CHAPTER 16

3.6K 222 32
                                    

ALIYU'S POV

Wannan wace irin magana ce ake min ace in aureta? Taya ma zasu biye shiriritar yarinya ? Ajiyar zuciya na sauke. Dadin abin ma ance in takai shekara 10 za'a sake tambayar ta. Toh ni ince wa nafeesa me? Dukda Cewa tana da hakuri amma ace tun kamin ayi aure a fada ma kishiyar ka? Lamarin nan da sake.

Kallon ya Abba Nayi nace Toh Allah ya kaimu nan da shekara 4 Daga nan aka Shiga sabgar biki na.

Akwana a tashi har Anyi aure na nida nafeesa Muna zaman lafiya mata me hankali da biyaiya samun irinta Nada mugun wahala. Tasha wahala sosai saboda 'bari da tayi yafi sai 4 Daga nan tahau jinya har Allah ya amshi ranta.

Daga nan na auri salma itama a hatsarin mota ta rasu. Kamin kace me na auri mata 6 amma duk babu mai tsawan rai kuma duk na kwarai ne saide abinda baza'a rasa ba.

Lokacin da luba tayi shekara Goma muna zaune mu mun mance da zancen ma Dan gani ake shirman ta ne ta manta kawai muka jiyota tana fadin indai zaman nan na batun aurena da uncle Ali ne toh ban fasa ba. Kallonta muka tsaya yi iko sai Allah yarinyar nada abin mamaki.

Yaune aka daura aurena na 7 da ladidi a yanzu shekarun luba 12 itane kirjin biki anata rawar kai. Inda Allah ya taimaka bata iya rawa ba Dan haka da akace za'a yi party tace baza ayi ba dama nima banaso ladidi ce ta dage.

Luba ko tace indai akayi dinner sai ta bata sauran ba'ayi ba wannan ms baza ayi ba. Dan haka aka fasa akayi Karin ango kawai aka kawo min amarya ta.

LUBA'S POV

Uncle aliyu kamar me aljanu da yayi aure se matar ta mutu ni da fari na dauka wasar buya suke mana ashe tafiya yama sunan wajen ? Yauwa ashe tafiya barzahu sukeyi duk sanda yayi aure toh gidansa nake weekend an hanani an hanani amma naki ji har an gaji. Aunty maryam tace AI idan ina zuwa ko wani lokaci bazaiyi dauki na ba amma nayi biris. Ba lura so suke na manta da zancen Niko kullum da na tashi daga bacci abinda nake tunawa kenan Dan bazan taba yarda suyi winning ba. Kenan fa na zama loser.

Matan sa nada kirki duk sanda naje suyita bani labari muna hira tun ina kankanuwa ta. Har goyona suke aunty nafeesa kam har cemin take idan na auri uncle aliyu ni zan dinga tayata wanke wanke. Niko sai na kyalkyale da dariya Dan abin birgeni take ashe de baza tayi Nisan kwana ba🥺 nayi kewarta.

Wasu idan aka fada musu cewa zai aureni da fari basa yarda amma idan suka ga banida matsala shikenan sai mu dinke Dan ni inason aiki sosai komai na gani sai na taba ko anyi shara sai nayi nima. Gani da surutu ba comma bare full stop.

Satin bikin uncle aliyu da aunty ladidi na shigowa na soma dauki, nayi can nayi can dukda yanzu shekarata 12 na soma game kishi amma ban damu saboda na Saba ganinshi da Mata. Bari na Baku labari in kuka ganni zakuce nakai shekaru 15 Dan mugun girma nayi.

Dinki naje karbowa dukda anyi anyi na bari a karbo naki Dan nasan telan Dan jagwal ne. Aiko koda naje ya yanka be dinka ba. Tada ma yan shagon hankali nayi sanda akayi a take aka bani ba zuburo Bali da yasha Jan baki sosai na dau ledar kayana na bashi 1500 nace yasin Rabin kudin zan biya saboda an bata min rai.

Kamar uwarsa jiki na ruwa yace jeki ba matsala kai ilu tara Mata me adaidaita sahu. Jiki na rawa kuwa ya tara mini ina tafiya suka Nemo ruwa da sobo suka kora Dan na caja musu kai ba kadan ba.

Ina dawowa naji ana wani batu wai za'a yi party nace in anyi shegiya nake. AI da gangan ake cewa za'ayi bayan ansan cewa ban iya rawa ba. Amma usilin zance babu rawar da ban iya ba tunba na bazo bazo ba. Kawai banish ayi party ne Dan a islamiya ance mana babu kyau amma nasan da na fadi wannan za'a kafa mini hujja da abinda nayi ina yarinya Wanda nasan abin ya faru amma na mance da abubuwa sosai bazan iya hada labarin ba saide a takaice.

