BUTULU.... Part..26

79 4 2
                                    

*BUTULU*

By
   *Maryam Abduul*

*wattpad@maryamad856*

💫 *DA BAZAR-MU WRITERS ASSOCIATION.*💫

Sadaukarwa gareku *BUTULU FANS*

*Part......26*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

************A gajiye ya shigo gidan wata muguwar yinwa yakeji sosai gashi bai samu ya wuce wajen Baba Ladidi ba.kai tsaye dinning ya nufa wayam yagani ba komi akai, kitchen ya wuce nanma wayam da alama dai kamar yadda akasaba ba'a d'ora komiba agidan, bacin sanda zai fita sai da sukai da ita cewa" lallai tayi girki" amma shine taqi.

Qwafa yai ya haye saman, sai dai ga mamakinsa bata gidan "kenan bata daina yawon ba har yanzu?" ya tambaya azuciyarsa.

Lallai ba shakka dole ya d'auki mataki ba zai lamunta da wannan iskancin nataba, fita ba izini ta raina shima gaba d'aya, take wani tunani ya fad'o masa sanda suna tare da Fatima, ko kad'an bata fita konan da qofar gida sai da izinin sa, kobaya gida zata mai waya tace" zata fita" idan bai amince ba kowa bazatanba.

Wannan wace irin rayuwace haka, da wannan tunanin ya fad'a bayi fan watsa ruwa.




.............A wajen su Hisham kuwa sai dai a godewa Allah dan sosai lafiya ta samu, duk wani iya qoqari Fatima nayi nasan ganin lafiyarsa ta inganta, takanyi mai abinci kala-kala ta aikamai dashi.

Kamar yau ma tuwan semovita tamasa da miyar ganye taji naman kaji, qamsheni kad'ai yake tashi.

Duk yadda dr.Auwal yaso tazo sutafi tare abin ya faskara, tunda suka baro asibiti bata wani yin qurin zuwa gidansu ba acewarta" itafa kunya takeji sosai" ba yadda ya iya haka ya qyaleta.

Shikam Hisham yaso ace ta biyosa dan yanzu yana da muradin danyata acikin qwayar idansa. 'Yar wayar da sukema bawani samun fuska yake sosai a wajentaba, dan dazarar sun fara hira ya jefomata maganar kalamai na soyayya to yanzun zata katse kiran, shi abinma tun yana bashi haushi har yasoma bashi dariya.

Koda dr.Auwal yakaimai abincin kamar yadda yasaba haka yadinga zuba loma yana santi, wani sa'in har da yiwa dr. gori wai bai sami meye masa.shikam dr.saidai kawai yai dariya tare da fad'in " kai dai kace kawai gawa taqi rami" daga haka sai su hau hirarsu.




..............Ammar zaune gaban Mama Suwaiba yana zu'be mata atamfofin da ya siyo dan yasoma had'a lefe yanzu.

Sosai tai murna da ganinsu dan wajen kala shida ne, 'yan kud'in da yake sana'arsa yatara da kuma wanda Mansur ke d'an bashi shine ya je ya siyogodewa

Suna haka Tabawa ta sanyo kai cikin d'akin tare da fad'in " to makitsa sai ki fito ai kiwa mutane shara kinbar mana gida kaca-kaca ko dayake halin kenan daman abinda aka gado ai sai dai addu'a "

Kafin Mama Suwaiba tai magana Ammar ya tare nunfashinta da fad'in " duk wani gado da za'ai bai kai gadin baqin hali da zuciya ba"

Cikin azama Tabawa ta qaraso cikin d'akin tare da d'aga hannu zata kai masa mari, caraf Mama Suwaiba ta riqe hannun tare da fad'in " kul wllh idan kina yi ina qyaleki to banda yanzu"

Ganin hakan yasata sauke hannunta tare da yin qwafa zuciyarta na gayamata "a ina tasamu wad'annan atamfofin ?" kana ta fice daga d'akin.

Ammar kam haquri yashiga bawa Mama Suwaiba tare da qara kwantar mata da hankali.



Sai da Ammar yai sati yana had'a kayansa, sannan Mama Suwaiba ta sanar da malam abinda ke faruwa, tare da baje mai kayan dan yagani.

