Bayan kammala sallar ne ya shige gida, Ashik bai bi shi ciki ba, ya ja motarsa ya nufi gidansa don isa gun Amaryarsa Afrah.

®®®®®®

A can cikin gidan kuwa ko da Asim ya shiga Babban falon ba kowa, hakan ya masa daɗi, domin a yanayin da yake baya son jin mutane kusa da shi bare a dame shi da tambayoyi.

Saurin haurawa sama ya yi ya shige ɗakinsa, bai damu da kullo ƙofar ba, ya zube a kan kujerar falon nasa, sai sauke ajiyar numfashi ya ke, haƙiƙa ya na cikin wani mawuyacin hali.

®®®®®®®®®®

Su Abba kuwa  hankali suka ƙarasa falon, a kan doguwar kujera ya dire ta, sai jera mata sannu ya ke.

Umma dake fitowa daga kitchen yanzu ta ƙaraso gun da sauri tana faɗar "Subhanallah! Sabreen me ya same ki?."

Bata iya cewa komai ba, sai ciccije leɓe take alamar tana jin zafin ciwon, ganin tana ta haɗa gumi, ya sa Umma ta kama zumbulelen hijabin ta cire mata shi, har zuwa lokacin goshinta na zubar da jini.

Cikin hanzari Abba ya juya ɗakinsa, domin ya ɗauko wayarsa tare da first aid box don bata agajin gaggawa.

Fitarsa falon ya yi dai-dai da shigowar Nasreen gidan, dawowar ta kenan daga aiken Umma, ganin ya wuce cikin hanzari ba tare da ya kula da gaisuwar da take masa ba, kuma ga shi kamar a ruɗe ya ke, hakan ya saka ta ji a jikinta cewa ba lafiya.

Cikin sauri ta ƙarasa falon dai-dai lokacin da Umma ke gyarawa Sabreen kwanciyarta a kan kujerar ta na ta jera mata sannu.

Ba ƙaramar ruɗewa Nasreen ta yi ba, nan ta saki ledar kayan dake hannunta a ƙasa ta isa gun da sauri tana faɗar "Yaaya me ya same ki? Yaushe kika ji ciwo? Ƙalau fa na bar ki ɗazu."

Sabreen bata ce da ita komai ba sai murmushi da ta yi, Umma ce ma ke ƙoƙarin kwantarwa da Nasreen ɗin hankali a kan cewa ba komai za ta wartsake da yardar Allah.

Har Nasreen ta buɗi baki za ta yi magana, Abba ya turo ƙofar bakinsa ɗauke da Sallama,su ka amsa ya shigo.

Kayan aikin ya fiddo tare da gyara mata gurin ciwon, ya bata pain reliever ta sha sannan ya fice, da ya fita ne ya kira mai gyaran karaya domin a dubata a gani ko ta samu gocewar ƙashi ne, saboda ya lura da yanda take takawa daƙyar, alamar ta ji ciwo a ƙafarta.

©©©©©©©©©

Jalila kuwa ta na can ta yi nisa acikin ƙudurinta na son mallakar Asim, musamman da ta ga ta yi nasarar raba tsakanin su, yanzu ba ta da burin da ya wuce ta gan ta a gidan Asim, tana ganin lokaci ya yi da za ta fito da maitarta a fili, saboda haka ta ɗauki waya ta tura masa text kamar haka:

Aminci ya tabbata a gareka sahibin rayuwata, ka sani na yi nisa a cikin kogin ƙaunarka, na yi nitso da linƙaya ta yadda ba na tunanin zan iya fitowa daga wannan kogin ba tare da tallafinka ba, a taƙaice dai ina matuƙar sonka, ina so ka samar mana lokacin da za mu haɗu ga-da-ga domin na tabbatar ma da yawan ƙaunar da nake maka.
Mai ƙaunarka Jalisim.

Tana gama turawa ta fice daga gidan, domin lokacinta ya yi na zuwa gidansu Sabreen don kwaso rahoto.

Ko da ta je ta tarad da Sabreen kwance, har mai dorin ya gama mata gyaran ƙashin ya fita, da yake ta samu gocewa a ƙafarta ta dama.

Kallon Sabreen ta yi a burkice ta ce "Subhanallah! Tawan me ya same ki ne haka? " Matsawa ta yi kusa da Sabreen ɗin ta zauna a ƙasa, kusa da ƙafarta ta na ƙarewa Sabreen ɗin kallo, ganin yanda ta ƙara ramewa ta zabge, ita bata ma taɓa lura da wannan muguwar ramar da ƙawar tata ta yi ba sai yanzu.

Ɗago kanta ta yi ta dubi Sabreen ta na mata sannu.

Kaɗa kai kawai Sabreen ta yi alamar amsawa, ta fara lumshe ido alamun barci, ta na jin lokacin da Jalila ke tambayarta "garin yaya kika ji wannan ciwon?"

Rufe idonta ta yi ta lafe luf a kan kujerar ko dogon motsi ba ta yi, alamun dai ta yi barci, alhali ba barcin ta ke ba, wannan tambayar ta banza ce ba za ta iya amsawa ba.

