A nan ya shiga zayyanowa Ashik duk abinda ya faru.

Dariya sosai Ashik ya yi sannan ya ce "Cab! Lallai Jalal ka Kuru da na iso nan da wuri, da oga Asim ya tumurmusa ka, domin zai yi abunda yafi wannan ma akan Sabreen."

Da ga haka ya juya ga Asim ya na masa dariya ya ce "Ya haka oga, bayan kun rabu kuma shi ne za ka hana wani ya kula ta? tun da kai ka fasa ka bari mu bawa Jalal ka ga duk ɗaya wai makafi sun yi dare." Ya ƙarashe ya na dariya.

Ba ƙaramin haushi ya bawa Asim ba don haka ko magana bai samu damar yi ba ya juya zuwa inda ya yi parking motarsa, fuskar nan ba fara'a.

Ya fara nisa ya jiyo Ashik na faɗar "Malam idan ka tafi waye zai mai damu ni da amaryata?."

Biris ya yi kamar bai ji ba ya figi motarsa a guje ya bar hotel ɗin.

Dariya sosai Ashik ya shiga yi, ya ja hannun Jalal suka juya zuwa hall ɗin a nan ya ke sanar masa, ai wannan yarinyar budurwar Asim ce tun farko, kuma ya na bala'in kishinta fiye da tunanin mai tunani, don haka ya rufawa kansa asiri, ka da ya bari son ta ya samu muhalli a zuciyarsa, da haka suka koma hall ɗin.

Bayan shuɗewar wa su y'an awanni taron Dinner ya watse, ko da su ka je gidan su amarya sha biyu ta yi, don haka ba su da zaɓi dole su ka kwana a nan, har da Jalila anan ta kwana.

Ta dai kira waya ta sanar da Umma sun yi dare don haka za su kwana.

Washe gari ranar Asabar kenan aka ɗaura auren Ashik da Afrah akan sadaki dubu hamsin, sai dai fatar Allah Ya basu zaman lafiya.

©©©©©©©©©

Bayan wasu y'an kwanaki da gama bikin Afrah ta na zaune a falo da yamma bayan ta dawo daga jami'a, ta  rafka tagumi da duka hannayenta biyu ta na tunanin da ya aure ta a kwanan nan, kamar a mafarki kawai sai ga kiran Lily, wani mugun haushinsa ne ya kamata, da ta tuna duk shi ya janyo mata wannan matsalar.

Da kamar ba za ta ɗaga ba don har kiran ya katse wani ya shigo, kawai sai ta yi tunanin bari ta ɗaga ta gargasa masa magana ko ta huce haushinsa.

A can ɓangaren Lukman ne ya ce "Hello my wife, ya kike na yi missing ɗinki na tsawon lokaci."

Sau ke wayar ta yi tana kallonta baki a buɗe tamkar wata gaula, a ranta ta ce "Ka ji wani sabon iskanci kuma, bayan duk sharrin da ka mun har kana da bakin kirana da Matarka?."

Mayar da wayar ta yi a kunnenta tare da miƙewa ta shige ɗakinsu ta rufe ƙofar don kada Umma ta ji, sannan ta ce "Yanzu Lukman abinda ka mun ka kyauta kenan?"

"Me na miki kuma?" Ya amsa da tambaya.

"Lallai sai yau na tabbatar da halinku na maza, tambaya ma kake kamar baka san komai ba?, To idan ka manta bari na tuna ma, ina magana ne a kan sharrin da ka mun, don girman Allah da yaushe muka yi magana da kai na ce maka na amince da kai? Wai har da cema su Abba na ce kunya na ke ji kada a tambaye ni, yaushe ka zama haka Lukman?"

Shiru Lily ya yi ya na sauraronta cike da mamakin yaushe Sabreen ɗin ta zama fitsararriya haka?

Jin bai ce komai ba yasa ta ɗora da cewa "Tun farko da ka ce ka na so na, na tabbatar maka da cewa ina da wanda na ke so kuma ba zan ji daɗin rayuwa in ba shi ba, amma ka yi biris, shi kenan
tun da ka dage sai ka aure ni na amince zan aure ka don na yiwa iyayena biyayya, amma ka kwana da sanin cewa gangar jikina za ka aura ruhina ya na tare da waninka"

Ta na gama faɗa ta kashe wayar ta cigaba da kukan zucinta, domin har hawayenta sun kusa ƙafewa saboda kuka.

A haka rayuwa ta cigaba da gara mata, har an tsayar da lokacin bikinsu ita da Lily nan da wata biyu masu zuwa.
®®®®®®®%

Abba ne ya fahimci cewa y'ar tasa ta na cikin wani mawuyacin hali, da alama damuwa ta gama samun matsugunni a zuciyarta.

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now