page 31

98 7 2
                                    

❤️💛💔💛❤️💛
         ❤️💛❤️
        ✨✨✨

*RIKICIN MASOYA*
           *(Masoyan gaskiya)*

❤️💛💔💛❤️💛
          ❤️💛❤️
         ✨✨✨

*WRITTEN BY:*

*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*A SANADIN KAMA*

              *AND NOW*
           *RIKICIN MASOYA*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHI RAHMANIR-RAHIM*

✨✨ page 3️⃣1️⃣

Washe gari tun 12 na rana Sabreen ta fice daga gida zuwa gidan su Afrah, duk da ta na cikin damuwa hakan bai hana ta yiwa ƙawar tata duk wata kara da ta kamata ba, yau ma tafiyarta ta yi ba tare da ta nemi Jalila ba.

Asim ma haka ya dage ya shige cikin abokanansu a na ta hidima,tun bayan dawowarsa asibiti, ya tare gidan su Ashik saboda acewarsa yawon zai masa yawa ne.

Bayan isha'i a ka shirya amarya Afrah don zuwa gun Dinner, y'an matan Amarya ma suka shirya cikin ankonsu na Dinner yadi ne kalar pink wanda suka yi iya su shida kawai ƙawayen Amarya, sauran mutanen bikin kuwa ankon su kalar dark blue ne.

A tare suka fito ita da ƙawayenta fuskokinsu sun sha make-up masha'allah sun yi kyau sosai, barin ma Sabreen da kwalliyar ta zaunawa sosai a fuska tamkar ma ita ce amaryar, duk da cewa fuskarta ba walwala hakan bai hana ta yin kyau ba.

Ranar ma kamar lokacin bikin Zee, har ta ɗauko wani katon mayafi pink za ta saka, su Lubna su ka ƙwace su na faɗar "To matar liman, yau ko ke ce masallaci gaba ɗaya ba za ki saka mayafi ba yasin."

Sakin baki ta yi ta na kallonsu ta so ta yi magana,amma sai ta yi shiru ganin a na ta sauri za a fice don motocin sun riga sun zo.

A haka a ka ɗebe su har bakin hall ɗin da za a yi Dinner a ciki, suka fir-fito zuwa ciki, yayin da amarya da ango su ke zaune a mota su biyu kawai yayin da Asim ya zama direban motar, domin kuwa Ashik cewa ya yi ba zai shiga tuƙin kowa ba sai na sa, saboda yau dole ne ya biya shi ladan mayar da shi direba da ya yi duk lokacin da za su je makaranta.
®®®®®®®

Sai bayan kamar minti 20 zuwa 25 da ƙarasowar su sa'annan y'an matan amarya da abokanan ango suka ƙara so gun don masu iso zuwa ciki.

A tare suka fito zuwa ciki gefe ɗaya y'an matan amarya ne su shida gefe ɗaya abokanan ango su shida.

Amarya da ango ne a gaba sun haɗu cikin shiga kala ɗaya, amarya ta sha doguwar rigar yadi peach wacce ta sha haɗaɗɗen ɗinki, an ɗaura mata brown head akai, tun daga kan yarinta har takalmin ƙafarta kalar brown ne.

Shi ma ango ya wanku acikin wani haɗaɗɗen yadi peach colour, ya sha hula wacce ta ji aikin zare brown, hakama takalminsa kalar ne sai zuba ƙamshi su ke su ka ratso gun dama abin ka da haɗin fararen fata.

Asim ne a sahun gaba ta bangaren ango,yayinda Sabreen ke sahun gaba ta bangaren Amarya sai harbawa ƙirjinta ke yi tunda suka shigo gun ta rasa dalili.

Daga ita har shi ba wanda ya lura da wani acikinsu saboda dukkanninsu hankalinsu baya gun, kowanne su damuwa ta yi masa yawa a zuci.

A haka suka ƙarasa filin sai kiɗa ke tashi, kamar hall ɗin zai tsage, y'an matan na taku a hankali.

RIKICIN MASOYAWhere stories live. Discover now