Part......61&62

69 7 3
                                    


    *ZAFAFA WRITERS FORUM*
               Z.W.F........


       _______BUTULU_______



       NA
MARYAM ABDUL-AZIZ.
   (MAI_K'OSAI).






  WATTPAD@MARYAMAD856.


Page.....61%62


Bisimillahir Rahmanir Raheem.




_________Malam Audu ne kwance ba lafiya, tun bayan tafiyar Ammar abubuwa suketa faruwa, ciki kwa harda bayyanar gaskiyar wadanda suka kwashewa Ammar kayan lefe, Wanda hakan ya faru ne sanadin kama Taga da 'yan sanda   su kazo yi anan komi ya faru.

   Yayinda abubuwa marasa dadi suke ta faruwa, har rashin lafiyar da Malam din ya kwanta, wanda sam Tabawa taqi kula dashi acewar ta bazai zame mata " jangwalgwal ba"

    Inda Mama Suwaiba ce ke ma zaman jinyarsa, kullum addu'ar ta d'aya " Allah ya tashi kafadunsa"

   Sai dai duk da hakan ,Tabawa bata fasa Tata rashin mutuncin ta ba, wanda sanadin hakan ke taqara rura zuciyar malam, lamarin dai sai dai muce "Allah ya kyauta".


    
   %

'Bangaren su Dr. kuwa sosai suka samu fahimtar junan su, duk da cewa har yanzun basu tare ba, amma zama na musamman Dr. yai da Na'ima, nan kowa ya fahimce d'an uwansa.

   Da dafari Sanda Fatima ta bijiro mai da buqatar ta ,yaso qin hakan, amma yanzu yana matuqar godewa Allah da yasa yasani Na'ima a matsayinka matar auren sa, duk da cewa basu tare d'in ba ,amma ko a haka yana yabawa da irin qaunar da take nuna masa, da kuma kulawar da yake samu daga wajenta.

   Shi yasa shima yake ta fafutukar ganin ya kyautata mata, fiye da yadda take masa.

      %

Riga da wando ne a jikinta wato English wears, wandon baqi ne sai rigar milk da ratsin baqi ajiki.

  Ta gyara kanta, inda ta zuba masa kyawawan robons , Saida ta tabbatar ta kammala komi sannan ta janyo littafin da Na'ima ta ba ta ta soma karantawa, Dan Hisham bayanan yaje gidan su.

   Bata Jima da fara karatun ba taji knocking d'in k'ofar shigowa falon nata.

   Ajjiye littafina tai, ta sanya hijab ta mik'e, tana bud'e k'ofar ta ci karo da shi.

    Sanyayyen murmushi ya sakar mata, tare da sake mata lallausan kiss a kumatun ta Wanda batai tsammanin saba, duk yana ta qoqarin sabar mata da hakan, yana so sunbatar tasa ta zame mata sabon ta.

    "Ina fatan dai baza'a ce Na fiye naci ba, dan daga fita ta sai dawowa kuma" ya fad'a yana me sauke mata idanuwansa a kanta.

  Murmushi tai kana tace " haba dai, ai idanuwa na basa gajiya da ganin kyakkyawar fuskar ka, balle su ce sun gajiya da ganin ka"

  Har ya bud'e baki zai magana ta dakatar dashi ta hanyar cewa " muje ka watsa ruwa, sai kaci abinci"

    "Duk yadda kika ranki shi dad'e"

   Saida ya kammala shirinsa tsaf tare da sauya kayan sa zuwa qananun kaya shima , sannan ya sakko k'asan Dan bawa cikin sa hakkin sa.


        %
Har ya wuce k'ofar kitchen d'in ya dawo da sauri,cikin hanzari ya shiga mutsttsike idanuwansa da abinda ya gani, lallai ba shakka itance sanye da dogowar Riga, tayi kyau da ita tayi fresh kai bakace itance da sani ba abaya.

      Ciki da fara'a yace " Fatima, ashe daman zaki dawo gareni, ashe daman haryanzun kina sona, amma kike kokarin Bari a rabamu, meyasa kika azabtar dani"

             BUTULU.....Onde as histórias ganham vida. Descobre agora