page 33

15 0 0
                                    

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣3️⃣

Da gudu Asim ya tafi zuwa ƙasan benen da ya ke ta riga ta dire a galabaice.

Durƙusawa ya yi a gabanta, har ya kai hannu zai ɗago kanta a firgice saboda ganin jini yana zuba a goshinta, sai kuma ya yi saurin janye hannunsa saboda tunawa da ya yi cewa ita fa ba muharramarsa ba ce.

Ya na nan durƙushe sai rarraba ido ya ke kamar taɓaɓɓe, ya ma rasa me zai yi.

Ita kuwa sai nishin wahala take saki saboda duk ta kukkuje a wasu sassan jikinta ga goshinta da yake a fashe.

Ɗago kanta ta yi daƙyar, idonta ne ya sauka akan Asim dake durƙushe a gabanta, cikin wani yanayi marar misaltuwa, karaf idonta ya faɗa a cikin nasa, saurin mayar da kanta ƙasa ta yi tare da rufe ido, saboda wani sabon sonsa da ta ji ya tsirgar mata a zuciya.

Suna cikin wannan yanayin ne Abba da Ashik suka ƙaraso gurin a ruɗe.

Abba sai maimaita kalmar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un, ya ke.

Hannu biyu Abban ya saka ya ɗagata tare da saƙalo ɗayan hannunta a kafaɗarsa, ta kuwa dafe shi sosai.

Nan ya ja ta suka fara takawa a hankali sai famar faɗar "Wash! Wash!! "  Take alamar ta na jin zafi idan ta taka ƙafar.

Abba ko sai sannu ya ke jera mata.
Har sun ɗan fara nisa ya waiwayo ya kalli su Ashik ya ce "Y'an samari nagode sosai da ƙarba gayyata ta da kuka yi, za ku iya tafiya, bari na shigar da ita ciki."

Daga haka ya ci gaba da tafiya tana maƙale da shi, amma kanta a sunkuye yake har suka isa falon Umma.

®®©©©®®®®

Shi dai Asim Ya na Nan durƙushe a inda yake har bayan shuɗewar wasu mintuna da ba za su haura biyar ba, ya kasa tashi daga gun, sai hawaye ya ke, shi kaɗai ya san irin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa akan wannan lamari.

Ashik ne ya shiga lallashinsa, daƙyar ya lallaɓa shi suka bar gidan, don da ya kafe akan cewa shifa ba zai tafi ba sai ya ga halin da Babynsa take ciki.

Ko a mota ma da suke tafiya ya kasa cewa uffan, sai kukan zuci da yake don tun tasowar su, Ashik ya roƙe shi a kan ya goge hawayen ka da ya sanya mutan gidan nasu damuwa.

Kai tsaye gadon ƙaya ya nufa don ajiye Asim, domin ya na so ya wuce gun amaryarsa, saboda yamma ta yi ba ya so ta tashi hankalinta na rashin dawowarsa da wuri.

A ƙofar gidan ya yi parking saboda anriga an kira sallar la'asar a masallacin da ke kusa da gidan, har ma an kusa tayarwa.

A gaggauce suka fito zuwa Masallacin, kowannen su rai a jagule, alwala suka yi tare da shigewa masallacin, amma fa kallo ɗaya za ka yiwa Asim kasan baya tare da nutsuwarsa, don dai ya kasance mai riƙo da addini ne, ban da haka da a wannan ranar ba na tunanin zai iya yin sallar a kan lokaci.

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now