TSAIKO (The Wait) CHAPTER SEVEN

10 1 0
                                    

#The igbo girl

Da isar sa garin owerri ya shiga cikin university din domin karasa cike2 sannan kuma da samun accomodation, bashi ya kammala ba se bayan maghrib a lokacin har gidan da ze zauna an kaishi ya gani anan cikin staff qaurters na makarantar.
Gidan ba wani me girma bane yana cikin jerin na junior clarks duk da kasancewar sa lakcara la'akari da cewa zuwa yayi ze tafi shi yasa be wani damu ba ya karba.
Bayan ya dan kintsa inda ze zauna ya fito domin samawa kansa abinda ze ci rabonsa da abinci tun azahar ya ayyana haka yana me shafa cikinsa. Fitowar sa ke da wuya yaji an rungume shi ta baya sannan an shiga jan sa don komawa cikin gidan sa cike, da firgici yake ta karanto duk addu'ar da tazo masa baki da zuci, gaba daya kakkarwa yaji wanda ya rungumeshi ya nayi hade da nishi me nuna alamun ya ci gudu, ganin an sake shi ya juyo cikin sauri don ganin waye
a durkushe ya ganta ta hade hannayenta ta tana rokonshi cikin muryar kuka please help me they are going to Kill me pleaseee ta ja kalmar yana tsaye a inda yake be motsa ba saboda be yarda da ita ba gani yake kamar hadin baki ne don gata kyakkyawa fara sol da ita kuma yana jin labarin mutanen kudu idan zasu cutar da kai babu irin dabarar da ba sa yi.

Oga We have search every where she no dey yaji wasu mutane suna fada daga bayan windown shi wanda aka kira da Oga ya ce search am well ooo We must Kill her today, Oga!! Wani a cikin su ya kira da karfi yana me cewa the wires here are broken she must have go through it lets follow her fast cike da taratsi suka fara maganganu da yaren igbo wanda hadarin su ke bayyane a cikin muryoyinsu su da haka suka kara gaba don neman ta.

Ajiyar zuciya muhammad ya saki hade da tsoro ya juyo domin kallon yarinyar ganin ta yayi rungume da wata jaka ta goyo tana ta kuka dan zama yayi daga gefen ta yace what is your name dago kan ta tayi hade da zaro Jajayen idanunta tana me kallon sa tace elizabeth why are they following you? Tace they were asked to Kill me, by who? By my uncles se ta kara rushe wa da kuka tana ta sheshheka ya ce mata stop crying i will help you,kanta ta girgiza ta ce masa indai bata bar garinnan ba to lallai ne za su nemo ta su kashe ta . Dan shiru yayi yana tunanin tsaka me wuyar da yake ciki kuma ya za'a yi ya temake ta.
Cikinsa ne yayi kara ya tuno da cewa yunwa fa yake ji ya kalleta ta hade da cewa let me go and get something to eat ta daga masa kanta ya ce mata ze rufe gidan kar tayi motsi me karfi kuma kar ta bude da mukulli a hannunshi ze bude ne in ya dawo tace masa thank you, yayi mata murmushi yana me tafiya.

A haka su na zaune tare da elizabeth har ya gama watannin sa ya fara shirin komawa gidah kuma duk tsawon zaman su be taba tambayar ta tarihin ta ba sannan a dan cikin zaman da sukai ya kamu da tsananin sonta do min itace kalar matar da yake kauna ya yi kokarin kare kansa daga sabawa mahaliccinsa be yi wani abu da ze kaucewa hanya ba duk da yasan ba musulma bace idan ya neme ta baza ta hana shi ba, amma ai shi son da yake mata yana fatan ya aure ta ne.

A cikin week dinnan zan koma garinmu , muhammad ya fada yana kallon elizabeth, tace to ni ya zaka yi dani mehet yace se ki koma gida mana ai yanzu nasan sun hakura da nemanki, ta ce no basu hakura ba saboda abinda suke nema yana gurina nasan dole kashe ni za suyi ko da na basu take me With you pleaseee ta yi pleading!! Dama abinda yake so ta fada kenan ya fi son ta nuna son kasancewa dashi ba tare da ya furta mata ba, ya ce how am married With three kids and am a hausa also a muslim while you are not my family will not accept you.
I can Stay With you for Your sake no matter what the situation is just marry me and take me away please ta fada hade da kuka.
Allah ya sani yana son ta amma yasan ze sha wahala kafin mahaifiyar sa ta yarda da ita, se dai baze iya barinta ba auren nasu dai shine mafita.

I will marry you but first i have to know who you are.
Kamar yadda ka sani sunana elizabeth ni igbo ce babana ne sarkin garinmu ina da yaya guda daya igbo name dina shine Adaeze ma'ana princess, kafin babana ya hau Sarauta shi dan sarki ne kuma yana da yen uwa wadanda ba uwarsu daya ba shi kadai mamanshi ta haifa kafin ta rasu, se ya kasance duk sun tsane shi.
Allah ya yiwa babana nasibi duk da baban shi sarki ne amma shi yana neman na kansa a haka har ya samu hanya ya fara zuwa dubai don harkar gwal su ke yi da diamond ya tara arziki me yawa har yafi mahaifin shi ma sosai yazo yayi aure itama mamata yer sarki ce suka zauna a dubai har aka haifi yayana nima aka haife ni duk a dubai ana haka kakana ya rasu muka taho nigeria don yin jana'izar sa aka binne shi da zuwan babana yan king emirate suka ce shi zasu nada sarkin su ganin yana da arziki.
ya ce shi baya so suka dage dole se da ya karba a take anan yan uwanshi suka tunzura suka ce se sun kashe shi sune ajalinsa a lokacin yayana ya gama university nima ina level three. ya wakilta shi a harkar companyn high jewelries dake dubai muka koma ni dashi don karasa karatuna muka bar iyayen mu a nigeria a haka har muka yi shekaru a can na gama karatu ni ma na fara aiki a companyn bayan wasu shekaru muka taho nigeria don ganin gidah.

