Tahowa sukai tana gaba yana binta a baya, Har suka iso falo, Sanar da Hajiya sukai yace Zasu dan fita Hajara zata rakashi, A ran Hajiya tace anya ba lauje cikin nadi?

"Mota ya tada Hajara ta shiga, fara tafiya sukai seda Sukadanyi nesa da gida Haidar yace kinsan meyasa na fito tare dake?

    "Tace 'a'a bansaniba

yace kin gama mum komai arayuwa ba karamin Dadi naji ba, Yanzu me kkeso nasai miki?

   Tace bakomai nima na temake kaina ne saboda akwai wanda nakeso kuma munyi alkawarin aure dashi, kaga Idan nai haka ban kyautamai ba,

Haidar yace Gaskiya ne, Yanzu me kkeso nasai miki? Naji Hajiya tace cikin satin nan Zaki koma gida ko? Tace eh Hakane

Ni Abunda nakeso kasaimun shine Waya, Ko nokia ne na dinga gaisawa da kawaye na, da gogayen riguna da takalma nima in zama yar gayu

Murmushi yai yace To angama kanwata

Shaguna wayoyi yaje yasai mata harda sim, sannan yai mata racharging Wayarta na 1000, murna taji sosai sannan ya biya yasai mata kayayaki masu kyau da takalma da jaka sannan suka dawo gida 

Suna dawowa gida cikin zumudi ta nunawa Hajiya kayyyakin harda wayar da yasai mata

Hajiya tace masha Allah a tsofe lafiya

shiga daki tai, ta lalabo inda tasa lambar saurayinta Ta kawo wa Haidar tace dan Allah kasamun lambar nan

Yace ok lambar waye? Rufe ido tai tace na saurainane, Se kuma yadan ji ba dadi

Sa mata yai ta shiga daki, tanaya kira yanata ringing ba'a dauka ba

Se chan anjuma yaga kiran dan haka yai mata flashing ta kira

Cikin dok'i ta fara magana tace Nine Hajara

Yace Ashe zansake jin muryanki, Tace Eh

Nan suka fara hira har ya fada mata yazo garin da take yana aiki, Tamai kwatancen gidan da take yace zaizo

Aikuwa tamai, Chan yamma sai gashi yazo, hada baki Da Haidar tayi dan budirin nan Hajiya sam bata sani ba

Ya haidar takira yazo suka gaisa, tace ga wanda zan aura nan

Haidar yace Masha Allah, Ba laifi yanada kyau dan dai kawai besama waje bane

Saurayin Hajara yace har zansake budurwa nace bari nazo birni nai kudi kar aimun irin yanda kikaimun

Dariya tai tace aa, Har yanzu ina sonka ai,

Hira sukai sosai da Zai tafi ta kira Haidar sukai Sallama,

Haidar ya bashi kudi me yawa, Yace duk abun da yake bukata yadinga sanar dashi, kuma yamai alkawarin zai dauke masu komai na auren tun daga akwati har kayan daki har ma gidan da zasu zauna, shidai kawai ua rigemai kanwarshi da Amana,

Saurayin Hajara yace Kai amma munji dadi sosai wallahi, Allah ya kara girma da arziki

Haidar yace Ameen

Saurayinta ya tafi, su kuma suka shugo gida tare, Hajiya na kallansu ta window tace anya kuwa

Hajara dadi taji sosai tace Allah Sarki, Haidar ashe kanada sauqin kai
Murmushi yai bayan Saurayinta din ya tafi yace karkiji komai, Saboda ba karamin Temakamun kikai ba Wallahi

Tace Bakomai Ya haidar

Adan kwanakin nan sun shaku sosai, Ya zama tankar yayanta

Shi kuna se a time din Haidar yaji yanason hajara, Saboda tayi kyau jikinta komai ya fito ta zama yan mata

Saurayinta kuma gaba ta kaishi zuwan Fauxeey birni ai arziki ne,

Haidar kuwa kullun seya sa mata card din 500 ta Kira yan uwanta da abokan Arziki, amma ya gargadeta da karta sake ta fadawa ummanta abunda yafaru sedai kawai su ganta Kwasam tace toh

***
"Haidar ne ya shugo dakin mum dinshi, yasameta azaune suna waya da kannanshi na school seda suka gama ta kalleshi tace Amma naga kamar Kanason Hajara ko? Aranashi yace Tab, Duk siyasane dukda yanasonta dan ba karamin jihadi tai ba amma Sam bazai iya auranta bane saboda bata waye ba,

Shuru yai mum dinshi tace ba magana nake maka ba?

