page 34

11 0 0
                                    

https://www.facebook.com/104534761033461/posts❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


✨✨ page 3️⃣4️⃣

A washe garin ranar Lily ya shigo garin Kano don duba lafiyar Amaryar tasa, sai dai ya tarad da saɓanin abinda ya yi tunani.

A da idan ya zo Kano Sabreen har rasa take inda za ta saka kanta don murna, amma a wannan zuwan sai ya ga bata farin ciki ko kaɗan sai ma wani kicin-kicin da ta yi da fuska, alamar bata so zuwansa ba.

Da yamma su na zaune a falo su duka a na hirar yaushe gamo, Umma sai tsokanarsa take ta na cewa "A'ah angon Sabreen kenan, ga ka nan ka ƙara kyau abunka."

Sussune kai ya shiga yi, ya na sosa ƙeya wai shi mai kunyar surukai, idonsa na ƙasa, amma lokaci zuwa lokaci ya kan saci kallon Sabreen.

Lura da hakan ne ya saka Umma ta fice daga falon, ta na shiga ɗakinta ta ƙwalawa Nasreen kira, ta yi hakan ne a dabararta ta ba su damar kaɗaicewa da junansu ko sa fuskanci juna, don ta lura har yanzu Sabreen ba ta wani son ɗan nata, amma ba damuwa a hankali za ta ware bayan auren, mai wuyar dai a ɗaura auren.

Ai kuwa ya na ganin sun watse ya matso kusa da Sabreen ya na faɗar "My wife ya jikin?"

Banza ta masa kamar bata ji ba.

Ransa ya ɗan sosu da hakan da ta masa don ya na da yaƙinin ta ji kawai ƙyale shi ne ta yi, amma sai ya dake ya yi murmushi tare da kuma cewa "My wife lokacin aurenmu ya na gabatowa, wane shiri kike mana?"

Shiru ya ɗan yi tare da kallonta, ganin ba ta da niyyar magana ne ya saka ya cigaba da cewa "Amma na ga kamar bakya murna da ganin Lilynki saɓanin da, da kike matuƙar farin ciki yayin da duk na zo."

Tashi zaune ta yi daga kwancen da take, domin maganganunsa sun ɓata mata rai matuƙa, Lallai ya cika ɗan rainin hankali, wato ya na son ya nuna mata bai ma san laifinsa ba?.

Da wannan tunani ta yunƙura kamar za ta miƙe, kuma sai ta koma ta zauna tare da cewa "Wanne shiri kuwa zan yiwa auren da ba na mararinsa? Ina ga ai shiri naka ne kai da za ka yi aure don soyayya, maganar murna da ka ke kuwa wannan a da ne, ina yin murnar ne saboda farin cikin ganin yayana Lukman mai adalci da son ganin farin cikina. Yanzu kuwa ba na yin murna saboda wannan Lukman ɗin saɓanin wanda na sani ne a baya, wannan bai damu da farincikina ba, taya kake ganin zan damu da shi?"

Tun da ta fara maganar ya yi shiru kamar ruwa ya ci shi, mamaki ya gama cika shi, wai yaushe Sabreen ta lalace haka? Anyah! Bata samu shafar Aljanu ba bayan rabuwar su? Don ya ga yanzu gaba ki ɗaya ta zama mara kunya, saɓanin da da take da haƙuri, kunya da biyayya.

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now