Ranar da muka zo nasan babana hankalinshi a tashe yake don naga yana ta zarya ya kira lawyers dinshi suka zo ya bamu takardun kadarorin sa muka saka hannu ni da yayana ma'ana ya bar mana mu biyu ya danka min takardun yace tunda ni zan riga komawa to na tafi dasu saboda yayana se an daura masa aure ze koma. Takardun sune a cikin jakarcan da na zo da ita kuma itace dalilin biyo ni za'a kashe ni saboda dukiya. Kuma yen uwan babana ne suka haye su a ranar suka kashe babana da mamana da yayana ni kuma na samu kubuta ta dalilin babban bawan babana har na tsira. Nasan har yanzu basu dena nema na ba don dukiyar da suke yiwa duk tana hannu na
Kaji labarina..

Muhammad ya jinjina kanshi hade da cewa zan aureki amma ya za'ayi mubar garinnan ta ce zan saka abaya da nikaf i will dress like Arabs se mu tafi. Bayan sun tsaida shawara ya kuma samo mata kayan suka yi shirin tafiya kano.

Sun sauka a kano direct ya tafi gidan iyayen su da ita da kyar ya shawo kan inna sa'ade har ta yarda ze aure ta kannen mahaifin shi kuwa duk da basu yi na'am da elizabeth ba amma sun yi shiru kowa na gudun ya soki auren ya dena samun ihsani daga muhammad gashi kuma sunji cewar itama elizabeth tana da kudi sosai a takaice dai arziki ne ze kara habaka kuma samuwar su ne. Anan gidan aka samu wani ya zame mata waliyyi aka daura auren duk suna me tausayin Maryam baiwar Allah don sun ga irin kallon soyayyar da muhammad yake wa kedarar wanda baya wa yer su shi.
Bayan an daura auren ne ya tafi da ita gidan sa Maryam  kawai taga an taho mata da amarya tayi hakuri ba tare da ta nuna Komai ba ta karbi elizabeth hannu biyu itama amarya ta rike ta amana saboda dama ita tana son mutane sannan bata da hayaniya,

Bayan shekaru uku da auren su ta samu ta shawo kan muhammad don su koma dubai ta cigaba da kula da companyn su ya yarda suka koma dubai din harda Maryam a lokacin elizabeth tana da cikin khalid.
ya dawo da su inna sa'ade da baba hajara gidan sa na nan janbulo tare da wasu daga cikin yen uwa.
Khadija kanwarsa ce ta haihu amma Allah yayi mata rasuwa ta haihu dan ta namiji rikon yayen harda jaririn se ya dawo hannun su baba hajara da inna sa'ade elizabeth tayi kuka don jinin su ya hadu khadijatu dan da ta haifa aka saka masa suna kamal bayan wata bakwai elizabeth ma ta haifi dan ta me suna khalid.

Shekarar khalid biyar suka taho ganin gidah sam baya jin hausa sosai saboda elizabeth da igbo take masa magana ga babansa kuma ba ya zama, a wurin Maryam kawai yake jin hausa ita ma kuma ba zama take ba dan tana karatu ya yen ta ma su uku duk karatu suke saboda haka se ya zama baya jin hausa sosai kuma gashi yayo farin babarshi don farin shi har daukar ido yake.
Suna dawowa khalid ya ga kamal yana sonsa ya samu aboki itama kuma elizabeth ta ce taga da dashi zata koma. Da zasu tafi kuwa suka tafi da kamal dubai shi ma ya zama dan gidah, aka saka shi a makarantarsu khalid, a haka suka taso a tare se dai halayyar su ta bambanta don shi khalid bashi da magana sannan bashi da ibada ga shan giya be dauki musulunci da mahimmanci ba (a inda alhaji muhammad yayi sakaci kenan be sa ido akan tarbiyar tilon danshi ba da addinin shi)

Dukiyar su ta habaka don Alhaji muhammad ya zama hamshakin me kudi sun bude kamfanoni da dama wanda anan ne kamal ya bada shawarar su bude reshe anan nigeria se su dawo su kula dashi.
Khalid dakyar ya dawo saboda ya ce ba'a holewa a nigeria amma duk da halayen shi baya neman mata basa cikin tsarin shi saboda shi ya fi bawa kudi da lokaci mahimmanci a rayuwa, yana cewa idan ka tsaya kula mata to zasu bata maka lokaci ne amma idan ka tara kudi matan da kansu zasu biyo ka kuma yayi alkawarin matar da ze aura se ta zama hadaddiya kuma first class amma bazai auri duk wacce ta nuna masa soyayya ba se dai wacce ya gani yana so.
Khalid ga masifa, ga rashin ganin girman mutane shi dai a rayuwarsa neman kudi kawai, ya na kuma bawa lokaci mahimmanci gani yake kamar in kana da kudi to Komai zaka samu..

Wannan shi ne labarin khalid muhammad diso /boss

TSAIKO (The Wait) Where stories live. Discover now