page 35

10 0 1
                                    

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

DEDICATED TO: BESTIENA MARYAM NASIR(MANAB YAR BABA) & SISTER JANNAT M NASIR

WANNAN PAGE KAM NAKU NE SAI YANDA KUKA SO YI DASHI.

BESTINA MANAB INA MIƘO GAISUWA TA MUSAMMAN, DA FATAR ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKI YA TSARE MUN KE A DUK INDA KIKE.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣5️⃣

Afrah ce ta shigo falon da yake cike da mutane.

Bayan y'an gaishe-gaishe tsakaninta da mutanen falon, ta wuce kai tsaye zuwa ɗakin Sabreen.

Isarta ya yi dai-dai da lokacin da Anty Jidda ke ƙoƙarin fitowa riƙe da roba wacce take ɗauke da kayan gyaran jikin amarya a hannunta, ga dukkan alamu gyaran jikin ta gamawa Sabreen.

Gaisawa suka yi da Antyn sannan ta shige ciki.

Can ta hango Sabreen ta kifa kanta a kan gado, ta na kuka mara sauti, da ya ke dama ta na zaune ne a gefen gadon.

Ƙarasawa Afrah ta yi haɗe da dafa ta, a ɗan razane ta juyo don ganin ko waye.

Ganin Afrah ce ya saka ta juyo gaba ɗaya tare da saka tafin hannunta ta goge hawayenta.

Zama kusa da ita Afrah ta yi gami da riƙo hannunta ta ce "Ki yi haƙuri ƙawata,  insha'allah komai zai zo ya wuce kamar ba a yi ba, kuma insha'allah za ki tsinci farinciki a rayuwar aurenki nan gaba kaɗan."

Zare hannunta ɗaya ta yi ta kai saitin fuskarta tare da ɗauke guntuwar ƙwallar da ta zo mata ta ce "Dole na yi kuka ƙawata, ni da kaina na rusa farincikina, ban taɓa tsammanin soyayyar Asim ta yi girman da za ta iya saka ni cikin irin wannan gagarumin tashin hankali ba, sai yanzu da na rasa shi, na san ba zan taɓa samun nutsuwa ba in ba shi, ni fa ina ji da an ɗaura auren nan mutuwa zan yi..."

Hannu Afrah ta kai ta yi saurin rufe mata baki, ta na faɗar "Kul, kada ki sake zancen mutuwan nan, insha'allah ba za ki mutu ba sai mun ga ƴaƴanki ke da Asim."

Y'ar dariyar jindaɗi ta yi, duk da ta san cewa Afrah ta faɗi hakane don ta faranta mata.

Nan da nan kuma fuskarta ta sauya zuwa damuwa kamar ba ita ce ta gama dariya yanzun nan ba, ta ce "Don girman Allah Afrah ki taimaka min, ina son sanin halin da Asim ɗina ya ke ciki, domin na ga tashin hankali ƙarara a fuskarsa a ranar da na masa gani na ƙarshe, ki taimaka min ki haɗa ni da shi asirrance."

Ajiyar zuciya Afrah ta sauke sannan ta ce "ya na asibiti fa, bari mu gani ko zan same su."

Wayarta ta ciro da zimmar kiran mijinta, kawai sai ga kiransa ya shigo, sai dai vidio call ne da yake ta manta datar ta abuɗe shiyasa.

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now