci takeji ji take tamkar ta rasa wani b'ari na jikinta, shi safiyya ke gayawa wasiyya wasiyyar itace kwance rad'am azuciyar ta, tanaso taga 'yar nan ta rungumeta ta gaya mata mahaifiyar ta tana gaisheta, ayau batada burin daya wuce taga wannan yarinyar rik'e hannunta, a yanda takeji idan zasu bata amanar yarinyar zata karb'a kuma duk namijin dabaze aureta da 'yartaba bazata tab'a yadda ta auresaba! haka sukaje mota ta bud'e da remote na motan suka runtuma ciki, motar ta kunna da remote ta zauna ta balbala AC sosai, kishingida tayi da sit na baya sannan ta lumshe idanta

DAN BATUREWhere stories live. Discover now