BUTULU... part 32

56 5 0
                                    

💫 *DA BAZAR-MU WRITER'S ASSOCIATION*💫
    
    We are here to make you happy .....smile, educated amd to realized that we are the best among all...... *DA BAZAR-MU MUKE TUNQAHO*💃💃💃💃
   
   
                     *BUTULU.....*
   
    *By Maryam Abduul*
   
   
Wattpad@Maryamad856
@Facebook maryam Abduul


*Part.....32*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

        **************Wannan lokutan shi kansa yana mai jin haushin kansa, meyasa ya aikata abinda zai sashi nadama, lallai tabbas Fatima tayi gaskiya da tace" zaiyi danasani" sai dai har yanzu shi kansa yasan baima fara ba domin irin *butulcin* da yamata yasan bai kyauta ba.

   Shine maqasudin wanda ya kawota nan, shiyasan komi nata, bata da kowa sai shi, amma yanzu ya ballagazar da ita yazaiyi yanzu.

  Lallai tabbas dolane ya nemota a duk inda yake, ya zama wajibi ya nemi ya fiyarta.

  

      **********Yanzu haka bikin Fatima ya rage saura wata daya da sati uku, kullum ta Allah sai Hisham ya turomata da second da a wannin da suka rage musu.

Itakam yanzu abin ma nasa ta maidashi haka kawai, kullum addu'a take mai akan Allah ya yaemasa wannan abun, fatan d'aya shine" Allah yasa suna da rabun kasantuwa waje d'aya n da yake ta musu fata" .

    ***********Zaune suke kan tab'arma, Tabawa malam Audu, sai kuma 'ya'yanta da tadawo dasu gidan cikin qarfi da yaji.

     Gabansu wani flet ne shaqe da abinci mai rai da lafiya.

    Malam Audu ne yace" yasin ko larabawa ba sukai ki iya abinciba, ke ki sune suka aureki wllh sunyi dace sosai, kin iya tarairarayar miji ba dai irin waccen shashshar ba ballagaza da ita solo'biyo.
   
    Fari tai da ido kan tace" kai malam fad'i dai gaskiya"
   
    Cikin sauri yace" yo to ai gaskiyar kenan, ni banma iya qarya ba sai dai nayi kuskure aciki barema kuma sam ba wani kuskure a cikin maganata.gaskiyar kenan, ai wllh dai ayi mugani badai maula ba suje suyi tayi wayasani ma ko kudin tsafine akazo za'a binne dasu"
   
    Tabawa tai caraf tace" yo to malam ai mu gaba takaimu daman an kanainayemu an hanamu sakat idan na tsafine ai alhamdulillah kaga sai su had'a dasu ai "
   
    Ba tare da yayi wata maganaba su Ammar suka sako kai cikin gidan tare da sallama abakinsu.
   
    Malam Audu ne kad'ai ya amsa yayinda Tabawa ta d'auke kanta daga garesu.
   
    Zulaihat ce ke riqe da mama Suwaiba, d'aki suka wuce yayinda sukai musu sannu da gida.
   
    Sai da Zulaihat ta dan dad'a gyarawa mama Suwaiba d'akin ta fito tare da qara baiwa Ammar wasu kud'i akan yai wata hidimar.da qyar ya amshe kudin.
   
  Karaf akan idan malam Audu hakan yasashi yin wata qatuwar qwafa.

   Har waje ya rakata ya sakya yiwa amininsa godiya sannan ya juyo gida.
  
  Yana shihowa malam ya qwala mai kira tare da fad'in " ita wannan yarinyar menene ta baka har da wani qunshewa kar agani, amma naga dai kamar ma kud'i ko??"

  Ammar yace" ehh sune catai a siyawa mama magan......"

   "Kai dallah rufen baki, baniso nan yanzu kai ko tausayintama bakaji ta kaika asibiti ta biya kudin komi amma ta dau kudi ta baka kasa hannu ka amsa, baniso nace"

  Cikin marairaicewa Ammar yace" haba baba kai nema fa yakamata ka siya mata, kai yakamata ka mata komi amma kuma an bada zaka amsa"

  " Ehh lallai baka da kunya, ubanwa ye zaiyi komi d'in, kai yakamata kayi komi ai dan ubanka tunda ita ce gyatumarka batawa ba"

Har Ammar ya bud'e baki zai magana Iya ta rafka sallama, wacce ta shigo yanzu daga asibiti take akace an sallamosu shine tayi gidan sai kuma gashi tazo akan ga'ba.

  Ganin yanayin da suke ciki kamar wani abu na faruwa yasata tambayar mke faruwa.

