Part 16/17

342 25 0
                                    

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on true Life Story) ( Full of Sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

Dedicated to
My 1 Nd Only Boo
Nisful Hayatee....

(16)&(17)

Da safe dana tashi na tambayi Khamis  cewa zanje gida, ya amince don haka ina gamawa nakama hanyar gidan da'aka sanar dani a mafarki.

Ina zuwa k'ofar gidan nayi sallama,wani yarone ya amsa,na tambayesa Malam yananan yace"...eh bari inmasa mgna."

Bayan Kamar minti 3 se yazo yace"....Ance kishigo ,shiga nay da sallama cikin parlourn."

Zaune yake da carbi a hannunsa mutum mai cikar haiba da kamala,bayan mun gaisa se yace"...baiwar Allah bangane kiba,tace"...nice Fatima surukar....nafad'a masa sunan surikata.

Ido ya zaro yace"...kece Fatima matar Khamis?,nace"...eh Dan Allah malam ka taimakamin ka warwaremin abinda kamin,ka tayusayawa mahaifana da rayuwar yaran dazan haifa."

Ajiyar zuciya yayi ya kalleni cikin jimami yace"...Allah Sarki Fatima kiyi hak'uri  a Yau nayi dana sanin aikin danayi miki,hak'ik'a UWAR MIJINKI tazo na mata aiki akanki kuma ba'aguna kad'ai ta tsaya ba tana kanyi miki aiki don ganin rayuwarki ta tagayyara,amma ina zuwa,ya tashi ya shiga wani d'aki ya fito."

Rubutu  yayi ya wanke yabani nasha,yace"....gashi Fatima nayi wanda zan iya nikam na warware wasu aikina akanki wasu kuma bazasu warwaru ba,amma Fatima keda kwanciyar hankali se a hankali wata k'ilama har kibar duniya bazaki zauna guri d'aya ba don aikinta kenan akanki kada kiyi amfani a rayuwa,Fatima kiyi hak'uri kiyafemin kitashi kije Allah yabaki lafiya.

Tashi nayi ina kuka,a zuciyata nace"...menayiwa  UWAR MIJINA ta tsaneni haka,to a washegarin  abun ne Khamis ya sakeni na koma gida,kuma a ranarne nayi mafarki ina kwance a gidanmu wai  matar danagani tana zuba zinare a jikin gidan Khamis tazo tana kwashewa tana tafiya dasu,to wannan shine silar karyewar arzikin Khamis.Muje zuwa.

CIGABAN LABARI.

Zuwana k'auyen danginmu da kwana d'aya na haifi y'ata mace kyekyawa kamar balarabiya ga gashi ga fari kamar ka latsa jini ya fito,duk da bata hanyar aure ja sametaba se naji inasonta son hak'ika haka ma mutane suna sonta kowa se so yake ya d'auketa.

Wani kawu nane ya tambayi wane suna nakeson asamata,har zance yasakamata sunan mahaifiyata se kawai sunan da zakaran yak'irata ya fad'omin,nace"....kawu asamata  FATIMA."

Yace"...to Allah ya raya ta yasa mai tausayin mahaifa ce,amin kowa ya amsa."

Ranar suna yarinya taci sunan Fatima,kuma Alhamduliilah komai anyishi a wadace.

Haka na zauna anamin wanka a k'auyen kuma ana kula dani sosai,kuma har lokacin Mahaifin Fatima yana zuwa guna ko ragon suna ma shiya  siya donshi a shirye yake ya amshi Y'ar sa.

To ana hakane naji labarin Khamis ya saida gidan mansa Wanda ya rage,gidan dana zauna acikima ya saida ya koma baida komai se ana taimak'onsa

Hartakai ta kawo  yaronsa Wanda shiyake  bawa mai ya saida yasamu riba,to yanxu shi yake taimakawa Khamis da abinci da kayan sakawa,Mahaifiyarsa kuwa a yanzu duniya ta mata zafi amma dukda haka bata daddara ba tananan tana bibiyar rayuwata.

To yau nayi arba'in kuma dangi sunyi abun sadaka harda Abban Fatima,and'anyi taro ba laifi akayi adddu'a aka tashi.

Toh haka nake rayuwa a k'auyen nida y'ata,Masha Allah Fatima se girma take Kamar ba Y'ar wata biyu ba.

Yau Kamar kullum mun kwanta bayan namana addu'a,acikin barci wani bawan Allah yazomin yana sanar dani na rik'e y'ata da kyau don Fatima Y'ar baiwace.

To daman ina sonta sosai fiyeda Ilham,uhmm yau kuma Fatima tacika Wata takwas inda har rarrafe take,jama'a se yaba wayo da girmanta suke.

Tana wata Wata goma sha d'aya tadaina shan nono,sede taci abinci ta k'oshi tayi bacci ga Allah yabata hak'uri da juriya Sam batada rigima.

Hakanne yasa kowa yakesonta kuma yakeson d'aukarta,kullum cikin bata kyauta ake,wani gamin in aka d'auketa tun safe se yamma za'a kawomin ita.


Uhm Ku biyoni donjin sabon kaddarar dazata riski wannna baiwar Allah n.

Ku KASANCE tare da YOUNG Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Auta

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now