(FINAL)CHAPTER 38

Start from the beginning
                                    

Bayan sun tafi tana zaune a dakinta taji shigowan su mus kukanta ya tsananta shi da aliyu ne kadai nan de aliyu yayi musu nasha da fata na gari ya gudu Dan shi kanshi kishi ke taso masa wai matarsa ce ke daukan sunan matan wani.

Koda ya koma gida ya samu luba ma an zuba tagumi ga rid'ed'en ciki taga ya shigo jiki a sanyaye. Zama yayi a gefenta baice komai ba sai hawayen da yake gogewa. Bata ce masa komai ba Dan itama tayi missing ladidi amma tana jin kishin yadda yake ma wata kuka ganin zai fashe da kuka yasa ta rungumo shi a kirjinta tana shafa kanshi ya gama kukansa harda shessheka ita kam mamaki ma ya bata a haka har yayi bacci.

Zata kwantar dashi a gefe saboda yadda bayanta ya rike ya kankameta yana fadin lubabatu Karki barni ke daya ce gareni Dan Allah. Shafa kanshi tayi a hankali tace bazan barka ba tana kwantar dashi kamin ta shige ban daki Dan fitsari take ji.

Dakin su mus kuwa tsoro yakeji kar ladidi tace baikai aliyu ba gashi shi ba gwani bane a fannin Dan bai taba sanin mace ba. Yace toh ladidi godiya ta tabbata ga Allah..... haka dai ya gama Mata jawaban shi ya ce su tashi suyi sallah. Shi yajasu domin kuwa cikin watannin nan ya zage ya koyi karatu sosai.

Riko hannunta tayi yace zo muci abinci kinji ? Kawai sai ta fashe masa da kuka shi rikecewa yayi dama haka amaren keyi ko ladidin ne? Da kyar ya lallabata ta bada hadin kai badan taso ba.

Bayan wata daya da sati uku ladidi tana bakin gadon luba tana zaune luba tace aunty ladidi Anya kuwa kinajin dadin zamanki da mus? Naga sai ramewa kike kina baki. Ladidi tace banida lafiya ne nace ma a kawo min sakamakon zasu iya zuwa ko wani lokaci. Nan take cewa kema haihuwa yau ko gobe gara na karasa hada miki jakan nan.

Baifi minti 5 da hiran ba akace Mata an kawo result din karbowa tayi ta bude taga maleria and typhoid report ne kuma negative dayan ta bude taga....

PREGNANCY REPORT ne kuma positive wani ihu ta buga tayi zaman daba tana fadin na shiga uku lubabatu innalillah wa inna ilaihi raji'un. Zabura luba tayi ganin yadda ta rude tace aunty karde kice min HIV gareki? Ladidi tace HIV din banza lubabatu ciki gareni na shiga uku na.

Luba tace kamar yaya aunty ladidi ? Cikin ne masifa ko me? Ladidi tace wallahi Allah banason mus kawai zama nake dashi yanzu kuma saina Haifa masa da? Aliyu ne ya shigo da gudu hannu a ka yana fadin innalillah wa inna ilaihi raji'un ladidi ashe har kinji sakon saide hakuri Allah yayinwa musa rasuwa. Dam! dam !! Kukeji take labour ya rike luba Wanda bata shirya ba ladidi ko shako aliyu tayi tace kaji maganar banza, kai ka kasheshi? Yace hakuri zakiyi ladidi.

Tace karya ne wallahi karyane musa na bai mutu ba ko a Nemo min shi ko nayi tashin hankali kace masa ya tashi, bai isa ya mutu ya barni ba. Aliyu yace haba ladidi karkiyi sabo mana. Bayan kin gama takaba sai na aureki ko?

Atake fire din luba ya fashe amma basu ma lura da ita ba ladidi tace bani SONKA wallahi yanzu shi nake so!
Murmushi yayi yace zo muje. Suna fita suka ga mus yana musu murmushi da gudu ta rungume shi tana fadin mus mus Dina shine zaka bari a bani tsoro ace min ka mutu ? Ta fadi haka tana dukan kirjinsa.

Dariya take yace laifinki ne AI muna dawowa muka jiki kina ihu wai baki sona zaki haifamin da shine oga aliyu yace zai gwadaki ashe de kina so na? Tace bana son tsokanan nan Dan Allah karka barni kneeldown yayi ya rungume jikinta yana dariya yace kai Dan samari kace daddy.

Dariya aliyu yayi daidai lokacin luba ta kwalla kara nan akayi hospital da ita bayan awanni 6 ta haifo yaranta maza 3 cas.

Bayan an gyarasu ne su ladidi suka shigo kowa yadau daya sai lokacin aka tuno da wasu aunty maryam aka sanar musu luba tace kai gaskiya nan gaba Allah yasa na haifi mace

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Bayan an gyarasu ne su ladidi suka shigo kowa yadau daya sai lokacin aka tuno da wasu aunty maryam aka sanar musu luba tace kai gaskiya nan gaba Allah yasa na haifi mace. Ladidi ta dungure mata kai tace oh su luba ande ji kunya..

Kwaikwayanta ta soma yi tana fadin waiyo Allah na aliyu ka cuceni bazan sake haihuwa ba wallahi ko yatsa na ka sake rikewa saina yanke ma hannu... yanzu kuma fadi take Allah yasa ta haifi mace.

Da shike a jingina luban take tayi Muryan ladidi tace "na shiga uku lubabatu innalillah wa inna ilaihi raji'un wallahi Allah banason mus kawai zama nake dashi yanzu kuma saina Haifa masa da?"
Sai kuma muka ga mutuniyar na fadin "karya ne wallahi karyane musa na bai mutu ba ko a Nemo min shi ko nayi tashin hankali kace masa ya tashi, bai isa ya mutu ya barni ba."
Dariya suka kyalkyale dashi dukansu aliyu yace toh ku jera muyi selfie! Yace cheese! Take da daukan hoton CLICK!

ALHAMDULILLAH! ALLAH YAYI KAMAR YADDA NA FARA A SA'A GASHI NA KARKARE MUKU WANNAN LABARI NAWA. INA MATUKAR GODIYA GAREKU MASOYA NA. FATAN ZAKU DUBA SABON LABARI NA MAI SUNA (YAJI TA MATA)

Sabon labari na me suna YAJI TA MATA shine littafina na uku....

Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsira ba domin kuwa babu wacce take iya zaman sati biyu dashi tsanani kwana 10 sai su gudu. Toh fa an Sami matsala domin reshe ta juye da mujiya inda Allah ya hadosa da Wanda ta fisa jaraba toh yanzu kuma shi ke gudu.

Wai ya za'a kwashe ne a lokacin da iyayen sa sukace bai isa ya saketa ba kamar yadda ya dafa kur'ani cewa bazai saketa ba?

KU BIYONI CIKIN WANNAN LABARI NAWA DAN JIN YADDA ZA'A KAYA.

GA LINK NAN https://my.w.tt/EMbqkgIeh8

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

17th July,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now