_"Ki shirya tarban babban bak'onki gobe da misalin takwas na dare insha Allah."_ siririn tsoki taja tana fadin"Kaji dan rainin hankalin wato ma bazai zo da rana in ga fuskarsa ba sai gari yayi duhu."

***********
Yau gidan shugaban k'asa babu lafiya don anyi news da abunda ya sami su Hameed acikin kwanakin nan da suka gabata, Momy ta zazzaga ruwan bala'i kuma har waya ta yiwa Mamu taci mutuncinta dak'yau.Mamu nata kuka kamar ranta zai Fita, Muhsin ne keta lallashinta kuma shima d'in sosai ya shak'a da irin zagin da Momy tayi wa matar tasa, azuciye yace"Kema ya miki k'yau, ina fatar daga yanzu zaki fita daga harkar Hameed Tunda shi d'in ba d'an goyo bane, rabon daya k'iraki har kema kin manta, ko kuwa kun samu matsala ne ban sani ba.?" Itama d'in afusace tace"Babu ruwanka Muhsin, dan girman Allah kabar shiga sabgar da bata shafeka ba, Abdulhameed k'anina ne kuma ya zama dole in shiga harkarsa don jini ya wuce yadda kake tsammani, idan bazaka iya shanyewa ba to ka sakeni muhsin in har akan Abdulhameed ne." Cike da mamaki ya mik'e tsaye yana kallonta, ji yake kamar maganar nata almara ne don haka yace yana sakin murmushin dole"Haba dai Maryam ina jin wasa kike ko.?kin saurari kanki kuwa.?cewa kikai in sakeki in har akan Abdulhameed ne fa.?"
"Ba wasa nake ba Muhsin, zauna kaji wani al'amarin da zai girgizaka, Ni da Abdulhameed mun tafka babban kuskure lokacin yarinta, Ka kwantar da hankalinka ba wai ina nufin wani abun tirr d'in bane ya shiga tsakanina da k'anin nawa ba, a'ah da sauki ammh ba sauki, Na tabbata girman alk'awarin dake tsakaninmu ne ke wahalar damu duka ayanzu, Mun kasa sauke wannan nauyin don bazai tab'a yiwuwa ba, ma'ana alk'awarin ba wanda zai tab'a cikuwa bane, Mun tafka kuskure babba, Allah sarki yarintarmu bata tsinana mana komi ba sai bala'i da kuma dana sani.Muhsin zauna kaji dalilin dayasa ni da Abdulhameed muke jin muguwar soyayya ta yan'uwantaka na yawo ah jininmu."

**
Ab'angaren Hameed kuwa Dad bai bari ko kadan lalurarsa ta tashi ba, jansa yayi dakinsa ya shiga kwantar masa da hankali sosai, yace"Abdulhameed inason ka kwantar da hankalinka insha Allahu zan yi maka abunda kakeso ammh for now inason ka bani goyon baya, Kayi na'am da zab'in mahaifiyarka sa'annan ni kuma kabar komi ahannuna zanyi wani abu akai." Ya furta yana cizan yatsa don tuni ya gama had'a duk wani plans akai, cike da mamaki Hameed yace"Dad yanzu kaima so kake in auri Suhailan.?" Da sauri Dad yace"Kai dai kawai kayi yadda nace, naka kawai ka zuba idanu kasha kallo Allah i promise to make u happy." Murmushin yak'e ya saki jin abunda Dad d'in ya fad'a kan yace"shikenan Dad, ammh in har na samo wacce nakeso d'in kana ganin zaka iya sa afasa aurena da Suhailah.?" Dafa kafadarsa Dad yayi yana Fadin"Insha Allahu son abunda kakeso shi za'ayi, burina ayanzu kawai ka amince da wannan Suhailar don inason ne na koyawa Sa'adatu hankali, darasin da zata dauka zai zamo izina ne ga sauran uwaye masu halaye irin nata."

Haka dai Dad ya cigaba da bashi magana har sai daya tabbatar da cewa ya gamsu sa'annan ya sallameshi.Hameed nason wannan yarinyar sosai don yana ji kamar bazai iya cigaba da rayuwa muddin babu ita ba, sai dai kuma jinin jikinsa na azabtar dashi sosai, akodayaushe yana tunatar dashi girman Alk'awarin daya dauka wanda bazai tab'a iya cikawa ba har abadan.

Da rawar jiki ya mik'e tsaye yana Fadin"Agaskiya Maryam kun tafka babban kuskure, haba no wonder nina fada wannan soyayya ta yan'uwantakar ba'a banza bace, meyasa zakui irin wannan al'kawarin jinin bayan kuna shak'ikan juna.?meyasa Maryam.?meya shiga kwak'walwarku ne awannan lokacin.?"

"Muhsin Allah ne kadai yasan dalili don komi baya afkuwa sai da sanin ubangiji, Ni ina ji ajikina ba hakanan kawai Allah ya kaddari faruwar hakan ba sai don bullowar wani al'amari mai girman gaske, wallahu ahlam! Allah mafi sani.In kuma hasashena ba gaskiya bane, to ina jin babban darasi ne agaremu.Muhsin don't judge us, ina jin tamu kaddararmu ce tazo ahakan, ina kuma rokon Allah yasa mu cinye wannan jarabawar, Muhsin dan girman Allah kar kace zaka rabu dani sa'anann na had'aka da Allah ka binne sirrinmu aranka banason kowa yasan irin yarintar da muka zuba abaya nida k'anina." Muhsin yace"Maryam in kinga na rabu dake to sai in mutuwa nayi, ko kuma in kece ayau kika sani gaba kikace alallai saina sakeki, sannan kuma zancen nan nayi alk'awari babu wanda zai ji, ammh fa Maryam alk'awarin jini fa ba wasa bane."

_kuyi hakuri dani wutan nepan ne ya zama zuma😩._

_2 more free pages to go, register now to avoid regretting later_

_Ku nunamin kauna ta hanyar siyan *SAWUN GIWA* akan 200naira kacal ta bank account dinnan *0824409678*, *MUSTAPHA HAFSAT*, *ACCESS BANK* ko katin waya ta *07065481260* saiku turo da screenshot ta *07065481260*....Hafnan tana maraba da masoyanta na gaskiya_
*GARA'BASA! GARA'BASA!! GARA'BASA!!!*
_Akwai gara'basar k'ayatattun novels d'inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk'i 👉 *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja'art, tare da novel d'in *SAWUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za'a samesu gabad'aya cikin sauk'i da rahusa akan naira d'ari biyar (N500), ga masu buk'atar biyu daga ciki zasu turo naira d'ari ukku (N300), ga wad'anda zasuyi transfer ta bank ga account number d'in da za'a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad'anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara'basar ko da kud'inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu😍👍🏻*

*#Ilove💓*
*#Anatare*
*#IWA*
*#Nagode*
_#ʰaᶠⁿaⁿᶜʸ_

    ♡

_*INA ZUWA🏃🏻‍♀️*_

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now