Cikin rashin sa'a kayan suka sauka kan idanun Tabawa, habawa nan fa zuciya taciyota jitake kamar ta banka musu wuta, tana zaune d'an wacce ta tsana zaiyi aure itakuma nata ko oho, ina abinda bazai yiwubane sam.da wannan tunanin ta kima d'akin ta batare da tabari wani ya kula da itaba.

Shikam malam ta'be kawai yai ba tare da yace" qala ba" yai gefe da kayan.itakam Mama Suwaiba na ganin haka ta tattara kayan tai komawarta d'aki  batare da itama tace" masa uffanba ".

Sai dai qasan zuciyarta na mata soya, wato malam bazai ta'ba canzawa ba kenan, kayan d'an ka na aurema bazaka kalla ba balle kasamasa albarka.da wannan tunanin tai kwanciyarta saman katifar dake d'akin.





.........Yau kusan sati d'aya da samun lafiyar Hisham soyayya suke ta zubawa shida Fatimansa ba kama hannun yaro, abin gwanin sha'awa.

Zaune suke cikin mota dawowarsu kenan daga gurin yiwa Basma siyayya, kallonsa tai cikin nutsuwa tace" yakamat acefa ka dakata da wannan d'awainiyar haka, gaskiya"

Had'a rai yai kamar bai ta'ba murmushi ko fara'a afuskartasa ba kan ya kauda kansa gefe kana yace" wai meyasa kike hakane Fatima, nasha gayamiki Basma 'yatace ina da ikin yimata duk abinda nakeso dan haka ki dainamin wannan zance indai bakyasan 'bacin raina"

Cikin sanyin murya tace" shikkenan insha Allahu bazan qara yimawa wata magana akaiba, amma ya kamata ka duba lamarin fa irin wannan kudi da kake kashe mata yakamata kadakatar......"

Cikin salon sa na soyayya ya katse mata maganar da fad'in " wai yaushene za'ace na fito nifa na gaji da wannan yawon akan hanya kullum, inason kasancewa tare dake dan Allah"

Murmushin gefen baki tai dan daman tasan maganar tasa bazat qare ba ba tare da anjefo wannan 'batu ba, kallon 'yan yatsunta tai kan tace" wai me kake cine haka, narigada na gayama lokaci na nan zuwa kadaina gaggawa haka kaji"

Hisham ya kalleta kana yai dariya wacce bazaka jitaba sai dai idan kana kusa dashi, dubanta yasake yi akaro na biyu kan yace" abubuwa dayawa Fatima su nake ci, wanda bazasu ta'ba barina hankalina ya kwantaba, idan baki kaine ga iyayrnki ba an nemamin auten kiba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba, sai nakejin kamar zakimin nisa ko wani ya qwacen ke"

Fatima ta kalleshi tare da sauke ajjiyar zuciya tana jinjina irin san da yake mata, kan tace" shikkenan naji zanyiwa su Hajiya magana abinda suka ce zan gayama inminyi waya, amma ka tabbatar hankalinka ya kwanta fa"

Hisham yai dariya kan yace" yawwa ko kefa, idan wannan ne baki da matsala, girman kujerarki" daga haka suka sauya salon zancen zuwa zallar nuna qauna ga kowannensu.




Fatima kam koda sukai sallama dashi bata tare Ammi da maganar ba sai da ta kammala komi, shima Salma ce tamata jagorar fara gabatar da zancen.

Koda Ammi taji wannan batu sosai tai farin ciki dashi, hakan yasa tace" zataje har gida tasami Hajiya da batun dan jin yadda zai kasance.

Sanda sukai waya da Hisham sosai ya takuramata akan wai ita taje yanzu man, dan yasan Ammi cazatai sanan da gobe ko jibi, da qyar ta lalla'bashi ya rabu da ita.



Idan naga comment ya qaru nima sai na qara yawan typing dan naga kamar bakwasan yin rubutun ne.

Banason sticker ko nagode sharhi kawai nakeso dan Allah....idan baku gyaraba kuma zan tafi ahaka da qarancin typing.


Not edited.....

Vote,
Comment,
Share and Like.....

*Mrs.Abduul ce*✍🏻✍🏻✍🏻

             BUTULU.....Where stories live. Discover now