Page 1

1.9K 156 7
                                    

*D'an Bature*


Yafi mintuna uku yana jiran tace wani abu amma seyaga sam ita wayan dake hannunta ma take dannawa, dabadan aikin kud'i yakewa matar nan ba daseya kwad'a mata mari wlh, yarinya k'arama na nema ta rainawa mutane hankali, seda ya cire rai akan zatayi magana sannan tace cikeda izza

"Kana tsammani zan hak'ura ne? kallonta yayi

"Ranki ya dad'e abinne ba nasara naga ai" kallonsa ta k'arayi

"Kai kake bada nasarar? ta wurgo masa wannan tambayar, kawar da kansa yae

"Naga kinata asaran kud'ad'enki ne ranki ya dad'e"

"Kud'in kane?" kallonta yanzu kam yayi

"Kiyi hak'uri"

"Get out from my car" Kallon nata yake har yanzu

"Hajiya dan Allah kiy....

"Get down this instant" Ta furta a fusace" B'alle murfin motar yayi ya fito ya tsaya yana kallonta, sauke Glass d'in motarta tayi ta kalleshi sosai

"Bana buk'atar sake ganin sunanka ko lambar wayarka yana yawo akan allon wayata daga yanzu am done with you" Wasu yawu ya had'iya masu d'aci sannan yace

"Dama bazan kuma kira ba" tsaki taja

"Better" iya abinda tace kenan ta fizgi motarta k'irar Lexus C350 fara k'al.

**************

     Tafi 2hours akan system d'in, ta zurfafa sosai akan binciken datake, idanta ya gaji jikinta ma ya soma gazawa, d'age madubin idanta tayi zuwa saman goshin ta tace

"Wash" tana yarfe hannayenta duka biyu, had'esu tayi ta lank'wasa yatsunta suka bada wani sauti raqaqas sannan ta mik'e ta mayarda kujerar mazauninta da kyau, wasu takardunta ta d'auka sannan tayi hanyar waje, sanye ajikinta lapcoat ce fara agaban rigar ata jikin aljihun an rubuta Dr.B Galadanchi ., har yanzu madubin idanta yana saman goshin ta kallo d'aya zakawa Dr. kasan  cewar lallai agajiye tale... Ta jima sosai tana kallon patient d'in nata dake zubar da k'walla batare daya nuna yasan mutum ya shigo bama a d'akin.... hannunta takai ta dafi goshinta sannan taja kujera ta zauna kusa dashi tana fuskantar sa

"Abdul" Ta kira sunan idanta a kansa, beko juyo ya kalleta ba, saukar da kanta tayii k'asa na kusan mintuna biyu kafin daga bisani ta nisa ta kallesa

"Haba Abdul? menene kake shirin aikatawa rayuwar ka haka? akan mutuwa Abdul? bazakayi tawakkali ba, wannan abin da kake bashida banbanci da jayayya akan hukuncin Allah abinda am sure bakada ikon  sauyawa dan yarigada ya faru and its God will" se yanxu ya kalleta

"Tawakkali? Ya ambata cikin sigar tambaya, sekuma ya soma irgen 'yan yatsun sa "tawakalli" ya dinga ambata yana ci gaba da irgawa da yatsunta kurun kuma seya tintsire da dariya

"Mutuwa waya mutu? kece kika mutu? ko kuma nine? E?....... kallon takaici ta masa ta mik'e kawai ta juya tabar d'akin zuciyar ta a karye, tana shiga office d'inta ta zaro wayarta a aljihunta sannan ta latsa kiran wata lamba... Daga d'aya b'arin akace

"Dr. B Galadanchi How may i help you"

"Good Afternoon sir" Gyaran tie Dr.  d'insa yayi zuwa sassautawa ya kishingida akan kujera sannan yace

"How are you?

