page 32

22 1 1
                                    

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣2️⃣

Da ƙarfi ya fige shi daga gun zuwa wajen hall ɗin, sai da ya ɗan yi nisa da hall ɗin kaɗan, dai-dai tsakiyar harabar hotel ɗin ya saki hannunsa tare da ƙanƙance idonsa cikin zafin rai ya fara magana kamar haka "Malam abunka ya fara yawa fa, me kake so da waccen yarinyar ne na ga ka na wani shishshige mata?"

Jalal da tun lokacin da ya ji an figo shi ba tsammani, ya juyo don ganin ko waye, ganin Asim ne ya saka mamaki ya kuma kashe shi, bai samu damar cewa uffan ba sai yanzu da Asim ya tambaye shi..

Sakin fuska  ya yi tare da yin y'ar dariya ya ce "Habah Abokina!, ni har ka tsora ta ni yasin, na sha ko wani abun ne dabam, zancen yarinya da ka ke kuwa ai ba sai na gayama ba, ya kamata ka fuskanci cewar ta cafki zuciyata ne, don Allah gaya mun sunanta na ga kamar ka san ta koh?"

Ya ƙarashe zancen ya na y'ar dariya.

Ran Asim idan ya yi dubu ya ɓaci, ƙara matsowa ya yi daf da shi ya cakumi kwalarsa cikin matuƙar ɓacin rai ya ce "Ka buɗe banzayen kunnuwanka ka ji ni da kyau Jalal, wannan yarinyar ta fi ƙarfinka, ita ba sa'arka ba ce, ka fita harkarta ko da wasa na sake jin ka ambaci kalmar so tsakaninku sai na ɓaɓɓalaka yasin."

Ya na gama faɗa ya saki kwalarsa tare da hankaɗa shi ya yi baya.

Har ya tafi tagaa-tagaa zai faɗi Ango Ashik da ke isowa gun dai-dai lokacin ya tare shi da hannayensa, sai ya faɗa a ƙirjin Ashik ɗin.

®®©©©%%%%%™™

Acan cikin hall bayan ficewarsu Asim ne, hankalin ango ya dawo gun rawar, rarraba ido ya shiga yi, bai ga Asim da Jalal ba, sanin halin Asim ya sa hankalinsa ya tashi sai ya tambayi ɗaya daga cikin abokanansa, a ka tabbatar masa da Asim ya ja shi sun fice, cike da damuwa ya fice daga hall ɗin ya fara neman su.

Ita kuwa Sabreen sai a lokacin ta ɗago kai, ganin ba shi agun ya tabbatar mata da ya koma mazauninsa, wannan dalilin ne ya saka ta juya zuwa mazauninta sai dai baya gun.

©©©©%

Shi ko Ashik fitarsa ke da wuya ya hango ɓarnar da ke shirin afkuwa, a hanzarce ya ƙarasa gun dai-dai lokacin da Asim ya hankaɗo Jalal ya na huci.

Janye Jalal ɗin ya yi ya mayar da shi bayansa tare da kallon Asim ya ce "Haba Asim, me ka ke yi haka ne?, menene ya shiga tsakaninku haka?, yanzu fa ku ba yara ba ne ya kamata ku kama girmanku, abinda ba ku yi da ƙuruciya ba shi za ku yi yanzu da girmanku?"

Ya ƙarashe zancen ya na duban Jalal.

Jalal ya ce "Ni fa ban san me na masa ba daga magana sai ya cakumi kwalata."

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now