Part......71

34 3 2
                                    

  *ZAFAFA WRITERS FORUM*
          Z.W.F.........


        ______BUTULU_______

NA
  MARYAM ABDUL-AZIZ.
       (MAI_K'OSAI).

WATTPAD@MARYAMAD856.

Page........71

Bisimillahir Rahmanir Raheem.

__________Mansur kam ganin mutumin be masa sallama yasa shi kiransa, "nace kodai akwai wata qualliyar ne bansan ba?"
   Ya tambaye shi cike da zolaya.

  Dariya Ammar yai kan yace "wataqila 'kanwarka tayi awan gaba dani zumud'i yasa na kasa nutsuwa har na tsaya muyi sallama".

   Shima dariyar yai kan yace " kun kyauta, to nidai kar a juyan baya"

  Ammar yace " sai dai in ba muzama cingum ba"

  Mansur yace " ku zama ma danqo mai narkewa yabi jiki"

   "Lah! baka saniba ai mun zama"

  Nan suka kwashe da dariya, yayin da Mansur ya nuna farin cikin sa akan wannan lamari tare da musu fatan alkhairi.





            %

Satin Fatima biyu da farfad'owa aka sallamota suka dawo gida, Ammin Hisham taso su zauna gidan ta amma hakan bata samu ba.

  Gidan su Dr. suka yiwa tsinke, yaran kam masha Allah sun fara wayo, dan yanzu watan su biyu cif da zuwa duniyar yayinda Hisham keda wata biyu da rasuwa.

    

         %
Al'amarin Abdallah ba' cewa komi sai dai godiyar ubangiji, zadai kaganshi zaune yai shiru amma da zarar kai masa magana to Fatiman nan ce dai a bakinsa.

  Da 'kyar Daddy yaje ya dubuahi shida Saliha, su kansu sun ja janta masa irin halin da yake ciki.

   Akace " tsakanin d'a da mahaifi sai Allah, alokacin Daddy kam yaga wautarsa naqin yimasa afuwa akan kuskuren da ya aikata.

   Sunyi magana da likitan dake dubashi, sai dai bayanin d'aya ne dai a gabatar masa da abinda zaisa ya sauya tunaninta wato *FATIMA*.

        %

Zaune take ta idar da sallah, addu'a take tayiwa Hisham d'in ta, dan a yanzu hawayen sun qafe ta daina masa kukan sai dai duk sanda ta tuna to zata masa addu'a.

   Saliha ce ta shigo fuskar nan duk a jume, kamar wacca akayiwa mutuwa haka ta samu waje ta zauna jigum tai tagumi.

    Kallon ta tai kana tace " Saliha meyafaru na ganki haka kamarara lafiya?"

    Sakkowa tai dab da inda take kan tace " Aunty Fatima dan Allah ki yafewa yaya" ta qarasa tamkar zatai kuka.

    Cikin rud'ewa tace " meyafaru Saliha?"

  "Tabbas nasan yaya ya miki ba dai-dai ba amma yanzu yafiyarki itace kawai zata sa yadawo yadda yake, Aunty Fatima yaya ya haukace, baya da hankali yanzu haka yana gidan mahaukata tsawon wata uku"

   "Me? "
Ta fad'a da qarfi, "Abdallahn ne yake gidan mahaukata, akan wane dalili??"

   "Duk sabida ke Aunty Fatima, yaya yayi nadama wacca hartakai da yayi loosing memory likitoci sunyi iyakacin qoqarinsu amma ba wani cigaba, kowa haka yake cewa " sai kina tare dashi zai dawo hayyacin sa"

    "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu yana can?

  Ta tambaya a kid'ime.

     " ehh yana can"

"Tashi muje " ta fad'a tana me miqewa.

    Miqewa tai ta zira hijab d'in ta, tare da d'aukar  kud'in da zasu hau napep.

   Dabyake Ammi batanan ta yanke shawarar ta fita batare da sanin kowa ba, sai dai suna zuwa falon suka ci karo da Na'ima da Hajiya, da Ammi sun shigo.

    "A'a ina zaku ku kuma haka??" Hajiya ta tambaya.

  "Hajiya zanje duba Abdallah" ta fad'a idanta a qasa.

Kallon-kallo sukai wa junan su, murmusawa Hajiya tai kana tace " naso na miki zancan ganin har yanzu jikin naki ba qwari yasa ban ba, amma yanzu shikkenan kuje da Na'ima itama bata jeba daman"

   "To Hajiya nagode " tace.

Tunda suka fito Na'ima bata ce musu uffam ba, hasalima haushin Teemahn takeyi duk irin rashin adalcin da ya mata shine batai zuciya har da wani cewa dubashi zataje yi, to ya mutu man .

    Sanda sukaje ba lokacin ziyara bane, amma Jin cewa "Fatiman da ake taso ta kawo masa ziyara nev

             BUTULU.....Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz