part 12/13

353 21 0
                                    

🐲🐲🐲
        UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story)(Full Of Sorry)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.

Dedicated to
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

Sayner Naseer Nd Aisha Abubakar(Dimple Deepika).

Anti Rabi'atul adawiyya Ina gaisuwa karki damu innazo Yola a gidanki zan sauka.

Welcome back Bandirawo am Bestie Aishat B Umar.

Pls amin uzurin rashin jina da'akayi ayyukane sukayi yawa amma insha Allah yanzu na dawo
(12)&(13)

Toh haka nake zaune a gidan yayana lokacin cikina nada wata biyu,to lokacin da matar yaya na tagane inada ciki ta tsorata sosai.

Kuka tasamin tana tambayata wayamin fyad'e,saboda ita a zatonta kamila irina  yazanyi  na yarda nayi zina harnayi ciki.

Uhm nace"...bakisan  jarabar dake jikinta ba bakisan aikin da'ke jikinta ba."

kuka nake nakasa magana saboda nima nasan wani abun yana bibiyar rayuwa ta,amma nakasa gane menene.

Dakyar nafad'a mata komai ina kuka sosai,kuka itama takeyi tace"....Fatima yazanyi da wannan abun Dan Allah karki fad'awa Mama kinga ke kad'aice gareta karki fad'a hankalinsu ze tashi."...

Cikin kuka nace"....Anti Hajara wlh in Yaya yasani nashiga uku kasheni zeyi,tace"....tashi muje asibiti a zubar dashi inba hakaba wlhh anshiga uku jama'a zasu sami abin fad'a a gari."

Tashi nayi  muka kama hanya batare da nace mata natab'a yunk'urin  zubarwa ba,muna zuwa wani specialist hospital.

Magunguna suka bamu sukace muna zuwa naci abinci nashasu cikin zai zube,muna zuwa gida naci abinci sosai nasha magani inajiran lokacin dasukabamu yayi cikin ya zube.

Da daddare bayan munci abinci muna fira yaya yashigo anti tamin saida safe tashige,nikuma dayake ana d'an zafi saina kwanta  da nufin anjuma innasha iska saina shige.

Ashe wannan kwanciyar danayi wani abin al'ajabine zai faru,Allah ne zai nunamin cewa komai saida izininsa yake afkuwa.

Ina kwance a tsakar gidan bacci yafara d'aukata sai naji k'asa tayi wata irin girgiza mai firgitarwa,bude ido nayi a zatona mafarki nake amma sainaga dagaske ne ba mafarki ba tsakar gidan duk jijjiga yake.

Take wani tsoro ya ziyarceni,at the same time kuma naji wani irin girgiza kamar wani babban  naman jeji yana  zuwa gareni,saboda ina  iya juyo takun abun kuma ko wane taku sai inda nake ya girgiza.

Nide tsoro ya rufeni kuma na kasa tashi na gudu,ga d'an k'aramin cikina yafara fitowa saboda inada girman ciki.


Abunne yake k'ara nufoni kuma a lokacin girgizar da k'asar takeyi tak'ara tsananta,cikeda tsoro nake k'ok'arin tashi saboda har nafara kuka ina karanto addu'oi.


Abunne yazo ya tsaya agabana kuma lokaci d'aya nadaina jin girgizar, kaina na d'ago a  tsorace don kallon menene.

Abin mamaki zakara (cock) nagani bawani mai girma ba, kuma fuskarsa tamk'e abun tsoro Yana tsaye akaina.

Cikin murya mai ban tsoro da tsawa  kamar ta mutum ya ambaci FATIMA!!!!! har sau uku,Kafin na amsa naji muryar yarinya k'arama tana amsawa,bangama tsinkewa ba saida nagane cewa daga cikina maganar ke fitowa.

A tsorace nakai hannuna  kan cikina inda abunda ke cikina yace"....Na'am,kuma duk wannan abun ba mafarki nakeba idona biyu kuma ko'ina da duhu se hasken farin wata dake haske tsakar gidan."


Muryarsace tak'ara dawo dani duniyar danaje,yace"....Fatima da fatan kina lafiya babu abinda yatab'aki?,amsawa tayi  tace"...Eh lafiyata kalau babu abinda yasameni."

Yace"...to Alhamduliilah nayi farincikin babu abinda yasameki,daganan kuma ya juya yafara tafiya nan take kuma ko'ina yafara girgiza kamar lokacin dayake zuwa.

Yana kaiwa k'ofar gidan naga ya bac'e,saboda daman bansan tayaya yashigo ba tunda an kulle gidan.

Wani wawan k'arfi ne yazomin bandamu da cikin jikina ba na antaya d'aki da mugun gudu nasaka sakata,kuma se alokacin jikina yafara rawa saboda gaskata cewa wannan abun   dana gani a zahiri ne ba mafarki ba.

Daganan na yanke shawarar bazan sake yunk'urin zubda cikin ba,da safe da anti ta tambayeni ko ansamu nasara  ban b'oye mataba nafad'a mata itama taji tsoro don haka tace"...mu bar cikin wata aya ce  wannan,kuma Insha Allah zata kula dani tasan ba halina bane k'addarace"...



Toh muje zuwa.
Taku a kullum.
Young Novelist.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Autah✍

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now