Page 2

686 101 7
                                    

*DAN BATURE*

*BILLY GALADANCHI*

*Aminci Abune me muhimmanci, amma abu ne dayafi hatsari arayuwar d'an adam, shin kunsan cewar a yanzu babu aminci a duniyar mu? kiyaye wannan, Nasiha ce.*

                *O2*
Kai tsaye gidan mai Billy ta nufa sabida taga tankin nata yaje half tank idan da har tanada iko da babu abinda ze sanya mai a motarta yadinga raguwa, k'aranta ne agareta zuwa gidan mai Barau yasan wannan tarasa dalilin daya sanya yake tsananin k'aunar sata magana, tasha fad'a masa bata so take ganin babu mai a motocin sabida kowane lokaci zab'ar motar hawa take agidan to yaya kuma zeyi sake?
    Hawa layin tayi wanda sanda tazo ba kowa, Haka wanda ke kan mesar yayita kallon ta yana magana amma ta mayar da hankalin ta akan wayarta ko kallon sa batayi ba, hannunsa yakai yayi mata knocking na glass d'in motar ta amma ko gezau batako d'ago ta kalleshi ba, ga motoci yanzu abayanta da dama, fusata yayi yahau banbami shi kuwa

"Kedanla tafi cen wulak'antacci ya, kinzo sekace wata sarki matsiya ciya anata magana kinyi zaune kin shanye mutane abayanki, ni ki matsa na baiwa mutane mai idan bazaki saya ba" Aikin b'ur inji tusa dan batama san yana yi ba hasalima wayarta take dannawa cikin tsanaki tanashan Ac harga Allah hankalinta yana akan wayar tama manta inda take, wani me mashin ne ya kasa hak'uri ya zo ya dingawa glass d'in dukan hauka, jin hayaniyar yayi yawa ya sanya ta d'ago ta kallesa, Ya salam ta furta dan se a sannan ma ta tuna inda take, waigawa tayi taga ko ina mutane ancika wurin ammata caa kowa nata fad'a, murmushi tayi ta sanya giya tanemi barin wurin batare data sauke glass bama, wani d'an taurin kaine yabi bayanta da mota wannan haushin baze kwashe saba shishi kad'ai seyaga 'yar gidan uban waye ita d'in....... luran da tayi ana binta a baya ya bata daman sauka daga kan titin ta gangara k'asa, parking tayi sannan tai unlocking motar ta ta zauna tana jiran sa don shid'inma taga yayi parking abayanta, fitowa yayi yanata masifa amma seyaga batako kalle saba, langwab'ar da kansa yayi cikeda mamaki ya matsa ya danna mata knock, seda ta gama shan k'amshinta sannan ta d'ago ta kallesa zuge glass tayi sukayi ido biyu dashi, shida kansa k'warjini ta masa amma seya dake irin ta maza yace

"Me kike tunanin kinyi haka? wulak'anta jama'a yaya zakizo kiyi mintuna sama da talatin bakya gaba bakya baya mu baki bari mun siya munje neman abinci ba ke kuma kin tsaya dankinzo a k'atuwar mota" Nannauyan ajiyan zuciya ta sauke

"Kayi hakuri kaji na b'ata maka lokaci ko, hankalinane baya gun kuma banso nayi rigima da kowa shisa nayi tafiya ta, bazanga laifin kaba laifin na wanda yabani aikin zuwa gidan maine" Shiru yayi yana nazarin kalamanta ta janyo rafar en dari biyar biyar tae ta mik'o masa ta glass, be k'arb'a ta yamutsa fuska

"ka karb'a mana inasone na biyaka asaran lokacinka dana maka ko bakaso? k'ank'ance idansa sosai yayi

"Mene keni kina tunanin kina da abinda zaki bani? bari kiji dake da kafatanin danginki d'an abinda kuka tara be isa ku biyani asaran lokacina da kikamun ba, ba'a ajiye abinda aduniyar nan ze maye mun gurbin lokacina da kika b'ata a d'azu dama yanzu danake wannan maganar dake, wacce batasan kanta ba kawai" yana kaiwa nan ya juya kawai ita kuwa mutuwar tsaye tayi, tunda take ba'a tab'a irin wulak'ancin daya mata ba, amma laifin na Barau xekoji ubansa!.....ta figi mota fuuuu zuwa asibiti dama centa nufa, yau kam 'yan matan ransu babu dad'i suka isa gun aikin.

