Kuka yaci mugun k'arfinsa, Ummi Sai nanata kalmar _inalillahi_ take tayi, Zuciyarta na bugawa dasauri dasauri, Tuni hawaye masu radad'i ya wanke mata fuska, Wai itace keda hawan jini?Tayaya ma ta bari hakan ya faru?Tasan Tunaninsa ne ya jawo mata hakan, bata tab'a bayyanawa kowa damuwarta ba balle tadan samu sassauci ah Zuciyarta.Babu Wanda keda alhakin ciwonta kamar yadda Abba keta fadi da babbar murya face ita.Itace Silar Ciwonta ba kowa ba.

Share Hawaye tayi tana mai k'wakulo murmushin dole, Cikin kwantar da hankali tace"Haba Abbana menene kake fadi haka Wanda kwata kwata babu dadin ji?kamanta cewa ciwo, Mutuwa da duk komi ma daga Allah ne suke?Meyasa kake daura al'amarin ciwona akanka Kacokam?meyasa bakayi tunanin cewa ai Wannan yana cikin jarabawata arayuwa ba sa'annan ka tayani addu'ar Allah yasa in cinyeta ba?"

Ta dauki lokaci sosai tana ankarar dashi har dai ya gamsu, Ammh yadau alk'awari daga yau yabar bawa su ummah damar wulakantasa masa ita, Zai zaburar dasu fiye da Zatonta.Kuma ya k'wabeta akan karta kuskura ta fadawa kowa tana da Wannan ciwon don dariya ne za'ai musu.

Ai kuwa da isarsu gida ya rufesu da fad'a, Sunsha mamaki kwarai da gaske don ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, yace"Duk wacce ta sake matsawa Ummi saina bata mamaki, Wallahi nayi rantsuwa kuma bazanyi kaffarah ba ko Ciwon kai wani ya sakata acikin gidan nan Sai yabarmun gidana awannan ranar...."

Babu Wacce tace dashi ci kanka don duk Sun tsorata da yanayinsa, Ya kuma rabawa kowa aikinsa agidan, daga yanzu baza'a dunga tuttulawa Ummi aiki ita kadai ba, Yace kuma daga yanzu zaisa idanu sosai yaga iya gudun ruwan mutum.

*     *      *

"Antynah ina matuk'ar bukatar Wannan yarinyar acikin duniyata, Ki sani ita kadai Zuciyata keso, bazan iya gutsirawa Suhailah Soyayyarta ba, Dan Allah Anty Mamu ki Shirya Zuwa gobe muje ki tayani fahimtar da Mom, Tayi hakuri karta Shiga hakk'ina, Ta tuna fa mu ya'ya amana ne Allah ya basu, don haka basu kadai keda hakk'i akanmu ba, muma muna dashi akansu, Anty Mamu wlh ko za'ai ruwa ayi tsaki ne bazan tab'a auran Suhailah ba, gwara in mutu babu auran....."

Girgiza kai tayi tana fadin"Abdulhameed wlh ka fiye taurin kai, Ni matsalata dakai ba'a isa abaka shawara ka karbeshi da hannu bibbiyu ba, Kafi son akodayaushe abaka goyon baya kan abunda ranka keso, Ni abunda nakeso ka gane shine, Tun kana karaminka Su Momy ke maka duk Wani abinda kakeso Wanda zai faranta ranka, basu tab'a gazawa ba haka kuma basu tab'a hana maka abunda ran naka keso ba.Akaron Farko Momy ta nemi wani abu awajenka ammh kana neman watsa mata k'asa a ido, Kai tsaye ka nuna mata cewa kwata kwata bata isa ba, Hameed kaje ka nemi gafarar Mahaifiyarka, sa'annan kayi hakuri kayi mata abunda takeso muddin kana son ka cigaba da ganin daidai arayuwarka, Wannan shine shawarar dazan iya baka, in kaga zaka iya yin aiki dashi fine, in kuma kaga a'ah bazaka iya ba to Wannan ruwanka, ni dai na gama magana.."

Shiru yayi mata yana Tunani, yana ta cizar leb'e kamar zaya hudashi, sai ga Dad ya kira ta layinta don basu Tashi meeting da Wuri ba, Kuma koda Suka tashin Masallaci ya nufa, Sai da aka idar da isha'i ya shigo Gida neman Hameed be gansa ba, Fareed ma ya nuna bai san inda ya shiga ba, Murmushi Dad yayi yace"Ni nasan inda Za'a Sameshi."

Wayarsa ya shiga nema ammh akashe don har zuwa wannan lokacin yaki kunna wayarsa don bayason Takura.Kai tsaye Dad ya nemo Mamu.Bayan sun gaisa yake cewa"Hameed yana wajenki ko?"

"Eh! Dad gashinan ma bai Wani jima da shigowa ba, halan bai sanar muku da tahowarsa bane?"
"Ke kuwa ina zai Sanar mana da fitarsa gudun karmu hanashi Zuwa ganin Uwarsa?"

Murmushi ta d'an saki kasa kasa Tana duban Hameed kan tace"Dad ayi hakuri, wlhy nima saida na masa fadar fitowa ah irin Wannan lokacin, Kuma ni ban ma san da cewa bai sanar daku ba, ammh kuyi hakuri Zan masa fada bazai kuma ba insha Allah, and he is Safe here, Kona bashi wayar ne..?"

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now