page 37

11 0 0
                                    

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣7️⃣

Jikin Lily ya yi sanyi matuƙa da jin irin roƙon da 'yan uwansa ke masa.

Sai da ya ɗan yi jim, kamar ba zai ce komai ba sannan ya buɗi baki ya ce "Duk na ji roƙonku, haƙiƙa ina matuƙar son my angel don haka zan yi sadaukarwa a gare ta, a yanzu na ajiye matsayina na mijinta, na dawo matsayin yaya Lukman ɗinta mai son ganin farincikinta, don haka na karɓi tayin Nasreen da hannu bibbiyu,  Allah yasa hakan shi yafi alkhairi." a sanyaye ya yi zancen.

Dukkan mutanen ɗakin suka amsa da Amin cikin farinciki.

Nasreen ce ta tako zuwa gabansa ta ce "Na gode sosai yaya, Allah ya bar zumunci."

Nan take ya saki Sabreen saki ɗaya, ya juya a hanzarce ya bar ɗakin, Jb ya bi shi cikin sauri gudun a samu wata matsalar.

Fitowar su daga ɗakin ya yi dai-dai da ƙarasowar Afrah ciki hanzari ta zo duba ƙawarta.

A gurguje su ka gaisa, har ta sa kai za ta wuce Lily ya Kira sunanta "Afrah! Don Allah tsaya ki ji."

Juyowa ta yi ta tsaya a inda take ya tako zuwa wajen ya ce "Don Allah ko kin san Address ɗin wanda Sabreen take so? Ina nufin inda zan same shi a yanzu.

Shiru ta yi ta na tunanin me kuma zai yi da address kar fa ta gaya masa a je a yi wata ɓarnar.

Shi ne ya katse mata tunani da cewa "Don Allah idan kin sani ki gaya mun, zan je na sanar da shi cewar na bar masa Sabreen ya zo a ɗaura masu aure."

Nan da nan fara'a ta bayyana a fuskar Afrah, ta ce "Don Allah da gaske kake yaya Lukman?"

"Eh." Ya bata amsa a taƙaice.

Cikin tsananin murna ta ce "Allah sarki yaya Lukman Allah ya saka maka da alkhairi, abokin mijina ne, bari na kira shi na ji ko ya farfaɗo daga suman."

Ashik ta Kira ya tabbatar mata da farfaɗowar Asim ɗin sai dai ya gaya mata ya na cikin wani hali.

"Ga mu nan zuwa yanzu, insha'allah daga yanzu wahalarsa ta yanke "

Daga haka ta kashe wayar ta dube su ta ce "Yaya Jb don Allah ku bari na duba jikin Sabreen sai na raka ku, mijina ya na can, daga can za mu wuce gida."

Ta na gama faɗa ta juya ta shiga ɗakin.

Can bayan wasu mintuna sai gata ta fito, suka rankaya sai asibitin da a ka kwantar da Asim.

Ko da suka isa ƙarfe takwas da kusan rabi na dare.

Kai tsaye ɗakin da yake suka nufa, cikin Sa'a kuwa suka tarad da su Mom, Dady, yaya Mubeen da Muniba duk suna gun, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Afrah ba, domin ta na so kowa ya ji abinda Lukman zai faɗa da kunnensa.

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now