BUTULU...part 37&38

33 2 0
                                    

      *BUTULU......*

By
   *Maryam Abdul'aziz*
           (Maryam Abduul)

Wattpad @Maryamad856

   Part....37&38

.............Layin wayarta ya soma Kira sai dai matsalar network ya Hana su sameta, ganin hakan yasa Sabir cewa"ya bashi address nata" shi zaije inda take.

DA haka suka rabu kan zaije duk yadda ake ciki inya dawo yaji.

    ..........Ammar ne jingine jikin wani qarfe da tayiwa qofar wani gida kariya, yafi munyi ashirin a tsaye duk da yaron da ya tura yace mishi" tana zuwa" amma shiru kamar anshuka makani.

Mord'a qofar akai tare dasanyo qafafunta, tsaki taja kan tace" me ya kawoka gidan nan?"

Fuskar sa d'auke da murmushi yace" Naje gidanku bakya nan Na Kira wayarki bakya d'auka ,nasan bazaki wuce nan ba shiyasa nace......"

" Dakata Malam" ta katseshi cikin sauri tare da d'aga mai hannu. Na dad'e da karb'e zuciyata daga wajenka domin a yanzu Na tabbatar da cewa "kaid'in mayaudarine" domin ka yaudaran da za'a kawo kaya amma ka shuka iyayena sabida rashin sanin halacci Dana maka, daman ance min halinku NE matsiyata amusu dare suyiwa mutum rana,"

  Murmushi yai a karo Na biyu kan yace" tsaya mana Affa ya kamata kiji uzurina ai koba komi sai ka yanken hukunchin da duk ya kamata"

  "Ai ni Affa BAKA da ABINDA zakace min domin iya cutuwa ka cutar Dani"

"Naji amma duk da haka yakamata kiban dama kiji uzuri Na ko ba....."

"Indai sai Affa taji uzurinka to har abada ba zaka taba fad'ar uzurirrikanka ba"

Cikin sauri ta juya zata koma zuciyarta Na mata zafi, saidai tsinkayo muryar mace Na sallama yasa ta d'an tsahirtawa.

Bata amsa sallamar ba illa Kawai Ammar da ya amsa, kan ya dire amsawar yarinyar ta d'ora da fad'in " tsohon mayaudari, nan dinma kazo kayi wata sabiwar yaudararne?

Cak Affa da Ammar SUKA dai-daita tsayuwarsu ,yayinda Ammar ke binta da kallon tuhuma, wace ita, meye had'in ta dashi?"

Cikin rashin fahimta yace " wace ke daga ina kuma, a ina kika sanni?"

Dariya Tai game da tafawa kan tace" lallai tsohon kilalki kar kace BAKA sanni ba, sabida kayi sabiwar baby, tunda kaci moriyar ganga ka yada qwallo mana, to Na rantse ka jira kiran koto da gaggawa"

Ta qarasa fada tana me qoqarin barin wajen .cikin zafin nama Affa da riqo hannunta tare da tambayarta "wace ke"

Dariya buduruwar Tai kan tace" au be sanar dake cewa "ya ta'ba zaluntar wataba, wannan da kike gani *BUTULU* ne kuma azzalumi mayaudari, ya cutar Dani inda ya dirkamin ciki kuma yatafi ya barni, yanzu haka cikin watansa biyu, amma kinji yace" be sanniba sabida kuna tare"

Sosai Kalmar ta dakesu su duka biyum musamman Ammar da tunda yake be ta'ba koda riqe hannun maceba amma shine ake cewa"yayi ciki" innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.

"Wllh Affa so ake Kawai arabamu kada ki yarda Dan Allah ban ta ba aikata zina Na rantse miki?

" Dallah yimin shiru, daga Yau Babu ni Babu kai, kudinka ka turo a amsar maka kaji ko, " tana gama fadin haka Tai ciki a guje .

Shikam kasa motsa qafarsa yai daga inda yake tsaye, Abu daya yasani"tabbas wannan SHARRIN maqiyane, to su waye?

Idonsa jajir ya kalleta yace" Wllh duk kalma daya da kika fadi Kaine bana yafiyarta har sai Randa Allah ya FIDDA min da haqqina" yagama fada yabar wajen cikin sauri.

Ta'be bakitai "yota Allah Na tuba wannan ai ba saban Abu bane a wajena" ta kwashe da dariya.

    ......Shirye shirye ake tayi Dan bikin Fatima ya matso sosai, ita dai bakaso ake wani hidima akan bikin ta ba amma ganin yadda su Na'ima da Salma suka dage yasa ta sakar musu linzamin komi.

Hatta Hisham tattarashi Tai gefe ta ajjiye, duk yanzu kusan fushi yake da ita kuma batajin dadin hakan, badan komi ba sai Dan Kawai yace" za'ai events hudu"  tace"a'a " shine fa ya hau sama da ita.

   Aunty Jamila ma tazo ita da ahlinta, GYARA akewa Fatima kamar ba gobe, ita dai bataso hakan ba amma ba yadda zatayi.Dan aganinta aure Na biyu zata mai mezaisa aita wani yimata gyaran amare ita da ba amarya ba ,zafa tayi auren NE amatsayinta Na bazawara.


     .......Granny ce zaune ita da Saliha kallonta Tai kan tace" inaji gabana na faduwa, wani 'bangare kuma inajin dad'i da annushuwa, bansan daliliba amma ina fata ubangiji yasa lfy kuma alkhairi ne"

  "Wllh granny kamar kinsan abinda ke zuciyata, kin rigani a fili Na rigaki a zuciya, tun jiya nakejina wani iri ba kuzari, gaba daya sai Na dinga Jin faduwar gaba, bansan meyasaba?". Saliha ta fad'a.

  "Insha Allahu alkkhairi ne" granny tace.

   Aunty Zubaida CE ta shigo falon granny, duk da kusan kwananta hud'u bata shigoba balle ta tuntubi granny ko tana lfy lau.

  Ko kallon inda batai ba ta neme guri ta zauna, tare da d'ora qafa d'aya kan d'aya tana latsa remote alamar chanza tasha takeson yi kuma da gayya.

  "Haba Mama wannan ai sai......" Saliha take qoqarin magana.

  Cikin zafin azama granny ta katseta ta hanyar d'aga mata hannu alamar Tai shiru.

  Aunty Zubaida da tsaurin Ido kam chatai" gwamma da kika dakatar da gwal d'in, amma Wllh ayi hlgaggawar fitomin da d'a na, in bahakaba ba hmmmm" Tai qwafa tare da dire remote d'in ta bar falon. Wanda daman ABINDA ya kawota kenan(nace).

  Wani zafi Saliha taji zuciyarta nayi, ta rasa yadda zata bullowa da Mamar Tata, kallon granny Tai da nufin bata haquri, ta d'ora MATA yatsa abaki alamar shiru.

 
 

             BUTULU.....Where stories live. Discover now