Yace" Mum nayi kokarin in fahimtar da ita ina sonta, Ko tsananin da kikaga ina mata farko farko, bansone ta rainani

Se rannan kawai tacemun bazata aureniba, bata sona

Hajiya tace" Eh Abunda tacemun kenan, Amma damuwata kadai shine yanzu da wani ido Mamanta zata kalleni nida nace zan hadata aure dakai

Haidar yai murmushi yace hajiya ba damuwa bane, Ni da kaina zan kaita har gida basai kinje ba, I'll explain everything to her,

Hajiya taji dadi sosai tace Allah yasa haka yafi Alheri yace Ameen, Dadi yaji ya shugo daki yace Yessss sannan ya kira Ahmad yake bashi labari

Ahmad yace kagani, Koma inkabi ahankali zaizo da sauqi yanzu bagashi an wuce wajen ba? Haidar yace gaskiya ne abokina

Haidar yace ka kintsa ran Saturday zaka rakani mukaita gida, Ahmad yace bakada da matsala Allah yakaimu, yace Ameen.....

Fauxeey zaune take tai tagumi ta rasa meke mata dadi, kiran Boyayyen masoyinta ta sakeyi nan ma taji shuru,

Wayar taqi shiga, Kiran Number farida kawarta tai shima still yaqi shiga, Yau na shiga uku tace who will help me,

   Ga dare yayi Kiran numbern kanwarta ummie tai tace Kicewa Mamma Yau aiki ya rikemu sosai, Zan kwana a wajen aiki, gobe zan dawo inshaa Allah

Ummiey tace Ok Allah yakaimu zan fada mata tace ok,

Jin alamun shugowar bobo tai ta kashe wayarta a hankali, ta boye ta shige toilet da sauri

Alwala tai tazo ta ganshi a zaune, Ko A batacemai ba ta tada sallarta

Seda ta idar tai addu'ointa da yake ta haddace azkar din safe da yamma akanta

Abinci ya kawo mata da Snacks da kayan kwadayi yace gashinan ki kula da kanki

Ya juya zai fita tace Allah ya isah

Allah ya sakamun,

Waigowa yai ya Kalleta yace Ke kikasani, Mind you yau sauran kwana 2 ko 3 kiyi tinani ki zaba ma kanki abunda yafi dacewa dake..

Tace ba tinanin da zanyi duk abunda kaga yadace Dani shi zakai, Nida Allah na dogara

Yace hakane.

Amma ba abun dayafi dacewa dake illa in kasheki bayan nagama samun abunda nakeso

Dan bazan kashi kiba ba tare da naji ni'imar da Allah yai miki ba, ke inason kisan Cewa inason naji yanda kike ne da har zaki dingawa mutane wulakanci

Tace Allah bazai baka iko ba, kuma ba wanda zai sanni a mace Sai mijina

Wani dariya yai yace ai in akwai wanda zai zama mijinki ba kowa bane illa ni

Wani kallo tamai, Ya ficewarshi

Hankalintane ya tashi matuka, Leke leke taketayi seda ta tabbatar ba kowa, Kunna wayarta yai ta kara kiran Number boyayyen masoyinta Still A kashe

      Hawaye Masu zaf zafi suka zubo mata, tace Ya Allah see me through

***
Bangaren Haidar kuwa yayi sallar magrib ya kwanta a kan sallaya saboda besamu yaje masallaci ba kanshi namai ciwo

Mafarkin Fauzeey yayi wai gatanan Ta biyoshi tana kuka, Wasu mazaje suna binta da gudu Tanata kwalla mai kira shi kuma sunyi fada yayi fushi

    Tana katemakeni zasu kasheni please

Firgigit ya tashi da addua, Natsuwa yai yana nazarin mafarkin..........

Muje ZUWA

Yours Ummiey Xeey

Follow
Vote
Comment

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now