  K'urawa Abdul ido tayi batako k'iftawa yanda ya takure agu d'aya yana wani karkarwa sekace wanda akewa wankan k'ank'ara, ga alama a tsorace yake tafa kula cewan Abdul dik sanda ya ganta k'ara gigicewa yake

"Abdul" ta furta cikin damuwa, k'ara matsewa yayi da bango jikinsa yana masa rawa wanda hakan ya sanya ta jingina bayanta jikin kujerar datake kai tana lumshe idanta, metake masa da baya sone? mesa ya tsani ganinta har haka? tayaya zata yi aikinta a kansa idan har baya mata magana, tarasa gano dalilin haukan sa batada wani clue akai, mik'ewa yanzu kam tayi, tabar d'akin batare data sake masa magana ba, kai tsaye office nata ta nufa, zama tae bayan ta bude ta shiga ta lalubo Land line na office ta danna kira wani office d'in

"Ka sameni a office" tana gama fad'an hakan ta kashe wayan ta kishingida tana tunanin inda zataga mutumin dayaci zarafinta d'azu ta rama, zuciyarta tana mata zafi akan abinda ya bata, koda yake idan ma bata ganshi ba akan barau zata sauke sabida shine sila.  

  kallonta mutumin data kira yayi bayan an masa umarnin shigowa ya durk'usa

"Ranki ya dad'e gani" seda tajan fasali  sannan tace

" Patient na room 13, inason duk wani muhimmin abu da aka samu acikin motarsa, harda plate number d'insa" jikinsa yana rawa yace

"Hajiya dik wasu muhimman abubuwa Dr. Ashraf ya k'arb'a tun tuni" yamutsa fuskar ta tayi

"What? ta ambata cikin k'araji "Kanka d'aya kuwa? akan me zaka bashi? patient d'insa ne kome? Jikinsa har rawa yake yace

"Dr. aicewa yayi kece kikace abashi komai daya shafi patient d'in, ina Abdurrahman kike magana? Mik'ewa tayi ranta a matuk'ar b'ace ta fita ta nufi office d'insa, setayi rashin sa'a Call yakeyi tsaki taja tabar office d'in, daga bisani asibitin gaba d'aya. Ta rasa me Dr. Ashraf yake nufi da ita arayuwa komai take seya nuna mata yafita iyawa akan wannan patient d'inma shiga gaban ta yakeso yayi a bincike ba damuwa da daren dayake call zata fito ta sameshi.

**************
     zaune take akan kujerar da aka tanada domin shak'atawa a farfajiyar gidansu, a k'ark'ashin wata runfar bunu ta zamani, k'afafuwanta a hard'e mik'e samb'al akan center table dake wurin, hannunta rik'e da glass cup d'ayan hannunta kuwa laptop dake kan cinyar ta take aiki dashi, tun d'azu wayanta dake silent take wurgo da haske amma batabi ta kai ba se yanzu taji tana ra'ayin dubawa, sabuwar lamba ce wanan batasan kota waye ba anya zama ta d'aga kuwa? gajeran tsaki tayi sannan ta mik'a hannunta ta d'auki wayar inda kafin takai ga d'aga kiran ya zama msd call, lumshe idanta tayi ganin sak'on dake sama

"Sunana Bature, and i need a new car"  Murmushi tayi sabida ta shaida shi, replying message nashi tayi da address d'inta a ranta tace kanka yana maka ciwo, kazo zamu biyaka hadda k'ari.....

Mom Nu'aiym👌🏻

DAN BATUREWhere stories live. Discover now