"Am fine sir" shiru tayi yace

"Ehm" ya fada alamun yana saurarenta

"Sir its a false information, patient namu bekosan da wannan maganar ba sam, he didn't react @ all" Nisawa yayi

"Fine, u keep on searching" dafe kanta tayi

"But sir"  sekuma tayi shiru ta kasa magana

"Karki wani dami kanki Dr. komai zezo da sauki amma se an daure

"Nagode sir" iya abinda ta fad'a kenan ta datse kiran.

Bak'in cikine ya sanya ta zubar da k'wallah har ranta ta gaji!

"Harse yausje wannan abun ze k'are? ta tambayi kanta ganin ba wata mafita ya sanya ta tattare duk wasu komatsanta tabar office d'in.

****************
     D'ayan hannunta yana sama strng motar yayin da d'aya yake akan wayarta, kaman kullum yauma da gudun fanfalak'i take tuk'in, batama jin tsoron yanda take gudu ga waya kuma a hannunta, k'uuuuu taja wani wawan burki saka makon bugun abu datayi, jin motar ta tsaya ya sanya ta bud'e idanta data runtse, yau Jeep ce a hannunta tanada k'arafa a gaba, sedai kuma motar data daka k'arama ce, bawai a kud'i ba A a adai girma, sabida  Accord ce 2018 sabuwa dal itad'inma fara k'al kamar tata, wanda ta biganwa mota matsawa yayi ya parka a gefe yayinda itama taja gefe tayi parking amma bata fito ba tayi zaune tana taunar cewing cum dake bakin ta. Dattijon dake bayan motar rik'e da jarida a hannu yana dubawa mak'ale da siririn farin madubi a idanshi ne ya d'ago ya kali matuk'in motar

"Hey what's happening? kallon sa drivern yayi

"Sir macece ta dakemu kuma batada niyyan fitowa ta bada hak'uri" cikin d'age kafad'u alamar ko in kula yace

"Then call the police" kallon sa drivern yayi

"Sir" D'agowa yayi suka had'a ido

"Do as i say" Shiru drivern yayi ya fito daga motar yana danna Lambar dayakeda yak'inin da police ce a wannan yankin, ganin yarinyar ta gama shan k'amshin ta sannan ta fito a motar ta ta duba gaban motar tana yunk'urin komawa ya sanya yasha gabanta

"Baiwar Allah akan me zaki mana b'arna ki mana asara daga sama sannan bazaki iya bada hak'uri ba" Da mamaki ta kallesa sannan ta kauce masa ba tare datayi magana ba ta shiga kotarta ta zauna seda ta bankawa motar key sannan ta balbala AC kana ta bud'e block compartment nata ta janyo rapar "yan dubu dubu guda biyu, ta zuge glass ta wurga masa

"Asarar da kake magana ni banma santa ba, sannan kuma ga kud'i nan kaje kayi gyaran motarka, karka cikani da hayaniya" Waigawa tayi acikin motar ta d'akko card d'inta, shi d'inma wurga masa tayi

"Irin wannan motar dakake tak'ama da ita agidanmu akwai sama da goman ta, ni tamun k'arama a hawa ma idan kud'in be isheka ba ko kuma sabuwa kake so ga card d'ina u call me" tana gama fad'ar hakan ta d'auke hannu ta rab'eshi ta figi motar ta tabar wurin....... Fitowa dattijon da komai ya faru a idanshi yayi ya kalli direban nasa yace

"Mekenan haka? kallon sa yayi

"Sir wata k'ank'anuwar yarinyace fa ta gantsare take mun rashin kunya.......Gaya masa komai yayi dattijon yayi dariya sannan yace

"Fine then i need a new car, so we call later in the day, ka tattare mata kud'inta" Sanin halin ogansa ya sanya ya tattare kud'in dan tabbas tunda ta tab'o *Bature* ta tab'owa kanta fitina!

*Billy Galadanchi (Mom Nu'aiym)*

DAN BATUREWhere stories live. Discover now