Duk yanda Jalila ta kai da son gulma a haka ta haƙura, ta tafi cike da takaici, ganin ba amsa za ta samu ba, don ko da ta tambayi Nasreen ma cewa ta yi ita ma bata sani ba.

©©©©©©©©

Da misalin ƙarfe 5:30 Asim ya fito daga banɗaki ɗaure da towel a jikinsa, ruwa na ɗiga a jikin nasa alamun daga wanka ya fito kenan,
har yanzu ba walwala a tare da shi, ya zo zai wuce ta gaban Mirrow kenan, ya ji ƙarar shigowar saƙo a wayarsa dake kan Mirrown, ɗaukowa ya yi don ganin ko waye kuma me a ka turo.

Ganin baƙuwar number ne yasa ya mayar da wayar da zimmar ajiyewa, kuma sai ya tuna cewa ashe fa ya goge lambar Sabreen, don haka ya yi saurin dawo da wayar saitin fuskarsa ya fara karanta saƙon ya na murmushi, a tunaninsa ko Babynsa ce ta turo, sai da ya je ƙarshen saƙon ya ja wani uban tsaki, nan take ransa ya mugun ɓaci zuciyarsa ta harzuƙa, ya ga ba zai iya ƙyalewa ba.

A bayyane ya ce "Yau zan kawo ƙarshen wannan iskancin na ki, wato kin ga ba na tamkawa shiyasa kika samu sake har haka koh?"

Ya na gama faɗa ya isa bakin kujerar gefen gadonsa ya zauna, ya fara rubuta mata amsa kamar haka:

"Wai ke mahaukaciyar ina ce?, Duk saƙunan da kike turowa ban taɓa ba ki amsa ba, ya kamata ki fahimci cewa ba kya tsarina, amma da yake ke jaka ce mara aji hakan bai sa kin haƙura ba, to koma wacece ke ina mai tabbatar miki da ki fita harka ta, domin tuni zuciyata ta yi zaɓin da ba nadama a ciki, idan ma da saka hannunki a cikin tarwatse farincikina, to ina miki Albishir da cewa kun yi nasara a zahiri, amma kuma a baɗini asara kuka tafka, domin har gobe har jibi ni na Sabreen ne, ina ji kamar an halicce ni ne don ita kawai, don haka ko zan ƙare rayuwata a haka ba aure, tabbas ba zan auri wata in ba ita ba, idan ma na rayun kenan."

Ya na gamawa ya tura mata tare da saka hannunsa cikin sumar kansa ya fara yamutsawa, sai huci ya ke.

Turo ƙofar da a ka yi ne ya saka ya ɗago don ganin ko waye ya shigo masa ɗaki a dai-dai wannan lokacin da yafi sha'awar ƙadaici fiye da komai.

Mom ce ta ƙaraso ciki ta na faɗar "Subhanallah! Asim me ke damunka ne?"

Ganin ya yi shiru ba amsa yasa ta ɗora da cewa "Na ji shirun ya yi yawa ne, tun da ka fice baka dawo ba, ga shi ban ji shigowarka ba, shiyasa na hauro sama don na duba ko ka dawo."

Nan ma shiru ya yi yana saurarenta har ta kammala bayaninta.

Ganin ba ya da niyyar yin magana yasa ta dube shi fuskarta cike da damuwa ta ce "Don girman Allah ka faɗa mun, wace damuwa ce wannan ta hanamin yaro sukuni a kwanakin nan?, ko ba komai zan taya ka da addu'a ai."

Cikin sarƙaƙƙiyar murya ya ce "Mom na shiga ukuna, shikenan na rasa ta garin jiran lokacin da banzan burina zai cika, Mom sun bawa wani ita, wanin ma wanda na fi tsana a duniya."

Hannun mahaifiyar tasa ya kama ya ɗora akan ƙirjinsa ya na faɗar "Mom kin ji ko? kin ji yanda zuciyata ke bugawa da ƙarfi ko? Ina tabbatar miki da cewa kina daf da rasa ni, domin a na ɗaura auren Sabreen mutuwa zan yi Mom, ba zan iya jura ba."

Hankalin mom in yayi dubu ya tashi, ganin yanda yaron nata ya burkice ya saka ta tabbatar ba wasa a wannan lamarin.

Lallashinsa ta shiga yi da maganganu masu kwantar da hankali, ta ce "Ka yi haƙuri yarona insha'allah ba za ka rasa ta ba, bari dadynka ya dawo ai tun da har ba a riga an ɗaura auren ba insha'allah komai zai zo da sauki."

Da ire-iren waɗannan kalaman ta samu ta ciyo kansa ya ɗan nutsu, sannan ta fice daga ɗakin cike da damuwa.

©©©©©©
Lily kuwa ya zage sai shirye-shiryen aure ya ke, tuni ya saka a ka cigita masa gidan haya mai kyau a Kano, domin a can za su fara zama har zuwa lokacin da za ta kammala karatunta.

Ko da Umma ta gaya masa rashin lafiyar Amaryar tasa, ya damu sosai a zahiri da baɗini don haka ya kasa zama sai da ya zo Kano don dubiya....

Follow me on Wattpad @ummu inteesar

Vote, share &
Comment




UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now