Aiko da alamu uncle aliyun ma bayaso Dan babu wasting time yace angama uwani AI abinda kike so shi za'ayi. Nasan gatse yayi min a wasa mikewa nayi ina tsalle zan fice nace haka nakeson ji ubale na. BIYONI yayi da gudu na arce ina dariya.

Karin ango Akazo yi da shike maman su uncle ABBA ne shuwa shiyasa uncle Ali ya Dan dauki haskenta yayinda uncle abban yadau duhun mahaifinsu Wanda yake kanuri gaba da baya hakan yasa ba Karin angon da hausawa keyi akayi ba. Kaulu akayi wato original din na kanurai.

Karkashi ne za'a Dama ka lakata ka taba ma ango a hannu kayi masa addu'a sai ka lika kudi. Niko abin yanamin dadi lokacin muna shiri Dan ango ya kusa zama. Su nana sonata hura hanci wai na janyo baza'ayi party ba nace nifa rawa ce banyi gaban maza amma ina zuwa aunty maryam na samu tana cikin mutane sunanta korafin yadda ka biye min aka ki yin Partyn tana bada hakuri.

Koda na shigo akan hanci suke kallo na suna bata rai shan kanshi na fara tare da dage kai ina hura hanci na jujjuya musu mazaunai na da basu zauna ba Dan ni albarka kirji gareni amma mazaunai na basuda girma na bazo a gani daidai kamar na kowa ne.

Gefe naja aunty maryam nace so Nike a Kira mini ma kadan fada ayi mana ganga kura (ganga kura shine kidan da kanurai keyi wadda yawanci suke hawa kan layi ko sahu a taka rawa iri daya bawai a girgije Dan mu a tsarin kanuri babu rawar girgiza. Ada kakannin my kanurai suna ganin kowa Arne Dan lokacin a borno empire kadai akeda musulunci tun kamin ya shiga su sokoto. Any way ba historynazo Baku ba wannan ma wani fanni ne na daban😉)

Tace toh babu matsala komawa mukayi na daura liffaya ta blue wato shudi (ba lafaya ba and also kurkum not kurkur, Dilke not dilka fatan mun gane?💃🏻)  muka fito anata shan kamshi kamar iyayen Mata. Fili aka buda mini dan dama nasa an sanar da abokan ango cewa da na fito susa a bude min fili.

Dangwala nayi amma memakon na shafa masa a hannu sai na muka masa a gemu sannan na ciro bandir din 50 wato dubu 5 na cire hularsa nasa aciki harara ta yayi nayi masa gwalo yayinda abokansa suka saki baki suna kallon mu uku Niko kara dage gira nake Dan karma suyi shawagin cewa suna sona kuma abinda zai baka haushi ko kwalliya bamuyi ba Dan ni ka'idata ban kwalliya bawai Dan inada kyau yasa nake haka ba sai Dan ba kowa ya dace yaga kwalliyata ba! Nafi karfin wannan.

Bayan mun dawo cikin gida ne na kyalkyale da dariya Dan nasan yadda uncle aliyu keson gemunsa Kamar me. Masu ganga ne suka iso aka sanar wa maza suka shigo sannan akyi rawa ta al'ada karfe biyar ummi tayi mana surprise da masu kidan kwarya Dan haka maza suka fice waje inda ake Kari tare da me ganga yayinda Mata suka rufe kofa bayan an tabbatar babu namiji muka girgije nan na naje na karkade jiki su nana sai makemin mazaunai suke wai haka ne rashin iya rawa. Nide nace kanku.  Da daddare ne akace ankai amarya aiko ni da nana da mama mukace toh muma can zamu kwana aka hanamu.
Mama ce ta samu uncle Samir ta roka mana shi Dan taga alamun sa Santa yake amma bai fadi ba saboda karantarta shekarunta Goma ne.

Aiko babu wata wata ya yarda ya daukemu mu uku a Motansa ya kaimu muku muka saka wayar mu a plane mode toh amma ba zuwan ba abinda muka tarar ne yasa zan iya ce muku ana gwarama ko kuma akwai kura hajiya!

UHM IKO SAI ALLAH KO MECECE KURAR NAN? NIDE BARI NA SAMU BAKIN GADO NAYI SHIRU SANNAN NAJI DAGA GAREKU!

AFWAN KUN JINI SHIRU WAYATA TA DAN SAMI MATSALA NE AMMA ALHMDLLH KOMAI YA DAWO NORMAL DAN HAKA ACI GABA DA GASHI KAWAI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

18th June,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now