LAIFINA NE 33

81 11 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*Dedicated this page To all My fans...I really like ur support thanks sweeties👄*

*PAGE 3️⃣3️⃣*

    Hajara Labe take bayan labule tana kallon Haidar yanda yake Daukar Hotuna yana sawa a status, Duk da baa taje Makaranta ba Amma kwakwarwarta naja, dan tana saurin daukar abu, tana ganin yanda Haidar yake Saka pics dinshi a status, Murmushin mugunta tai,

   Haidar gefe yadan juya ya dauka pic din yana kallon wani waje ba yana kallon camera ba irin ta gefen nan, Hajara na ganin Haka ta shugo hoton ta baya batare da ya sani ba ta shiga kusan hutuna uku gashi sunyi kya sosai,

Karamar wayarshi na daki Yaji yana ringing dan haka ya ajiye babban yaje yai picking karamar,

yana shiga Hajara ta dauke wayar ta shiga kitchen dama taga Yanda yake sawa a status, Aiko ta saka wanda ta fito a ciki, kamar Ana jira mutane suka fara viewing

Shi kuma Ya fito yaga wayar bata falo, dan haka ya koma dakinshi, Ya fara nema beganshiba,

Dawowa falo yai yaganta kuma a kujera, Messages din suketa shuguwa yasan na birthday wishes ne, dan haka yai off din datarshi

Yaci gaba da wayarshi a  yar karamar waya

Kowa mamakin Pic din dayasa guda uku daga baya yakeyi

Se Comment akeyi dan Gulma, daga wacece wannan se Itace matar dan kowa yasan ba yar gidansu bane dan This this the time da sukaga yasaka pic din sabuwar fuska, kuma ansan yau ranar farincikinshine dole zai saka Wacce take very Important to him, Kuma be saka hotunan Family dinsu indai ba in group akai ba, balle a ce Family member ce

***
    Fauxeey Kuwa tana zaune taga Karfe goma wata zuciyar tana taje wajen aikinta wata zuciyar kuma tana karkije, Dan a yan kwanakin nan bakar wahala kawai yake bata, Ga isa ga komai zaiyi da Izza yake mata, Ita tasan bakomai bane kawai wulakantata yakeso yai kuma da Allah ta dogara,

Dan Haka ta tashi ta shirya ta tafi cike da fargaba da tsoro

    Koda ta shiga Gidan Samunshi tai A harabar gidan as usuall yana training, Daka mata tsawa yai yace Tsaya

Tsayawa chak tai yazo yana zagayeta kamar wani maye, Itakam Addua take tayi a zuciyarta, Kallonta yai yace yau naji kina warin talauci

    A zuciyarta kuwa tace Bakaji da kyau ba kuwa,
Tana tsaye dai batace mai komai ba

Me gadi ya kalla yace karfe nawa yanzu? Yacemai karfe 10:30,

Me kika tsaya yi? Da se yanzu kikaga dama zuwa? Zatai magana kenan yace malama dakata cikin izza sa isa..

Shuru tai tanata rokan Allah ya tsareta da sharrinshi, Zo muje yace mata

Yana tafe tana binshi a baya, azuciyarta tana mugu azzalumi, Fito mata da kayan wankinshi yai da yawa kuma ya bata one hour ta wankesu tas

To tacemai, ta kwasa tai bayan gidan Dashi, tana wankewa taji alamun Tafiya kamar anshugo

Sanda tai ahakali ta leka su waye, Yan mata tagani gudu biyu sun shiga dakin Ya rufe, Allah ya shirya tace Ta ci gaba da aikinta,  ranta tace kayan ma duk Karni suke, Yar karamar tsaki taja tace Ka kusan Zama abun tausayi inshaa Allah

Wankinta tai ta gama, suka bushe,

Dakin Tazo zata shiga da sauri ya tareta a kofar daki ya amsa ya shigar da kayan, Yace zata iya tafiya amma gobe tazo da sauri

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now