page 18

374 76 4
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCweMTaFag7ZSEaLUhajelHQ.

Wattpad @68billygaladanchi.

*Kindly subscribe to our YouTube channel and follow us on wattpad.*

*DAN BATURE*

*BILLY GALADANCHI*

*JINI YAFI RUWA KAURI✍️✍️✍️*

            *18*

Kiyi Hak'uri Mommyn Abdul, ni banida uwa, ban rayu da mahaifina ba akusa dani ba, bansan dad'in duniyar nan ba, son kaina kawai aka koyar dani, kud'i kawai aka nunamun, na soma fahimtar rayuwane bayan sauraren labarin da tarihin ahalin nan agun D'an bature, ban san tausayi ba, babu wanda ya koyar dani se d'an bature, bansan babu ba dan babu abinda na tab'a nema na rasa a duniyata se gatan iyaye, banida wani makusanci nikad'ai na rayu, ni mujiya ce bana zuwa wurin kowa haka zalika bame zuwa wurina kallon farko dana miki na hango mahaifiya a idonki, zanyi biyayya amma ki taimaka ki jib'anci lamarina, ki taimaka koda bazaki bari na kula da d'an bature ba ke ki kula dani, ki zama mamana, ki kalleni tamkar nice marigayiya Safiyya, kar kema kiyimun Fushi dan Allah" kalamanta ba k'aramin sanyayar da gwiwar mom sukayi ba, komawa tayi ta zauna tana me sauke tagwayen numfashi, seda ta rintse idanta sannan bud'esu tas a kanta takai hannunta asaman kan Bilkisu tace

"Na fahimci ke yarinyace da raunin dake cikin zuciyarki yafi na tsoho me iyalin dabashida abinda ze ciyar dasu, na soma fahimtar bakida tubalin jingina me k'wari, na fahimci anginaki ne kawai batareda tubali me inganci ba daga k'asa, na fahimci bakisan meye rayuwa ba, Bilkisu kin tab'a sakawa rayuwar ki xaki iya mutuwa yanzu? se a sannan ta d'ago ta kalli mommy cikin sanyin jiki ta furta

"Mommy aduniyar danake ciki da bana tunanin mutuwa ko kad'an  tunanina ya tsaya ne cak akan ba yanxu ba, lokacin mutuwata beyi ba tukunna, dududu shekaruna nawa, ban kawowa kaina mutuwa nan kusa ba, amma tunda Labarin mutuwar Safiyya da rayuwarta ya riskeni sena tabbatarwa kaina ko yanzu ko gobe ko anjima! na tabbatarwa kaina cewan zan iya mutuwa mom" Nisawa Mommy tayi

"To Bilkisu ki nutsu ki saurareni kiji abinda zan gaya miki, karki k'ara wa Dad zancen kulawa da D'an bature kedai ki kula dashi for the time bn, sannan kuma ki masa Biyayya idan yace ki koma gida kice masa to kawai, abu na gaba gobe zan zauna inaso nasan koke wacece, inaso nasan tarihinki ciki da waje, abinda ya faru tsakanin ki da Daddynku kuma zan basa hak'uri na tabbatar ze saurare ni kinji" Share k'wallan idanta tayi sannan muryanta yana rawa tace

"Mommy karki gaji dani, ina roqon alfarka ta k'arshe agareki yanzu" kallon tausayi tabita dashi "To inajinki Bilkisu" Wasu yawu ta had'iya

"Inaso ne ki taimaka ki barni na kwana a bayanki, inaso naji d'umin uwa akusa dani, Mommyn gidanmu kona rok'eta bata bari na sedai tace nayi gand'amemiya, inaso koso d'aya ne in d'and'ana dad'in kwanciya ajikin mahaifiya" Murmushi tayi sannannta rungumota jikinta

"Dan wannan Bakida matsala 'yata, Allah ya miki albarka kinji, yanzu kinga share hawayen jeki ki duba  d'an ubanki" Cikeda fara'a tace

"Ameen mamana, Ameen ya Allah nagode sosai da kika sanyamun albarka, wannan shine karo na farko dana tsinkayi wannan kalmar abakin mahaifiya, Ameen mommy" Ko Mommyn seda taji k'wallah tabbas rayuwarta madubi ne a baibai, bakowane ze fahimcetaba seya zauna da ita, tana da tabo fiyeda tunanin me tunani, tanada raunuka fiyeda awon me awo, tana rayuwane acikin duhu kwatankwacin wanda ya b'ata acikin duhuwar daji.

*************
     Zaman dirshan tayi a k'asa yayinda DB yake kwance akan k'aramin gado, tausayinsa takeji gashi yau an samu ma yayi magana, idansa a lumshe kamar ko yaushe ya furta

"Sophie ki kiramun Daddy jiri nakeji" da sauri ta zabura, har yanzu sophie ce aranshi? ta tambaya cikeda tausayin sa, durk'usawa tayi  agaban nasa takai hannu ta shafi sumar kansa

"Sannu yaa Abdul, Allah ya baka lafiya" Tana maganar lokaci d'aya tana share k'wallan daya silalo mata, mommy dake lab'e tana kallon su ta juya cikin kuka dankuwa idan ba hakan tayi ba kukane ze kwace mata sosai.
k'ura mata idanshi yayi sosai sekuma cen ya lumshe idan k'wallan shima daya taru masa ya silalo ta gefen idanshi hannu yakainya rik'o hannunta d'aya yace

"Banajin dad'in wannan duniyar, yanayin gidan da k'amshin gidan da komai ma yana tunamunne da marigayiya, har gizo takemun, dan Allah kimun alluran bacci kinji Bilkisu" Bayan hannunta taka ta share k'wallan daya zama hawaye me gudana akan kuncinta

"You have to br it kaji, kai musulmine Allah ze iya kashe ni yanzu seya k'ara maka wani zafin tunda tawakkali ya gagare ka" Bud'e idanta yayi fess

"_Wane magana kikeyi haka?"

"To kadena zancen allurar bacci, oya start reciting qur'an, tabbas inkayi hakan zaka samu salamar zuciya" Yana share k'walla yanzu kam yace

"To Kunnamun karatun alk'ura'anin daga wayar mom jeki karb'o" Yanaji ne tamkar ya runtuma ihu shikam.

    Mom Nu'aiym.

DAN BATUREWhere stories live. Discover now