Nan Ammar yashiga zayyana mata abinda ke wakana, yayinda Malam Audu keta zungurarsa akan yai shiru da bakinsa shikam ina yayi nisa.

Jin hakan yasata mugun fusata, nan tashiga Allah wadai da wannan sabuwar d'abi'ar tasa daya 'bullo da ita, tare da nemami shiriya a wajen Allah, nan ta amshe kud'in sukai d'akin mama Suwaiba dan duba jikin nata.

Shikam malam Audu sai surutai yake qasa-qasa, yayinda Tabawa keta faman zugashi akan yaci uban Ammar idan ya damqeshi.

 

  Koda ta shiga d'akin ba laifi jikin nata ya samu relif, nan ta shiga yimata sannu.

  Sai alokacinma Ammar yakejin wai " kayansa na lefe da yake had'awa aka kwashe " wanda shine sanadiyar jinyar mama Suwaiba.

  " Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un " shine kawai abinda yake ta ambata wata zuface ta shiga keto masa.

Shikkenan yanzu ya zaiyi ya rasa kayan da yake had'awa wajen ganin yakaiwa sahibarsa gashi har ya sanar da ita nan da sati d'aya zasu kawo, yanzu ya zaiyi da ransa, amma an cuceshi iya cuta matuqa.

  Ganin halin da yashiga yasa suka hau rarrashinsa tare da bashi baki akan" Allah zai kawo wasu da yatdarsa, ya kwantar da hankalinsa."

  Cikin kuka yace" mama ni ba 'batan kayanba yanzu me zancewa da Affa na shaida mata nan da sati d'aya za'a kawo kaya, yanzu ya zanyi"

  Cikin rud'ewa Inna tace" wace magance haka Ammar me yasa kace mata naga ma bikin da sauran lokaci ko, meyasa zakace za'a kawo lefe bayan kai finma baka gama had'awaba?"

  "Tsautsayi Inna, atunanina idan akaa kai za'a dad'a matso da bikin kusa shiyasa nai haka, nasan nayi lefe amma dan Allah ku yafeni"

  "Bakomi Ammar ai kowa ma yana laifi, amma ka kiyaye gaba, sai kasanar da ita cewa ba yanzuba kan nan Allah ya dad'a horewa ka sai wasu kayan"

  Gyad'a musu kai kawai yai batare da yasakya cewa" uffan ba" amma a zuciyarsa shi kad'ai yasan abinda yakeji.

  Nan ya miqe ya fita daga d'akin ba tare da yai magana ba, suma binsa kawai sukai da ido tare da tausaya masa halin da ya shiga, tabbas an cuceshi iya cuta matuqa, kuma suna mai tayashi addu'a akan " Allah ya sakamishi"

  

  
       ***************Qarar wayarsa ce ta dameshi tun d'azu take ruri hakan yasashi saurin miqewa ya d'akko ta dan kashewa dan ahalin yanzu bai buqatar komi na hayaniya da zaisashi surutu.

Amma ganin no d'in sakatariyarsa yasashi dagawa, batare da yace" komiba"

  "Sir daman d'an kwangilar nan ne yace" lallai yana buqatar ganawa dakai, shine nace bara na sanar maka"

  Shiru yai bai cemata komi ba hakan yasa ta sake maimaiawa a zatanta ko bai jiba " sir dan Allah ka daure kazo ku had'u its inportant issue sir"

  "Is ok Fa'iza na rigada nace miki komi zakiyi ki wakilceni ko, yanzu ma ko dan ba zai gana dake ba to ya iya fatiya mu kuma mu janye alaqar tamu"

Cikin sauri tace" no sir plz kada kai haka, wannan alaqar tana da matuqar anfani, kuma muma zamuci riba sosai akai wacce zata qara habaka Compny d'in plz sir ka daure "

  "0k uwar tsari naji, amma ba zan sami zuwa ki bashi adress dina ya saman agida, bazan iya fitowa ba Fa'iza"

  " sorry sir, yadda kace ayi haka za'ayi" nan ta kashe wayar.tsaki yaja tare da fesar da iskar bakinshi kan yace" useless man kawai"




Tofa readers......za'a baiwa Daddy adress na gidan Abdallah....... Shin zai biyo sawun gidan ko kuwa....yaya Ammar zaiyi zai gayamata gaskiya ko kuwa....ku biyoni dai cikin wannan littafinawa dan jin yazata kaya........




Comment and Share.......


*Mrs.Abduul ce*..........

  
   
  

             BUTULU.....Where stories live. Discover now