Butulu.....8-9

178 7 1
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
   〰〰〰
        

Story...writing by

*Maryam Abdul*

Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all..
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

   
   Masoyana ina matu'kar ALFAHARI DAKU sosai da sosai.

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
     *BIYAYYAH*

*page...8-9*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

-------'Bangaren Abdallah kuwa bayan ya kori Fatima daga gidansa ko d'ar baiyiba, Dan kwa Sam bawata nadama agareshi.

Bayan kwana uku da wannan batunne yasami jonewa da wata budurwarsa...mai suna *LATIFA* daman ta dad'e yana so ta bashi had'in kai amma baisamuba.

Itama d'in bawai Dan bata sonshi bane ba a'a kawai dai tana yimai yawo da hankaline.

*LATIFA* yarinyace ga Alhj.Mala     shahararran mai kud'ine shi sosai yayi fice Dan ko ina kake kace Alhj.    kake nema za'a kawoka har gidansa kuma kowa yasanshi.

Matansa biyu Hajiya Karima itace matarsa ta farko kusan shekararsu goma shadaya kafin Allah ya basu LATIFA alokacinne kuma ya 'karo aure inda ya aure hajila Laila saidai ita haryanzu batasami haihuwaba.

Kusan kullum sai Hajiya Karima sai tayi Allah wadai da halin da LATIFA ta jefa kanta aciki , saidai in ta tuna Wanda yai ummul aba'isin hakan sai taji zuciyarta na mata ba dad'i.

Dan Alhj.Mala  Sosai ya sangarta 'yarsa acewarsa ita kad'ai gareshi Dan haka dole yai mata abunda takeso.wannan dalilin me yasa LATIFA mugun sangarcewa.

Batajin maganar kowa ciki kwa harda iyayen nata, Sam LATIFA bata da wani halin kirki....ko kad'an.

LATIFA tan'kwararriyar 'yar bariki ce, Dan ba club d'in daba tazuwa...har hotel take kamawa Dan wani sa'in bata kwana a gidansu ma...wannnan hali da take ciki yasa kullum Hajiya Karima sai tayi tir dashi har 'kwallar tausayawa rayuwar 'yartata takeyi.

LATIFA nada saurayi mai suna *BASH* asalin sunansa Bashir Ishaq. Shima d'in ta'kadiren kansane sosai, kuma sunason junansu sosai da sosai.saidai Bash talakane sosai, wannan yasa latifa komawa talaka a wajen iyayen Bash Dan sunce" Sam bazai aure 'yar masu kud'i ba gwara tun wuri yanemi dai-dai dashi" wannan dalilin ne yasa LATIFA sauyawa daga 'yar masu kud'i zuwa 'yar talaka a wajen iyayensa.

LATIFA ta had'u da Abdallah ne wajen ciro kud'i...lokacin ATM d'inta ya ma'kale shine Abdallah ya temaka mata.wannan temako shine yazama sanadiyar son Abdallah acikin zuciyar latifa.tun daga wannan lokacin ta fara fafutukar neman soyayyarsa amma batare da tabari yasaniba saida tasa yaranta yaimata binciki sosai akansa.nan ta fara shiga duk wani motsi na rayuwarsa takan kirashi tacemai" kawai takirane su gaisa tare da sakya mi'ka godiyarta " irin wannan abubuwanne yasa har ya fara buye mata idan tai kwana biyu bata kiraba zai kirata su gaisa.

Itakam latifa bawai tanason Abdallah neba kawai har zuciyara a'a saidan kawai yaba kyansa datai da kuma cimma muradinta akansa wannan dalilin ne yasa take sonshi...amma ayadda ta lura shiba mai harkar banza bane...tasan muddun inba ta hanyar aurensaba bazata samu cika wannan muradin nataba...hakan yasa har sa'bani suka samu da Bash...saidai have n tacemai" badan komi takeain Abdallah ba sai Dan kudinsa tanaso kawai ta kwaso musu nairane yadda basai tayi anfani da kudin dad d'in taba, kuma tanason ta kafamasa jari" wannan maganganu da latifa taiwa Bash shiya ya Dan faranta ransabdan duk duniya ba'abinda yafiso sama da kud'i, amma yana 'kyashin yaga Latifansa na harka da wani.

             BUTULU.....Où les histoires vivent. Découvrez maintenant