page 36

10 2 0
                                    

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*(Labarin soyayya mai ɗauke da wani salo na dabam)*

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

DEDICATED TO: MY ƘAWAS FATIMA SUNUSI RABI'U (UMMU AFFAN)

ƘAWAR AMANA, INA FATAR AMINCIN DAKE TSAKANINMU YA ƊAURE HAR ABADA.

WANNAN PAGE NAKI NE.

ƘAWALLIYE INA MIƘO GAISUWA TA MUSAMMAN, DA FATAR ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKI YA TSARE MUN KE A DUK INDA KIKE, ALLAH YA RAYA ZURI'A AKAN SUNNA.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣6️⃣

Umma bakya so na tun da har ba kya son abinda nake so, ku sani cewa matuƙar kuka bari Asim ya mutu da ƙaunata, tabbas nima zan bi shi."

Ta faɗa ta na ci gaba da kukanta da fashe-fashen abubuwa.

Ganin abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ya saka Baba Babba ya fice cikin hanzari ya je falonsa don neman daɗaɗɗun ajiyayyun maƙullan gidan.

Falon nasa a cike yake damƙan da da maza abokanan su Abba.

Haka ya shiga birkita lokokin ɗakin ya na neman maƙullin kasancewar an daɗe ba a yi amfani da su ba, daƙyar ya gano maƙullan ya dawo a hanzarce.

Ya buɗe ɗakin, ya na buɗewa jama'ar dake gun suka afka ciki gaba ɗaya, amma duk Lily ya riga su isa gunta ya na faɗar "Habah! My angel so kike ki kashe mun kanki ne?, me yasa bakya sona?."

Su Abba ne suka yi saurin janyo ta daga ɗakin, su ka fito da ita waje don ganin yanda goshinta ya yi wani ƙulu sosai, Allah dai ya gyara gun bai yi jini ba, amma ya tashi sosai.

Alhaji Zaid ne ya ce "A kaita asibiti mana."

Abba ne ya yi saurin cewa "A'a Alhaji ai ba wani rauni ta ji ba, kawai a bar maganar asibitin saboda jama'a basu riga sun watse ba."

Da yake shi Abban bai damu da zuwa asibiti ba.

Hajiya Babba ce ta nemo pain reliever tare da ruwa ta bata ta sha.

Haka iyayen nata suka saka ta a tsakiya, su na ta yi mata nasiha da wa'azi har su ka ga alamar ta ɗan nutsu sannan suka watse.

Watsewar su daga gun kenan Jalila ta shigo gidan da fara'arta ta na faɗar "Ina Amaryar ne?"

'Yan matan dake falon suka nuna mata ɗakin, kai tsaye ta shige ta na faɗar "Amaryar Lily sai ƙamshi ki ke zubawa."

Murtuƙe fuska Sabreen ta yi tare da taɓe baki, bata ce komai ba.

A haka a ka cigaba da gudanar da shagalin bikin ba wani armashi sosai, domin ango da amarya basa cikin walwala.

####@@@@

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now