BUTULU... part 30

56 2 0
                                    

     *BUTULU*

By
*Maryam Abdul'aziz*

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫


*Marubuciyar:*
     *BIYAYYA*

*Part......30*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

    ******************Kamar yadda Hajiyan su Na'ima tace"zata gana da wanda zai tsayawa Fatima, akan batun auren " hakan kwa akai dan sun tattauna komi yayinda suka basu damar zuwa nan da kwana biyu.
   
    Koda ta dawo wayatai ta sanar da Ammi abinda ke faruwa, sosai itama tai murna nan ta labartawa Fatima abinda ake ciki, akan lallai tasanar da saqon zuwa ga Hisham.
   
   
    Koda su Salma sukaji abinda ke wakana murna kamar me, kowa cike yake da farin ciki, dan sun matso suka auren nan.
   
   
   

     To Hisham ma ba'abarshi a baya ba dan suna gama waya da Teemansa ya sanar da Umminsa abinda ke faruwa, nan itama ta sanar da dad dinsa.nan fa suka fara shirye-shiryen zuwa nema masa aure.

      ............Zaune yake a cikin office d'insa sam ya kasa ta'buka komi, yarasa me yake masa dad'i a yanzu.

  Sallama take sai dai sam hankalinsa baya wajenta hakan yasa baisan me ake cewa ba.saida tai qoqarin buga tebur din nasa sannan ya dawo daga duniyar tunanin nasa.

    Kallonta kawai yake amma yakasa cewa" komi" itakam duk da cewa ba wata ce gareshi ba amma kallo d'aya ta masa tasan tabbas yana cikin damuwa domin bata ta'ba ganinsa cikin wannan haliba, sai dai bata da abinda zata iya yi akai wannan sam ba hurumin tabane, hakan yasa taja kujera ta zauna tare da zub'emai takaddu agabansa.
   
   
   
    Fa'iza wacce take sakatariya awajensa, duk wani abu da zai shigo ta wajenta yake shigowa haka zalika yake fita.
   
   
   
    Cikin qarfin hali tace" sir i think something wring with you, can i help u?"
   
   
    Ba tare da ya kalleta ba yace" nothing for me, ki fad'i abinda yakawoki"
   
   
    Jin hakan yasata tsuke bakinta, files d'in ta d'auka tare da fara yimai bayanin yadda sukai, da kuma yadda kasuwancin zai tafi"
   
   
    Sai da ya shafe 'yan sakwanni kan yace" banajin wannan harqallar zatayi, inaso ki sallame kowanne ma'aikaci yanzu bana cikin walwala"
   
   
   
    Cikin firgita tace" haba sir, kasankwa mekake fad'a, idan wata matsalar ce yakamata a zauna ayi solving d'inta, amma ba a rufe company ba, kasane mutane da yawa na anfanuwa dashi wasu dashi suke ci da iyalansu idan aka rufe yazasuyi da ransu, dan Allah sir ka sakya duba lamarin"
   
   
    Tabbas idan maganar gaskiya za'abi to sai tafishi maki, sai dai halin da yake ciki ayanzu baisan mezaice ba, cikin sanyin jiki yace" is alright, amma sai dai komi zai dawo gareki duk wani abu da za'ai yana wuyanki, sannan bana buqatar ganin kowa kowaye ya gana dake, kin fahimta"
   
   
    Gyad'a masa kai tai alamar " ehh"
   
   
    "Zaki iya tafiya" ya fad'a a hankali.hakan yasa tasakai tai ficewarta tare da tattara files d'in tai waje, cikin zuciyarta na masa fatan samun rangwame na quncin da yake ciki.
   
   
    Tana fita ya had'a kai da tebur d'in dake gabansa, nan fa qwaqwalwarsa tashiga saqamai abubuwa da dama.
   
   
   
   
   
   
    ...............Tsiren kwana biyu sukai suka kai ziyara gidansu Hajiya dan aiwatar da nufinsu nasan had'a zuri'a da gidan.
   
   
    Masha Allah sun sami kyakkyawar tar'ba kuma anyi komi cikin mutunci da kamala, yayinda aka tsaida rana wata biyu kacal, dan Hisahm yace" bai buqatar wani dogon lokaci" hakan yasa aka sa wata biyu.
   
   
   
    Hohoho zu kuga murna wajensa jiyake kamar an saukemasa wani qaton abu akansa, a ranar kam sunyi waya tafi aqirga abu kadan zai kirata yace mata" matata, saura kwana nawa, da mintina nawa da second nawa" tun abin na bata dariya har ya koma bata mamaki wai mutum da qirga ranar aurensa.
   
   
   
    Har walima sai da suka shirya wacca dr. ne ya musu wannan gagarunar walimar, anci ansha an gode Allah, yanzu kawai zaman jiran rana ake wacce zasu angwance.
   
   
   
   
    *Dare mahutar bawa*

    ...............Sunan Allah kawia take anbata tare da neman agaji, sai dai ina hakan sam bai samu ba, dominkwa Allah bai amshe roqontaba, sakamakon nasarar da yabawa jibga-jibgan samarin dake dakin nata.

    Da gudu suka fice daga cikin gidan, kai tsaye wani daji suka nufa, nan suka fara ajjiye akwatin dake hannayensu.
   
   
    Wani saurayine wanda bazan iya gane fuskarsaba domin kwa qulle take da baqin qyalle ajiki, dai-dai akwatunan yazo ya tsaya tare da bud'e su.
   
   
    Wata shegiyar dariya ya sake tare da fad'in" yayi kyau, aikin ku ya burgeni sosai"
   
   
    'Daya daga cikin samarin ne yace" ai muda man ba'a samun matsala damu, sai dai abu d'aya tsohowar tamun gardama ne shine na dan maketa da wuqar nan" ya qarasa yana mai nuna mai ita.
   
   
   
    "Ah haba dai amma dai ta mutu ko?" ya tambaya.
   
   
    "No baba kawai dai ta sumane , amma banda tabbacin ta mutu"
   
   
    "Ai da kasani ka sheqe shegiya, dan ba Tsohowa ta bace ai"
   
   
    Ya d'ora da fad'in" bakomi hakan ma yayi, ko banza tayi jinya ai"
   
   
    Nan ya bud'e wata jaka ya zaro kud'i ya miqawa saurayin, kar'ba yai kan yace" kuzo muware" nan suka mara masa baya.
   
   
    Suna tafiya ya kwance qyallen tare da sheqewa da wata iriyar dariya," yaro-yaro ne bai san wuta ba sai ya taka, ai sai ayi auren mugane ko" nan ya sa'be akwatun nan guda uku aka yabar wajen da sauri-sauri.
   
   
   
   
   
    Gari na wayewa Ammar yashigo cikin gidan dan yau sam ba'a gida ya kwanaba, kai tsaye d'akin Mama Suwaiba ya nufa sai dai me cikin tashin hankali ya fito ya nufi d'akin Tabawa tare da buga mata qofa kamar zai 'balla qyauran.
   
   
   
   
   
    Tofa!!! Ammar me ya faru......? Su waye wad'annan mutanen me sukeyi a dikar daji??   Waye ya amshe kayan...kuma kayan waye???? Muje dai zuwa readers.
   
   
   
   

Comment and Share......

*Mrs.Abduul ce*.........

             BUTULU.....Where stories live. Discover now