Part 30/31

354 26 0
                                    

UQUBAR UWAR MIJINA
(Based On True Life Story)(Full Of Sorrow)
https://www.facebook.com/groups/
1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
~*
*_~ We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to my
Beloved Baby Fatima Sulaiman Allah ya rayamin ke.
(30)&(31)
To bayan naje border na shiga niger daganan nayi abidjan don sayo kaya,to Alhamduliilah nakai lafiya kuma nasiyo kaya na abinda yakai miliyan hud'u,
To abinda yafaru dani bazan tab'a mantawa dashi ba,shine silar rugujewar rayuwata.
Bayan nabaro Abidjan nazo border dake tsakaninta da Niger custom suka tsayar damu,suka k'arbe duka kayayyakinmu.
Tashin hankali Wanda ba'asa masa rana na shiga,don mafarkin danayi ne ya fad'omin.
Kuka na fashe dashi don ganin basuda niyyar bamu kayanmu,mun kwashe tsawon awa hud'u amma babbansu yak'i kulamu.
Hak'ura mukayi gaba d'aya muka bargun,zuciyata duk ta cunk'ushe don bak'in ciki.
Gabanane ya fad'i tuno da mafarkina,subhanallah na furto tare da karanta innalillahi wainna ilaihirraji'un Allah ajirni fil musibati haza wakhalifni khairun minha,wannan addu'ar ita yakamata mutum yana karantawa aduk lokacin dawani abun yasameka bawai mutum yana ihu ba,Allah yasa mu dace Amin.
Bayan nazo Lagos se wannan matar ta fad'omin,k'iranta nayi tasanar dani inda take,nacemata ganinan zuwa,tace"...se nazo."
Cikin mota ne nake tunanin abinda ke faruwa ga rayuwata,bangama tunani ba wayata tafara ringing,ganin wata y'ar uwarmuce yasa na d'aga,bayan mun gaisa takecemin Fatima yanzu haka ina gida wata mata daga kano takawo gawar y'arki Fatima,ido na zare cikeda fargaba nace"...shikenan narasata na rasa Fatima mafarkina yazama gaskiya,kawai sena saka kaina tsakanin cinyoyina ina kuka mai tsuma rai dasaka tausayi ga duk mai sauraronta,haka har muka iso unguwar.
Unguwace mai kyaun gaske kunsan de yadda Lagos yake da gina ginan manyan gidaje ga kyau da tsari,unguwar gaba da baya gate ne,bayan Na sauk'a nak'irata tamin kwatance har na iso.
Da fara'arta ta tarbeni tana mini sannu da zuwa,bayan mun gaisa tace"... yanzu har kin kai kayanne ko kinbadane?,kuka na fashe dashi nan na fad'amata abinda yake faruwa,hak'uri tabani kan cewa nayi hak'uri Allah yana tare da ni."
Na k'ara dace mata ina hanya aka k'irani aka sanar dani rasuwar y'ata, tace"... Dama kina da y'a?,nace".. Eh inada yara biyu,nan nabata labarin rayuwata ina kuka tana kuka,nima nayi kuka lokacin da take bada labarinta na rayuwa,ba'aiyawa mutum ko kad'an,wasu burinsu su lalata rayuwar jama'a to Allah ya karemu da mugun ji da mugun gani Amin.
Kuka naci gaba dayi saboda rasa Fatima danayi,haka matar tadinga bani hak'uri har nasamu na d'an tsagaita.
Tace"....toh Yanzu zakije yobe d'inne ko yaya?,nace"...inason naje amma ina tsoron kar akamani a kano saboda dukiyar Hajiya."
Tace"....insha Allah bazasu kamakiba kiyita addu'a,to bayan sati uku a gidan Matar nakama hanyar kano a sace a tsorace don tsoron kar'akamani a d'aure ni.
Bayan naje yobe ne natadda gidanmu yananan yanda yake,iyayena naganina suka fashe da kuka,Rungumesu nayi ina kuka suna kuka.
Mama tace"....Fatima haka Allah yaso sa rayuwarki zamuci gaba da miki addu'a,Allah yajik'an Fatima ya gafarta mata,magana ma kasawa nayi se kuka.
Mama tace"....satin dayawue ina zaune a gd ni k'adai naji sallama,bayan nafito naga wata mata mai kud'i ga babbar mota. "
Bayan mun gaisa ko ruwa batashaba,tafara mini bayanin abinda yakawota, tace"...kinzauna a gunta tunda kikabar gida,to bayan tafiyarki Abidjan Fatima ta fara k'enda Wanda hakan yayi sanadin rasuwarta"
Tazomana da gawar Fatima,kuma na tambayeta shin meyasa bata binneta acan ba?,setacemin ita mutum ce Wanda Allah yabawa arziki tana tsoron ranar da zaki waiwayeta ki tambayi Y'arki kinga batada hujjar gamsar dake cewa Y'arki ta rasu kar jama'a su d'auka nayi tsafi ko kud'i da'ita, to wannan dalilin ne yasata kawomana ita.
Kuka nake na jinjina hali irinna Hajiya,mutum ce mai amana kwarai da gaske,nima nan nafad'a musu abinda yasameni,Mama tace"...Uhm Fatima haka Allah yaso da rayuwarki ,inamiki fatan alkhairi a rayuwarki,kuma Hajiya ta tabbatar mana da cewa ita ta yafemiki duniya da lahira gashi Y'arki ta rasu a hannunta.

Taku a kullum Young Novelist.

Royal Blood Typing

Alk'alamin Auta

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now