A ranar da aka ɗaura auren Ashik bai samu halarta ba, duk da matar shi ta gayyace shi, sai kawai ya bata uzurin cewa ya na jinya ne shiyasa ba zai samu damar zuwa ba.

Amma a zahirin gaskiya ya na taya amininsa kishi ne shiyasa ya ƙi ya je.

Bayan an ɗaura auren Afrah ta kira mijinta, domin ta shaida mi shi kamar yanda ƙawayensu dake can suka sanar mata.

Sai da ya duba ya tabbatar da Asim barci ya ke sa'annan ya amsa wayar.

Abinda bai sani ba shi ne Asim ba kwana yake ba lamɓo ya masu.

Ta na gama faɗa ya miƙe ya na faɗar "What! An ɗaura auren? Ya Salam!"

A zabure Asim ya miƙe zaune ya na rarraba ido, can kuma zuciyarsa ta buga da ƙarfi Dam! Kawai sai ya baje kan gadon a some.

Mubeen da Ashik hankalinsu ya matuƙar tashi, nan fa suka hau jijjiga shi amma inah! Ba alamun motsi a tare da shi.

A gigice Mubeen ya fita da gudu don kirawo likita, Ashik kuwa ya ma kasa ɗagawa daga gun, tuni ya manta wayar da yake duk ya ruɗe sai kallon Asim dake kwance ba motsi ya ke.

Afrah da take jin duk abinda ke faruwa ta wayar itama ta ruɗe matuka.

Likiti ne ya shigo ɗakin tare da duba shi, ya ce masu "Doguwar suma ce ya yi, amma insha'allah zuwa dare sai farfaɗo, amma a shawarce ku yi gaggawar nema masa abinda yake so kafin ku rasa shi gaba ɗaya."

Ya na gama faɗa ya juya ya fice, fitarsa ta yi dai-dai da shigowar Mom da Dady a ɗakin.

Mom ta ƙarasa bakin gadon ta na faɗar "My son ya jikin."

Shirun da ta ji ne ya saka ta juyo ta kalli Mubeen ta ce "Bai tashi daga barcin ba ne har yanzu?"

Jiki a sanyaye Mubeen ya ce "A'a Mom ba barci yake na, dogon suma ne ya yi."

Ashik ya ɗora da cewa "ya samu labarin ɗaurin auren Sabreen ne shiyasa."

A firgice Dady da Mom suke kallonsa "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Kai! Wannan wace irin rayuwa ce, kai kam Asim soyayya ta zame maka masifa a rayuwa, ita ta na can suna shan shagali cikin kwanciyar hankali kai kuma ka ƙare a some."
Mom ce mai wannan furucin yayinda idonta ke kawo ƙwalla.

©©©©©©©%

Da misalin ƙarfe 5 na yamma motoci suka zo don ɗaukar amarya.

Dama daga gidan Baba Babba za a ɗauke ta zuwa hotoro domin a can Lukman ya samu hayar gida.

Da aka zo fitar da amarya ne tashin hankali ya dawo masu sabo, domin kuwa ana zuwa ƙofar fita daga falo, ganinta ya ɗauke kawai sai ta sulale a gurin ta na sumammiya.

Hajiya Babba dake riƙe da hannunta ta rafka salati, nan fa hankalin kowa ya yi gun, sai salati ake.

Zee ce ta ajiye jinjirin yaronta dake hannunta ta fice da gudu don kiran su Abba.

Su na zuwa a ka kwashe ta sai asibiti.

A haka bikin ya watse kowa ya tafi cikin jimami, ba ma kamar Afrah da abin ya haɗewa biyu, ga rashin lafiyar abokin mijinta ga ta ƙawarta, ita kam ta na jinjina girman soyayyar da suke yiwa junansu, ga shi dai dukkansu sun suma a rana ɗaya ba tare da sanin ɗayansu ba.

Kai a wannan rana hatta Jalila da take munafuka sai da tausayin Sabreen ya ɗarsu a zuciyarta, har ta na ganin da ta na da hanyar gyara wannan kuskuren da ta yi, don ba shakka komai ya faru da Sabreen ita ce sila.

A haka ta koma gida a sanyaye ta na ta saƙa da warwara, ita kam yanzu duk jikinta ya yi sanyi ta tabbatar soyayyarsu daga Allah ce ba wanda ya isa ya raba sai shi da ya haɗa.

