(FINAL)CHAPTER 38

3.2K 248 80
                                    

IDAN KUNA KARUWA DA LABARINNAN AYI FOLLOWING DINA SANNAN AYI VOTING

Mikewa su aunty maryam sukayi uncle ABBA yace toh malam aliyu mu zamu wuce abinda ya faru a baya a yafe mu tunda de kasan ba laifin mu bane mantuwa ce ni bazan iya cewa komai ba saide Allah ya bada zaman lafiya.

Tunda kuma kunyi shawara kamin kuka yanke hukunci mu bazance komai ba. Aunty maryam tace mun kuma gane kuskuren mu na auren sirri da mukayi muku muna kuma bawa iyaye shawara kimin rintsi kar suyi ma yaransu aure a boye ko na dole domin duk sun Saba addinin musulunci domin hakan bai taba faruwa a zamanin magabata ba.

A kwana a tashi wasa wasa cikin luba ya baiyana ya girma kuma ladidi ta fita a iddarta. Kullum kaman yaya da kanwa ita da luba suna dinke idan aliyu ya dawo daga wajen aiki tsakaninsu gaisuwa. Daga nan ya shige ciki luba tabi bayansa.

Yauma kamar kullum suna kitchen luba an bararraje akan island kamar uwar Mata ladidi na dama Mata kunun madara. Sallamar aliyu da musa sukaji domin kuwa shugaban leburori aliyu ya bashi tunda daga karatun primary ya tsaya amma ya jona yaki da jahilai kuma yana skill acquisition na computer so yana sa rai yayi using certificate dinsa ya shiga jami'a nan da watanni 7.

Mika Mata kunun ladidi tayi tace toh maman yan uku mijinki ya dawo nima najiyo Muryan future hubby na bari nabi bayan labule na wuce ko? Dariya Luba tayi ta zamo dakyar sanadiyyar nauyin da cikin ya fara saboda ya shiga wata na bakwai.

Bin bayan ladidi luba tayi da kallo tana mai tausaya Mata yadda ta rabu da mijinta kuma bata hassada ma matarsa.
Fitowa parlour tayi musa wato mus yace a ah auntyn mu ashe kece a kitchen din tace wallahi kuwa yaya mus ina wuni? Yace lafiya mun sameku lafiya ko? Tace Alhamdulillah dan kyakkyalla ido yake ko zakiga ladidi amma bai ganta ba.

Luba da ta gano sa tace aiko yanzunnan aunty ladidi ta shige daki nasan zata fito diba maka abinci da wannan ta shige dakinta aliyu yabi bayanta bayan ya dauko ludayi a kitchen. Bata ankare ba kawai taji ya tsindumo Ma ta ludayi a cikin kunu turo baki tayi tace wai kai wani irin baba ne kullum kana cikin shanye ma yaranka kunu ? Gwaliyo ya Mata yana dariya ta matsar da kunun tace kasha rabonka.

Yace haba maman babies kar muyi haka dake please kinji kunun ne dadi dukda cewa na jiya yafi dadi tace Allah ya soka ni nayi na ajiyan bani ludayin in diba maka rabi.
Yace uhm uhm kishi na damun wata ko? Ya fada yana dauke kai tace a bakin kunun ka yace tuba nake sarauniya yana miko Ma ta ludayin Suka kyalkyale da dariya.

Ladidi kuwa tana shiga daki ta goge hawayenta ta fada kan gado tana cire hijab din dake jikinta tace ya Allah ka yaye min kashin dake damuna Allah ka gani bawai Dan inason musa nabar aliyu ba na barshi ne saboda ina tsoro. Bazan iya zama da kishiya ba kar na cutar da luba Allah ko digon son musa ne kasa min Allah indai na taba yin wani aiki na ALKHAIRI ina tawassali dashi ka zaba min mafi alkhairi.

Mayar da hijab dinta tayi ta fita ba kowa a parlourn ta dauki abincin mus ta nufi dakinsa dake bayan gidan tu da saura satu a gama gyaran gidan da aliyu ya basu. Kwankwasawa tayi ya bude yana Mata murmushi ta tsuguna ta gaisheshi yana fadin nagode sosai ladidi aci gaba da hakuri dani tace ba komai ni zan koma yace toh anjima zanzo inji me da me kike bukata na auren dukda cewa kinsan har yanzu abubuwan basu bude ba.

Tace ai ba komai kasan ba wani shagali za'ayi bama nagode. Tana kaiwa nan ta Mike ta shige gida abinta. Ita fa har ga Allah a wani sako na zuciyar ta haushin mus takeji.

Bayan Sati biyu aka daura auren musa da ladidi saide luba abin bai Mata dadi ba saboda bata iya tafiya Dan yara 3 sunyi Mata nauyi idan ba ya zama dole kamar zuwa bandaki ba toh bata tashi yaso ayi auren bayan ta haihu musa yace AI bazai hana ladidin zuwa Gidan ba.

Su aunty maryam da makota kadan ne kawai suka kaita ba wani taro Dan ma kwana 3 kamin biki aunty maryam uwar gyara ta dauketa akayi Mata gyara Wanda ko aurensa na farko ba'ayi Mata ba.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now