Yau ne karon farko da ta ji ta yi nadamar wani abu da ta aikata, ta na so ta je ta bawa Sabreen haƙuri amma kuma ta na fargabar abinda zai biyo baya, domin ko ba Sabreen da iyayenta ba, ko da nata iyayen da suka haife ta ta na da tabbacin ba za su yafe mata ba, shiyasa ta ja bakinta ta yi shiru ta na addu'ar Allah ya rufa mata asiri.

©©©©©©©©

Lily dake can tare da abokansa su na jiran a kawo amarya suka ji shirun ya yi yawa, kawai sai Jb ya ɗaga waya ya kira Zee a nan ta ke sanar masu abinda ke faruwa.

Hankalinsa ya tashi sosai da jin halin da ƙanwarsa ta shiga duk a dalilin soyayya, shi kam ya gama sarewa da lamarinta, ina ma yaya Lukman zai haƙura da wannan auren da ya ji daɗi matuƙa.

Shi da Lukman ne suka ɗunguma zuwa asibitin hankali tashe.

A can suka tarar da iyayen na su kowa ya yi jugum-jugum, ita dai amaryar ta na kwance a cikin wani yanayi da baka isa ka gane a raye take ko a mace ba, idan dai ba ka da ilimin hakan.

Nasreen ta na gefe sai rusgar kuka take har bata jin lallashin da Umman tasu ke mata.

Shigowar su yaya Jb ɗakin ne ya saka ta zo gun su da gudu gaban Lily ta durƙusa ta na kuka.

Ɗago idonta da suke cike taf da hawaye ta yi, ta kalle shi sannan ta ce "Don girman Allah yaya Lukman ka haƙura da auren nan, idan baka haƙura ba na san zan rasa 'yar uwata, ita kaɗai ce nake da 'yar uwa mace ka tausaya mun, na tabbatar in na rasa ta nima za ku rasa ni...."

Ɗan tsagaitawa ta yi ta na jan shassheƙa, yayinda mutanen cikin ɗakin suka zuba mata ido cike da tausayawa.

Shiru Lily ya yi daga shi har yaya Jb ba wanda ya tamka.

Ganin baya da niyyar magana ya saka ta ɗora zancenta da cewa "Ka tausaya min yaya Lukman, na san halin da kake ciki, na san kana cikin ɗemuwa da damuwar rasa soyayyar yayata, to a shirye nake da na maye maka gurbin ta, idan dai hakan shi ne zai dawo da farincikin yayata tare da na ka gaba ɗaya."

Wannan karon kam kowa zuba mata ido ya yi su Abba dake ƙofa a tsaye suna jinta sai a lokacin suka ƙaraso ciki.

Kowa mamakin Nasreen ya ke yarinya 'yar shekara goma sha biyar amma ta iya furta waɗannan kalaman.

Abba ne ya zo ya ɗaga ta daga durƙushen da ta ke, ya juyo ta suna fuskantar juna ya ce "Nasreen kin tabbatar za ki iya auran Lukman? Ki na son shi? Ka da ki saka aje a yi biyu babu kin ga dai halin da muke ciki."

Ɗaga masa kai ta yi alamar tabbatarwa sannan ta ce "Tabbas zan aure shi don dawo da farincikin yayata, amma ni ban san miye soyayya ba bare na gane ina son shi, na dai tabbatar zan iya rayuwa da shi har abada matuƙar zai kula da ni."

Abba ya kalle ta sosai, ya na jin ƙaunar 'yar tasa na ƙara ratsa shi.

Alhaji Zaid ne ya ƙarasa gurin ɗansa dake tsaye gun kamar an dasa shi ya ce "Lukman ka dai ji abinda Nasreen ta faɗa, shin kai ma ka shirya yin sadaukarwa ga masoyiyarka kamar yanda ƙanwarta ta yi?"

Sai a lokacin Lily ya ɗago kai ya sauke dubansa ga Nasreen, ba laifi, ita ɗin ma kyakkyawa ce, kamar su ɗaya sak da Sabreen, sai dai ita tafi Sabreen ɗin hasken fata da manyan ido.

Idan kuma a halayya ne zai iya cewa ba su da banbanci sai abinda ba a rasa ba tunda duk abu ɗaya ya yi su...

Sai da ya ƙare mata kallo sannan ya sauke ajiyar numfashi, ya na so ya yi magana amma bakinsa ya ƙi buɗuwa.

Jb ne ya dafa shi ya na Faɗar "Wannan shi ne karon farko da zan nemi alfarma a gunka ɗan uwana, don Allah ka yi haƙuri ka yi wannan sadaukarwar wa angel ɗin ka, na san ka fi kowa sonta ba za ka so ka rasa ta ba.......

Follow me on wattpad @ummu inteesar



UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹

RIKICIN MASOYATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon